Kamar yadda da daman jama'a suke da masaniyar dambarwar da ke tsakanin Sheikh Sanusi Khalil da Manjo Hamza Al-Mustapha akan zarge-zarge na rashin gaskiya da rashin tsoron Allah da Malam Sanusi Khalili ya yiwa Manjo Mustapha. Rahotanni sun ce bayan sanya baki da Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya yi akan batun da shi Almustpaha ya garzaya kotu yake neman hakkinsa akan kazafin da yake tuhumar Malam Sanusi Khalil ya yi masa. Yanzu Malamin ya janye maganganun da ya yi akansa, abinda yake tabbatar da cewa Kage da Kazafi Malam Sanusi Khalil ya yi ga Manjo Mustapha, haka kuma ba karamin zubar da kima bace ta Malanta da shi Malam Sanusi Khalil ya yi.
Babban abin takaici ne ace Malami mai wa'azi wanda ya fi kamata ace yafi kowa siffanta da tsoron Allah, kuma Mutum mai shekaru irin na Sanusi Khalil ace idansa ya rufe, rashin tsoron Allah ya rinjayeshi ya yi irin wadannan maganganu masu zubar da kima da mutunci, ba dan komai ba sai dan burge jahilan mabiyansa da basa dora komai a ma'auni na hankali da Shari'ah. Ita daukaka daga Allah ta ke, Allah shi ne yake daukaka wanda ya so, ya kuma kaskantar da wanda ya so. Wasu malamai da dama sukan fada halaka ta san lallai sai sun tarawa kansu dimbin mabiya ta hanyar yin maganganu masu tsuma zukata da burge jama'a ko da kuwa karya ce da kage da kazafi irin wanda Malam Sanusi Khalil ya yi.
Hakika na yabawa Manjo Hamza Almustapha da ya yadda da wannan janye maganar da malamin ya yi a wajen kotu, duk kuwa da irin nisan da maganar ta yi, har wasu da dama suke kallon Almustapha a matsayin wani mutum mai hadari wanda ya zama barazana ga tsaro da zaman lafiya. Wanda wannan zargi ne mai girman gaske. Kamar yadda wasu suka ce "SULHU" Dakta Gumi ya yi musu, a kashin gaskiya kuma wannan ba sulhu bane, domin kazafi aka yiwa Almustapha shi kuma ya garzaya kotu domin neman hakkinsa. Shi kuwa sulhu ana yinsa ne ga wasu mutane da suka samu sabani da juna, kowa ya kafe akan wani ra'ayi, sai a shiga al'amarinsu a sasantasu kowa ya sassauto daga ra'ayinsa da ya kafe akansa.
Ina kira da babbar Murya ga Majalisar Malamai ta jihar Kaduna da Majalisar Malamai ta Kasa da fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi da su dakatar da Malam Sanusi Khalili daga yin wa'azi da huduba har tsawon Shekara guda dan haka ya zama darasi a gareshi da kuma sauran al'umma. Muna da masaniyar cewa Malamanmu ba ma'asumai bane, suna iya yin daidai kuma suna iya yin kuskure kamar yadda ko wane Mahaluki zai iya yi, amma abinda Malam Sanusi Khalil ya yi ba kuskure bane, ganganci ne da rashin tsoron Allah! Muna fatan a dauki mataki akansa, dan haka ya zama tilar a ja masa kunne dan hakan ya zama izna gareshi da sauran al'umma indai mu din al'umma ce mai tsari. Allah ya shiryeshi da mu baki daya, Allah ya kare sake aukuwar irin haka nan gaba ga sauran Malamanmu.
Yasir Ramadan Gwale
15-05-2014
No comments:
Post a Comment