Sunday, May 11, 2014

Tsakani Boko Haram Da Amerika Waye Abin Tsoro? [2]

TSAKANIN AMERIKA DA BOKO HARAM WAYE ABIN TSORO? [2]


Har yanzu akwai da dama daga cikinmu da suke ikirarin cewa wai babu wata Boko Haram, a cewarsu Gwamnati ce kawai! Da dama suna kore samuwar Boko Haram, cewa wannan duk wata makida ce ta gwamnatin Najeriya da kasashen yamma dan kassara yawan al'ummar Musulmin Najeriya. Sukan ce, duk wadannan hare-hare da ake kaiwa babu wasu Boko Haram Gwamnati ce kawai. Duk wanda yake da irin wannan ra'ayi ko tunani to hakika yana da rarraunar fahimta akan zahirin abinda yake faruwa dangane da Boko Haram.


Idan muna kauda kai daga gaskiya muna juyawa zuwa ga abinda ba gaskiya bane, kamar muna kara tsunduma kanmu cikin matsalar da muke ta mararin fita daga cikinta ne. Domin a duk sanda muka kauda kai ga masu laifi, muka koma kallon wasu daban cewa su ne suke mana wannan abin, alhali kuma a zahiri ga gaskiya nan ta bayyana kamar rana, to kamar muna kara rudar da kawukanmu ne.


Wadannan mutanan da suke kiran kansu Boko Haram sun sha yin ikirarin kai harin kunar bakin wake da na bama-bamai duniya tana gani, muma muna gani, kuma daga baya su yi ikirari su ce sune suka kai hari kaza da kaza. Kamar harin 20 ga janairun bara waccan a Kano da hare-haren da aka kai a kusan daukacin jihar Borno da Yobe duk sun yi ikirari cewa sune suka kai. Amma yana can kwance kan dakali yace ai babu wani Boko Haram, Gwamnati ce kawai. Ni dai na san cewa duk duniya babu wani mutum da za'a hada baki da shi, dan shi din ya mutu, babu wani mai hankali da zai bayar da hadin kai ga duk wanda zai hallakar da shi.


Kamar yadda kowa ya sani ne, akan idanunmu wadannan mutane suka fito suna ikirarin Boko Haram, suna kai hare-hare babu ji babu gani, wasu da dama ma an sansu. an san iyayansu. Amma sai wasu su kafe akan karya cewa wai ba Boko Haram bane. Dan haka ya zama dole a garemu mu gamsu cewa wadannan tsagerun da suke ikirarin kai wadannan hare-hare da sunan Boko Haram cewa su din ne ba wasu ba, tilar mu gamsu sune.


Haka kuma, a halin da muke ciki ai bama bukatar a ce har sai mun jira Malamai a Saudiyya sun yi fatawa sun nesanta Musulunci da Boko Haram, domin mu da muke Najeriya mu muka san abinda yake faruwa, da wanda aka dafa a cikin ruwa da wanda aka soya a cikin Mai ai duk labarin wuta suka ji, wanda aka gasa shi ne yaga wuta ganin idanunsa, tuni ya kamata a ce majalisar Koli ta Addinin Musulunci a Najeriya ta fitar da wata gamammiyar Fatawa ta Nesanta Musulunci da ayyukan Ta'addanci da Boko Haram suke yi, su kuma yi Alla-wadai da dukkan wani aiki na ta'addanci da zai kai ga salwantar rayukan da basu ji ba basu gani ba.Amma sai bayan da bango ya tsage!


Zan cigaba In Sha Allah.



11-05-2014

No comments:

Post a Comment