Saturday, May 31, 2014

Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un!!!

INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN!!!

Daga Allah muke kuma gareshi zamu koma! Hakika jiya wasu abubuwa guda biyu sun tayar min da hankali. Abu na farko wani Video da Kabiru Danladi Lawanti ya yi sharing a Timeline dina wanda IG Wala ya saka shi, inda naga ana yanka mutane da ransu kamar Tumaki, babban abin da ya tayar min da hankali shi ne, mutanan da ake yankawa a gabansu ake yanka dan uwansu, sannan kuma wanda za'a yanka din ba daureshi aka yi ba, hannu kawai za'a sanya a dafe shi wani ya yanka, Subhanallah! Kuma suma wadan da ake yankawa din suna zaune suna kallo ba tare da sun nuna wani yunkuri na guduwa ko nuna damuwa ba. Wannan al'amari ya tayar min da hankali matuka!

Da farko na yi zaton cewa abin da ya faru a kasar Afurka ta Tsakiya ne, amma da na sake kallo sai naji Turancin da ake yi Pidgin English na Najeriya ne, haka ita ma gurbatattar Hausar da aka yi irin ta yankin Arewa Maso Gabas ce. Abinda na kasa ganewa shi ne, shin su waye suke aikata wannan mummunan aikin yanka mutane? Sannan su waye wadan da ake yankawa? Abin ya tayar min da hankali ainun!

Abu na biyu kuma, labarin da na ji a BBC cewa an sace Sarakuna masu daraja ta daya a Borno, ciki kuwa har Sarkin Gwoza ya samu Shahada. Ba shakka hankali na ya tsahi da jin wannan labari ace hatta Sarakuna basu tsira  daga wannan mummunan Bala'I na shekara da Shekaru ba! Manzon Allah ya yi gaskiya, yace ku guji tayar da fita domin tana shafar wanda ya janyota da wanda bai san hawaba balle sauka. Allah ya la'anci masu tayar da Masifa.

Ya Allah mun tuba daga laifukanmu, Ya Allah mun zalinci kawukanmu, Ya Allah mu masu laifi ne, Ya Allah kaine ka ce mu roke ka zaka amsa mana, Ya Allah kaga irin halin da muke ciki na tsanani da damuwa da tashin hankali Ya Allah ka kawo mana dauki. Ya Allah ka ceci rayukanmu. Ya Allah, Ya Allah Ya Allah ka kawo mana karshen wannan masifa da Bala'I.

YASIR RAMADAN GWALE
31-05-2014

Friday, May 30, 2014

SHEIKH BALA LAU: Adalin Jagora Abin Koyi!

SHEIKH BALA LAU ABDULLAHI: Adalin Jagora Abin Koyi!

Tun bayan zamansa sabon Shugaban kungiyar Izala ta Kasa, Sheikh Bala Lau Abdullahi ya nuna shi shugaba ne mai dattako da tausayi da taimako da sauraren koke-koken al'ummar da yake jagoranta. Sheikh Bala Lau ba shi da bukatar a yiwa al'umma dogon ta'arifinsa, domin a bayyane yake ga duk wanda yake bibiyar ayyukan Kungiyar Izala ya san yadda Shugaban yake yin jagoranci abin misali wajen nuna kulawa da halin da al'umma ta ke ciki tare da nuna damuwa akan irin mawuyacin halin da ake ciki a kasa baki daya da bayanin hanyoyi na gaskiya da za'a kubutar da al'umma daga halin ni 'ya su.

Irin yadda Shugaba Sheikh Bala Lau yake nuna damuwa da halin da Talakawa da Marayu suke ciki na daga cikin irin Jagoranci abin koyi da Sheikh Bala Lau yake nunawa, kullum burinsa yaya al'umma zasu samu saukin rayuwa, dan haka bai taba gajiyawa ba wajen kutsa kai cikin talakawa musamman marayu dan ganin irin halin da suke ciki tare da yi musu goma ta arziki da share musu hawayen maraici da ya kwanranya a idanunsu.

Yana daga cikin irin kyakkyawan jagoranci abin Misali da Sheikh Bala Lau yake yi na kokarin hada kan Malaman Kasar nan Mabiya Sunnar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam wajen ganin an gudu tare an kuma tsira tare, an yi aiki tare wajen taimakawa al'umma dan rage musu radadin halin da suke ciki da kalamai na hikima.

Sheikh Bala Lau Abdullahi yana daga cikin sahun farko na Malaman da suke damuwa da irin halin da kasarnan ta ke ciki, kuma su gayawa Shugabanni gaskiya ba tare da shayi ko fargaba ba, a koda yaushe ya samu fursa ta haduwa da Shugabanni yana iyakar kokarinsa wajen ganin ya isar musu da sakon gaskiya tare da kira a garesu wajen sauke nauyin al'umma da yake kansu. Da dama daga wadan da suka san Sheikh Bala Lau sun shaideshi cewa Mutum ne mai kankan da kai mara girman kai bashi da kwadayi ballantana rowar abin hannunsa koda yaushe hannunsa a bude yake wajen tallafawa mabukata.

Hatta wadan ba Ahlussunnah ba Allah yana matsa bakinsu su fadi magana ta gaskiya akan Sheikh Bala Lau. Haka kuma, Sheikh Bala Lau yakan kai ziyarce ziyarce asobitoci domin duba halin da al'umma suke ciki tare da basu tallafi, ya isa abin misali, Sheikh Bala Lau shi ne kadai Shugaban wata kungiya ta Musulmi da ya kai ziyara babban asibitin kasa da ke Abuja dan jajantawa wadan da harin bom din Nyanya ya rutsa da su, ya kuma basu tallafi kamar yadda ya saba.

Yana daga cikin halin dattako irin na Sheikh Bala Lau girmama mutane da girmama ra'ayinsu, mutum ne da kofarsa a bude take wajen ganin ya saurari al'umma tare da karbar shawarwari daga garesu ba tare da wani jidali ba. Muna yi masa addu'ar Allah ya yi masa jagora a wannan Shugabanci abin misali da yake yi, Allah ya kare shi daga sharrin masu sharri, Allah ya haskaka masa hanya wajen bin dai-dai tare da aiki da gaskiya. Allah ya taimaki Sunnah da masu Da'awar kira zuwa ga Sunnah.

YASIR RAMADAN GWALE
30-05-2014

Thursday, May 29, 2014

RANAR DIMOKARADIYYA: Gwamnan Jigawa Sule Lamido Ya Ciri tuta


RANAR DIMOKARADIYYA: Gwamnan Jigawa Sule Lamido Ya Ciri Tuta

A yau 29 ga watan mayu da ake bikin ranar da mulki ya koma hannun farar hula a karo na 15. Gwamnan jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido ya tserewa sa'a a yayin wannan biki. Ba shakka dole na yi yabo da jinjina ga Gwamnan Talakawa Alh. Sule Lamido bisa irin yadda ya nuna cewa inganta rayuwar Matasa da al'umma shi ne burinsa, da yawan takwarorinsa Gwamnoni sun mayar da hankali akan batutuwa da suka shafi siyasa a wannan rana, amma shi a nasa bangaren Gwamna Sule Lamido masana da manazarta ya gayyato irinsu Alh. Abdulkadir Balarabe Musa da Farfesa Ahmad Dandatti Abdulkadir da Barr. Solomon Dalung ya kirawo domin su tattauna su bada hasken yadda za'a inganta rayuwar matasa. Ba shakka irin wannan halin kishin Talakawa da Sule Lamido yake nunawa firi-falo haka ya kamata dukkan shugabanni su siffanta da shi. Gwamna Lamido ya ciri tuta a wannan janibi.

Bana mantawa a bara ma a irin wannan rana, gwamna Lamido ya gayyato masana tattalin arziki zuwa Dutse jihar Jigawa domin tattauna yadda za'a bunkasa tattalin arzikin Jihar Jigawa sabuwar Duniya. Wannan abin a yabawa Gwamna Lamido ne akan irin kokarinsa na ciyar da rayuwar Talakawansa gaba. Haka nan kuma, bana mantawa Gwamna Lamido a lokacin da ya zama Gwamna a zangon farko a irin wannan rana ya kirawo taron Talakawa wanda ya sanyawa sunan TALAKAWA SUMMIT inda Gwamnan ya tattauna da Talakawa kai tsaye babu shamaki tsakaninsu, inda suka bashi shawarwari kuma suka yi korafe-korafe a gareshi. Irin wannan salon Shugabanci da Gwamna Sule Lamido yake yi wanda kadan ne daga cikin irin kayan gadon da marigayi Malam Aminu Kano ya barwa 'yan baya, shi ne abinda muke fatan dukkan shugabanninmu su mayar da hankali akai.

Shugabanni su ji tsoron Allah, su zauna su kallai rayuwar Talakawan da suke shugabanta, me aka gabatar musu wanda zai dadada ya kuma saukaka rayuwar al'umma, a kuma yi Nazarin halin da al'umma ta ke ciki domin samar mata da mafita sahihiya.

Daga karshe ina kara nuna jinjina da yabawa ga Gwamna Sule Lamido akan irin wannan manufa tasa ta nuna kishin al'ummar da suka zabe shi, ina kuma kira ga sauran Gwamnoni Makwabta da su yi koyi da Gwamnan jihar Jigawa Alh. Sule Lamido wajen shirya taruka irin wadannan da ake gudanarwa a Jigawa a irin wannan rana. Ina kuma taya Gwamna Lamido murnar cika shekaru 7 kan kujerar Gwamnan Jigawa, Allah ya bashi ikon sauke nauyin al'umma lafiya.

YASIR RAMADAN GWALE
29-05-2014

NAJERIYA: Aikin Kamfani Ko Aikin Bauta?

A Najeriya dokar kasa ta ce duk wasu da zasu kafa kamfani a wani waje a fadin tarayyar Nigeria dole ne su dauki Personnel Manager dan asalain wajen da aka kafa kamfanin. Personnel manager shi ne zuciyar kamfani, amma a KANO dukkan wani kamfani da yake aiki na 'yan China da indiyawa da kwarori da na Sadarwa babu wani kamfani da aka dauki Personnel manager dan asalain jihar kano. Ba komai ya janyo haka ba sai CIN-HANCI duk masu kafa kamfani sun san da wannan doka, amma sun bayar da cin-hanci ga manyan gari an dauke kai daga kansu suna yin abinda suka ga dama. Kaje dukkan wani kamfani da yake aiki a Chalawa/Panshekara, Sharada, Dakata, Bompai kaga yadda ake cin zarafin al'ummar jihar Kano, kwara ko dan china ya fellawa ma'aikaci dan Kano mari akan laifin da bai kai ya kawo ba kuma ya mari banza babu abinda za'a yi sai dai ma'aikacin ya yi kukansa ya yi Allah Ya isa!

Da yawan ma'aikatun 'yan Indiya da kwarori da 'yan Chana suna hana ma'aikatansu zuwa Sallar juma'a, Sallar azahar da la'asar da magriba da Isha kuwa lokaci suke bayarwa duk wanda ya d'ara ana dandana masa kudarsa ko a zaftare a cikin albashinsa da bai taka kara ya karya ba. Wannan fa duk yana faruwa ne karkashin igiyar 'YANCI da muke da ita a kasarmu da mutanenmu suke shugabantarmu ba Bature farar fata ba. Duk wani ma'aikacin Kamfani ko wanda ya taba yin aikin kamfani musamman a Kano yasan da wannan dama wasu al'amura masu muni.

Sannan kuma, da yawa damar samun gurbin aikin da muke da ita a matsayinmu na 'yan Asalain jihar Kano raba dai-dai muke yi tsakaninmu da mutanan Kudancin Kaduna da Arnan Jos da Katafawa da sauransu. Mun zama masu matacciyar zuciya cima zaune, abubuwan da ya kamata mu ci gajiyarsu mun bari wasu daga nesa sun cin moriyarsu. kaje duk wasu Kamfanunuwa da Bankuna masu hada-hada yau da kullum kai ka ce ba a kano yake ba, domin tun daga kan masu Gadi wadan da sune koma baya a cikin ma'aikata zaka fahimci irin yadda aka kwashe mana kafafu! Kai ba kamfanoni ba hatta wasu daga cikin Ma'aikatu har da na Gwamnati zaka taras da Mai Gadi ba Bahaushe bane balle kayi maganar mutumin Kano.

Mun taba yunkurin kawo dauki akan wani kamfanin sadarwa da ya dinga binne wayoyinsa a kasa, danganin al'ummarmu sun ci moriyar abin cikin wadan da aka yi wannan yunkuri da su har da Dakta Aliyu Jibia, amma abinda aka sanar mana shi ne jefa rayuwarmu zamu yi cikin hatsari idan har muka dage sai anyi gyara akan haka. Gyara ba zai taba yuwuwa ba a Najeriya sai an yaki CIN-HANCI bilhakki da gaske a dukkan fannoni.

YASIR RAMADAN GWALE
29-05-2014

Thursday, May 22, 2014

Dangane Da Batun Sheikh Sunusi Khali Da Hamza Almustapha


DANGANE DA BATUN SHEIKH SUNUSI KHALIL DA HAMZA ALMUSTAPHA!!!

Jiya da na yi magana akan abinda ya faru tsakanin Sheikh Sunusi Khalil da Manjo Hamza Almustapha, na samu sa’kwanni da yawa, inda wasu da dama suke ganin tayaya zamu yiwa Malamin Sunnah wanda d’an uwanmu ne irin maganganun da suka gabata! Wasu sunyi maganganu masu muhimmanci wasu kuma sunyi shirme. Amma abinda na sani Adalci shi ne, dan Malamin Sunnah ya yi irin abinda Malam Khalili ya yi ba zamu dauke kai daga gareshi ba mu binne abin wai dan kada 'yan Shi'ah su gani su yayata mu ko su yi mana dariya.

A zamanin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, wata mata daga cikin Musulmai ta yi sata a farko-farkon Musulunci, kuma kayan da ta sata na Bayahude ne, Sahabbai suka shiga cikin damuwa suna tattauna yadda za'a boye abin dan kada Yahudawa su gani su zargi Musulmi, dan gudun kada hakan ya sanya dari-dari ga masu shiga Musulunci a lokacin. Manzon Allah SAW har ya karkata zuwa ga ra'ayin Sahabbai na a rufawa matar Asiri kar a tona maganar dan kada Yahudawa su samu abin fada, Ta ke Allah Subhanahu Wata'ala ya saukar da ayar Al-Qur'ani yake umarni da yi wa duk wanda ya aikata laifin sata hukuncin haddin sata! Wannan ya kore dukkan wata kara dan Musulmi ya aikata wani aiki na ba dai dai ba a rufa abin a boye dan kada wasu su yi magana.

A lokacin da ake jihadi, sahabin Manzon Allah SAW Kahlid Ibn Walid, ya bi wani Muhsriki zai kashe shi, sai Mushrikin ya yi Kalmar Shahada, amma duk da haka Khalid ya fille wuyansa, da Manzon Allah ya samu labari baiyi wata-wata ba wajen barranta daga Abinda Khalid ya aikata, duk kuwa da cewa Khalid yana da tarin Alkhairai masu dumbin yawa dab a zasu lissafu ba a Musulunci amma Manzon Allah bai yi masa kara ba a matsayinsa na wanda ya fito Gwagwarmayar tabbatar da wanzuwar addinin Allah a ban kasa. Haka batun yake, idan muka koma kan Kissar su Ka’ab Bin Malik.

Duk wanda ya saurari kalaman Sheikh Sunusi Khalil akan irin maganganun da ya yi akan Almustapha zai tabbatar da cewar Malamin da gaske yake, domin ya yi rantsuwa da Allah cewa abinda ya fada dai-dai ne kuma gaskiya ne, har yake ikirarin wajen da aka zauna aka nakasha abinda yake ikirari, ya kuma kalubalanci duk wanda ke san sanin hakikanin abinda ya faru ya garzaya kotu dan shi Malamin ya baje kolin hujjoji, akan tuhumar da yake yiwa Almustapha na amfani da ake das hi dan cutar da al’ummar Musulmi.

Da muka ji cewar Almustapha yaje kotu munyi farinciki domin muna san ganin irin hujjijin da shi Malam Sunusi Khalil ya dogara garesu dan fayyacewa al’ummar Musulmi irin Makircin da aka hada baki da Almustapha wajen shirya mana. Haka kuma, ya zama kamar wajibi akansa ya bayyanawa al'umma wadannan hujjoji domin ya nuna cewa za'a cutar da Musulmi ne, tunda kuwa yana da masaniyar hakan wajibi ne ya bayyana dan kare rayuwar al'umma.

Tun da aka fara wannan Shari'ar wasu daga cikin Malaman Sunnah suka fahimci cewa lallai idan aka kai karshen yanke hukunci tabbas za'a ji kunya, dan haka aka yi ta rokon shi Manjo Hamza Amustpaha akan ya yi hakuri ya janye karar da ya kai kotu, Hamza Almustpha ya ce ba zai janye ba sai Kotu ta tabbatar da gaskiyar lamari akan batun, idan har an sameshi da laifin da malamin ya fada baya shakkar a yi masa dukkan hukuncin da Shari'ah ta tanadar, aka tursasawa Almustapha akan janye maganar a gaban kotu, a tattauna ta bayan fage dan warware batun, har daga bisani ya mika lamarin a hannun Sheikh Dr. Ahmad Gumi inda ya yi alkawarin biyayya ga dukkan matsayar da Gumi ya zo da ita akan batun. Dan haka dukkan wata tattaunawa akan wannan batu ta takaitu ne tsakanin shi Malam Sunusi Khalil da Dakta Ahmad Gumi, dan haka duk wanda y ace Sulhu aka yi, to ya fada dan ya gyara zancen domin zaman bad a Almustapha aka yi shi ba.

A bisa bincike da bayanan da suka fito yayin wannan tattaunawa, shi kansa Malam Khalil abinda ya fada din ba maganarsa bace, domin wasu ne suka yi amfani da shi tare da alkawarin bashi hujjojin da suke tattabatar da maganar, suka yi masa ingiza mai-kantu ruwa, amma da ya tashi yin jawabi sai yayi magana sabanin yadda ya samu labarin, su kuma wadan da suka ingiza shi yin maganar suka dare suka barshi. Har ta bayyana karara cewar abinda ya faru Kazafi ne aka yiwa shi Almustpha.

Wasu da dama suna batun cewar ai Malam kuskure ya yi, kuma ya gane kurensa dan haka ya janye maganarsa. Wanda ko kusa wannan ba a kiransa da kuskure, domin a jawaban Malam Sanusi Khalil Magana yake da karfin halin cewar yana da hujja akan abinda ya fada. Mu Ahlus-Sunnah ne, Muna da yakini akan cewa babu wanda baya yin kuskure, hasalima shi ne cikar Dan-Adamtaka mu kasance masu aikata kuskure, da saninmu ko babu sani, amma abinda Sheikh Khalil ya yi ganganci ne, haka kuma, duk wanda yake bibiyar Da’awar Sunnah irin wadda Sheikh Sunusi Khalil yake yi, Da’awa ce mai cike da abubuwan tuhuma, dan Malamin ya cika mafiya yawancin maganganunsa da kalamai na Rantsuwa da Tsinuwa, ya ambaci shigabanni ya tsine musu yace kowa yace Ameen, wanda yaki cewa Ameen shima Allah ya tsine masa! Wannan duk wanda yake bibiyar karatuttukansa haka yake fada, kuma wannan ya sabawa koyarwar Sunnah.

Yanzu dan Allah, da wane irin ido Sheikh Sunusi Khalil zai kalli Hamza Almustapha a matsayin wanda ya gina maganganu akansa wanda ba gaskiya bane? Yaya Hamza Almustapha zai dinga kallon shi Sheikh Sunusi Khalil a nan gaba? Kamar yadda na fada, babu wani Malami wanda yake Ma’asumi da baya kuskure kowa na yi, amma na Sheikh Sunusi Khalil ganganci ne ba kuskure ba, domin ikirari ya yi ya kuma cika shi da rantsuwa da Allah mahalicci. Duk da ya bayyanawa duniya cewar dukkan bayanan da ya yi akan Hamza Almustapha din ba gaskiya bane, dole abin ya yi mana ciwo mu shiga cikin damuwa, akan irin abinda ya faru.

Tabbas wannan al’amari zai bude wani sabon babi akan dukkan wasu maganganu da malamai zasu dinga yi musamman ga ‘yan siyasa. Fatana Allah ya kare malamai daga gurfana a gaban kotu dankare irin maganganun da suka yi watakila bisa kuskure. Allah ya shiryemu shirin Addini ya nuna mana gaskiya mu fahimce ta ya kuma bamu ikon aiki da ita ko daga wa ta ke.

Yasir Ramadan Gwale
16-05-2014

Thursday, May 15, 2014

Ya Kamata A Dakatar Da SHeikh Sunusi Khalil Daga Yin Wa'azi


YA KAMATA A DAKATAR DA SHEIKH SUNUSI KHALIL DAGA YIN WA'AZI!!!

Kamar yadda da daman jama'a suke da masaniyar dambarwar da ke tsakanin Sheikh Sanusi Khalil da Manjo Hamza Al-Mustapha akan zarge-zarge na rashin gaskiya da rashin tsoron Allah da Malam Sanusi Khalili ya yiwa Manjo Mustapha. Rahotanni sun ce bayan sanya baki da Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya yi akan batun da shi Almustpaha ya garzaya kotu yake neman hakkinsa akan kazafin da yake tuhumar Malam Sanusi Khalil ya yi masa.  Yanzu Malamin ya janye maganganun da ya yi akansa, abinda yake tabbatar da cewa Kage da Kazafi Malam Sanusi Khalil ya yi ga Manjo Mustapha, haka kuma ba karamin zubar da kima bace ta Malanta da shi Malam Sanusi Khalil ya yi.

Babban abin takaici ne ace Malami mai wa'azi wanda ya fi kamata ace yafi kowa siffanta da tsoron Allah, kuma Mutum mai shekaru irin na Sanusi Khalil ace idansa ya rufe, rashin tsoron Allah ya rinjayeshi ya yi irin wadannan maganganu masu zubar da kima da mutunci, ba dan komai ba sai dan burge jahilan mabiyansa da basa dora komai a ma'auni na hankali da Shari'ah. Ita daukaka daga Allah ta ke, Allah shi ne yake daukaka wanda ya so, ya kuma kaskantar da wanda ya so. Wasu malamai da dama sukan fada halaka ta san lallai sai sun tarawa kansu dimbin mabiya ta hanyar yin maganganu masu tsuma zukata da burge jama'a ko da kuwa karya ce da kage da kazafi irin wanda Malam Sanusi Khalil ya yi.

Hakika na yabawa Manjo Hamza Almustapha da ya yadda da wannan janye maganar da malamin ya yi a wajen kotu, duk kuwa da irin nisan da maganar ta yi, har wasu da dama suke kallon Almustapha a matsayin wani mutum mai hadari wanda ya zama barazana ga tsaro da zaman lafiya. Wanda wannan zargi ne mai girman gaske. Kamar yadda wasu suka ce "SULHU" Dakta Gumi ya yi musu, a kashin gaskiya kuma wannan ba sulhu bane, domin kazafi aka yiwa Almustapha shi kuma ya garzaya kotu domin neman hakkinsa. Shi kuwa sulhu ana yinsa ne ga wasu mutane da suka samu sabani da juna, kowa ya kafe akan wani ra'ayi, sai a shiga al'amarinsu a sasantasu kowa ya sassauto daga ra'ayinsa da ya kafe akansa.

Ina kira da babbar Murya ga Majalisar Malamai ta jihar Kaduna da Majalisar Malamai ta Kasa da fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi da su dakatar da Malam Sanusi Khalili daga yin wa'azi da huduba har tsawon Shekara guda dan haka ya zama darasi a gareshi da kuma sauran al'umma. Muna da masaniyar cewa Malamanmu ba ma'asumai bane, suna iya yin daidai kuma suna iya yin kuskure kamar yadda ko wane Mahaluki zai iya yi, amma abinda Malam Sanusi Khalil ya yi ba kuskure bane, ganganci ne da rashin tsoron Allah! Muna fatan a dauki mataki akansa, dan haka ya zama tilar a ja masa kunne dan hakan ya zama izna gareshi da sauran al'umma indai mu din al'umma ce mai tsari. Allah ya shiryeshi da mu baki daya, Allah ya kare sake aukuwar irin haka nan gaba ga sauran Malamanmu.

Yasir Ramadan Gwale 
15-05-2014

Tuesday, May 13, 2014

Tsakanin Amerika Da Boko Haram Waye Abin Tsoro? [3]


TSAKANIN AMERIKA DA BOKO HARAM WAYE ABIN TSORO? [3]

Wasu da dama suna da tunanin ai babu yadda za'a yi Musulmi ya dinga kai ire-iren wadannan hare-hare na rashin imani da Boko Haram suke kaiwa. Dan haka ne suke kaddara cewa duk wanda zai kai irin wannan hari to ba Musulmi bane. Ko dai gwamnati ce a yadda wasu ke cewa wanda jagornta ba Musulmi bane, ko kuma  kungiyar Kiristoci ta kasa CAN wanda suma duk ana zarginsu. A kashin gaskiya duk wanda yake da tunanin cewa Muslmi ba zai iya yin abinda Boko Haram suke yi ba, to yana kishirwar sanin tarihin Musulunci. Domin Musulmi wadan da suke ikirarin Musulunci da fatan shiga Al-Jannah su ne suka kashe Sahabin Manzon Allah SAW kuma surikinsa Uthman Ibn Affan Allah ya kara yarda da shi, haka kuma Shia da suke ikirarin Musulunci suka kashe Al-Husain Ibn Ali jikan Manzon Allah SAW, dan haka, duk wanda ya san tarihin Khawarij a Musulunci, ya kuma karanta tarihin Sarkin Musulmi Hajjaj Bin Yusuf Ath-thaqafy to ba zai taba yin mamaki ba idan duk hare-haren da ake kawai Musulmi ne sike yinsu wadan da ake kira Boko Haram.

Addinin Musulunci ya yi tir da dukkanin wani aikin Ta'addanci da ya hada da kisan rayukan bayain Allah da basu san hawa ba, basu san sauka ba, yayi hani ga lalata dukiyoyin al'umma haka siddan. Dan haka, dan Musulunci ya yi hani ga aikata aikin Ta'addanci irin wanda Boko Haram suke aiwatarwa,, wannan ba shi ne zai sanya idonmu ya rufe har mu dinga ganin Musulmi ba zai iya yin abinda ke faruwa ba, dan haka dole idan an bigi jaki a bigi mangala. Amma ba zamu yi mamaki ba idan ance ana taka sawun barawo acikin al'amarin Boko Haram, wannan ce hikimar da Musulunci yace idan an san farkon Masifa to ba'a san karshenta ba, dan haka Allah ya la'anci dukkan masu tayar da ita.

Aganina zai zama tufka da warwara, idan aka ce Gwamnatin da ake zargi ita ce ke kai hare-haren da ake kaiwa Musulmi a Arewa da sunan Boko Haram, amma kuma ana zargin ta da gazawa wajen magance matsalolin tsaron! Tayaya gwamnatin da muke zargin tana kashe mu, kuma mu dinga kiran ta shawo kan al'amuran tsaro?  Babu shakka  Gwamnati ta gaza matukar gazawa wajen dakile ayyukan Ta'addanci irin wanda Boko Haram ke aiwatarwa, anyi sakaci mai girman gaske wajen tsare rayukan al'ummar kasa da dukiyoyinsu, hakki ne na wajibi akan hukuma da Allah ya dora mata alhakin tafiyar da al'amuran al'umma ta tsare musu jininsu da Mutuncinsu da Hankalinsu da dukiyoyinsu. Amma a nan hukumomin tsaro basa daukar irin matakin da ya dace wajen samar da cikakken tsaro ga al'ummar kasa da magance matsalar Boko Haram.

Zarge-zargen da ake yiwa Gwamnati na hannu a cikin abubuwan da ke faruwa, wannan ita ce zata kare kanta daga dukkan wani zargi mai tsuhe da mara tushe. Musamman tambayoyi irin, a ina Boko Haram suke samun kudi da Makamai? Ya aka yi batun ya kawo har yanzu bai zo karshe ba, duk kuwa da irin kudin da aka lafta a bangaren tsaro. Wani karin magana na Hausa da yake cewa KIFI NA GANINKA MAI JAR KOMA, a tunani na kamar fassara ne na irin abinda Boko Haram ke yi, domin karin maganar ba cewa ya yi Mai Jar Koma Yana Ganin Kifi ba; a har kullum shi mai laifi ko mai shirin aikata laifi, yana ganin hukuma amma ita hukuma bata ganinsa, dan haka kamar yadda Kifi yaga jar komar Masunci zai yi dukkan mai yuwuwa wajen zillewa fadawa cikinta, sai dai fa idan kaddara ta fada masa, to haka shima mai aikata laifi, kullum tunaninsa da basirarsa ita ce ya za ayi ya kaucewa fadawa komar hukumomi, dan haka ba zai zama abin mamaki ba a gareni idan ance wadannan masu aikata ta'addancin suna yin abinda suke yi ba tare da sun fada komar jami'an tsaro ba.

Ta bangarenmu kuma akwai sakaci mai girma daga jagororinmu da suka hada da Sarakuna da Masu Mulkin Siyasa da Kuma Malaman Addini da wadan da ke kiran kansu Shugabannin Arewa, domin tun farko ana ji ana gani Boko Haram suka dinga ikirarin abinda suke yi Musulunci suke karewa, kuma Shari'ah suke son aiwatarwa, amma kusan wadan da Mas'uliyyar ta ke a hannunsu suka ja baki suka tsuke, ko dai dan tsoron fushin Boko Haram ko dan ko inkula da sauransu, Allah ya jikan Sheikh Jaafar Mahmoud Adam da Sheikh Adam Albani da suka yiwa al'umma bayani akan wadannan miyagun mutane.

Har ila yau, bisa ga zato na Adalci da kyautatawa juna zato, babu yadda Gwamnatin tarayya zata dauki Makamai tana kashe jama'a a Arewa da sunan Boko Haram, amma Sarakuna da Masu Mukaman Siyasa suna ji suna gani su yi shiru ana kashe al'ummarsu ba su dauki mataki ba. Saninmu ne cewar Boko Haram sun kaiwa Shehun Borno hari, sun kaiwa Sarkin Fika hari, sun kaiwa Sarkin Dikwa hari, sun kaiwa Mai Martaba Sarkin Kano hari amma ace duk suna da masaniyar Gwamnati ce ke da alhakin abinda ke faruwa amma su ja baki su tsuke gwamnati na neman halaka su. Bana jin wani abu mai kama da haka zai iya faruwa.

Zan cigaba In Sha Allah.

YASIR RAMADAN GWALE 
13-05-2014

Sunday, May 11, 2014

Tsakani Boko Haram Da Amerika Waye Abin Tsoro? [2]

TSAKANIN AMERIKA DA BOKO HARAM WAYE ABIN TSORO? [2]


Har yanzu akwai da dama daga cikinmu da suke ikirarin cewa wai babu wata Boko Haram, a cewarsu Gwamnati ce kawai! Da dama suna kore samuwar Boko Haram, cewa wannan duk wata makida ce ta gwamnatin Najeriya da kasashen yamma dan kassara yawan al'ummar Musulmin Najeriya. Sukan ce, duk wadannan hare-hare da ake kaiwa babu wasu Boko Haram Gwamnati ce kawai. Duk wanda yake da irin wannan ra'ayi ko tunani to hakika yana da rarraunar fahimta akan zahirin abinda yake faruwa dangane da Boko Haram.


Idan muna kauda kai daga gaskiya muna juyawa zuwa ga abinda ba gaskiya bane, kamar muna kara tsunduma kanmu cikin matsalar da muke ta mararin fita daga cikinta ne. Domin a duk sanda muka kauda kai ga masu laifi, muka koma kallon wasu daban cewa su ne suke mana wannan abin, alhali kuma a zahiri ga gaskiya nan ta bayyana kamar rana, to kamar muna kara rudar da kawukanmu ne.


Wadannan mutanan da suke kiran kansu Boko Haram sun sha yin ikirarin kai harin kunar bakin wake da na bama-bamai duniya tana gani, muma muna gani, kuma daga baya su yi ikirari su ce sune suka kai hari kaza da kaza. Kamar harin 20 ga janairun bara waccan a Kano da hare-haren da aka kai a kusan daukacin jihar Borno da Yobe duk sun yi ikirari cewa sune suka kai. Amma yana can kwance kan dakali yace ai babu wani Boko Haram, Gwamnati ce kawai. Ni dai na san cewa duk duniya babu wani mutum da za'a hada baki da shi, dan shi din ya mutu, babu wani mai hankali da zai bayar da hadin kai ga duk wanda zai hallakar da shi.


Kamar yadda kowa ya sani ne, akan idanunmu wadannan mutane suka fito suna ikirarin Boko Haram, suna kai hare-hare babu ji babu gani, wasu da dama ma an sansu. an san iyayansu. Amma sai wasu su kafe akan karya cewa wai ba Boko Haram bane. Dan haka ya zama dole a garemu mu gamsu cewa wadannan tsagerun da suke ikirarin kai wadannan hare-hare da sunan Boko Haram cewa su din ne ba wasu ba, tilar mu gamsu sune.


Haka kuma, a halin da muke ciki ai bama bukatar a ce har sai mun jira Malamai a Saudiyya sun yi fatawa sun nesanta Musulunci da Boko Haram, domin mu da muke Najeriya mu muka san abinda yake faruwa, da wanda aka dafa a cikin ruwa da wanda aka soya a cikin Mai ai duk labarin wuta suka ji, wanda aka gasa shi ne yaga wuta ganin idanunsa, tuni ya kamata a ce majalisar Koli ta Addinin Musulunci a Najeriya ta fitar da wata gamammiyar Fatawa ta Nesanta Musulunci da ayyukan Ta'addanci da Boko Haram suke yi, su kuma yi Alla-wadai da dukkan wani aiki na ta'addanci da zai kai ga salwantar rayukan da basu ji ba basu gani ba.Amma sai bayan da bango ya tsage!


Zan cigaba In Sha Allah.



11-05-2014

Tsakanin Boko Haram Da Amerika Waye Abin Tsoro?

TSAKANIN AMERIKA DA BOKO HARAM WAYE ABIN TSORO?

Shekara da shekaru 'yan Boko Haram suna kashe mutanen da ba su san hawa ba basu san sauka ba, sun kashe mata, sun kashe maza, sun kashe tsoffi, sun kashe Malamai sun kashe dalibai, sun kashe da dama daga cikin al'umma babu sididi babu sadada akan laifin da jama'a basu aikata ba, aka kawo karshen rayuwarsu ba dan sun zabi hakan ba. sun kashe Musulmi a cikin masallatai kuma suna ikirarin Musulunci! Wannan wane irin musulunci ne haka! Bayan mun san cewa ko a yakin Fathu Makkah, Manzon Allah SAW cewa ya yi duk wani Mushriki da aka bi za'a kashe matukar ya shiga gidan Abu-Sufyan sarkin Makkah na lokacin to ya tsira! To ina ga jinin Musulmi a cikin Masallaci inda yake yin Munajati tsakaninsa da Allah Mahalicci?

Boko Haram sun sanya tsoro da firgici da razani da gigita a cikin zukatan dubban al'ummar da basu san laifin da suka yi ba, sun sanya da dama sun yi hijira sun bar garuruwansu na asalai ba dan suna so ba, sai domin ceton rai, sun tafi sun bar dukiyoyinsu da duk abinda suka mallaka ba dan sun yiwa kowa laifi ba. Sun kona dubban gidajen jama'a, sun bankawa kasuwannin da Musulmi suke neman abinci, sun bankawa Masallatai wuta! Subhanallah.

Boko Haram sun aikata dukkan dangin ta'addanci da zalunci da cin mutunci da cin zarafin dan Adam, kuma duk da haka suna ikirarin Addinin Musulunci suke karewa! Alhali tun daga surar Farko ta Al-Qur'ani har zuwa sura ta karshe babu inda Allah ya yi umarni da kisan ran da bai ji ba bai gani ba irin wanda Boko Haram suke yi. Duk wani Musulmi na gari yasan cewa dukkan aikin ta'addancin da Boko Haram suke aikatawa babu ko daya da ya yi kama da Musulunci, bil hasalima adadin Musulmin da suka rasa rayukansu ta sanadiyar Boko Haram ya ninka ninkim ba ninkim na adadin wadan da ba Musulmi ba da suka rasu ta sanadiyar Boko Haram.

Ciki da wajen Najeriya kowa na Allah wadai da ayyukan ta'addancin Boko Haram ko dai a sarari ko a fake. Addu'ar al'umma a koda yaushe ita ce Allah ya kawo karshen wannan zaman zullumi da razani da Boko Haram suka jefa al'umma ciki dare da rana, birni da kauye.

Zan cigaba In Sha Allah.

YASIR RAMADAN GWALE
09-05-2014

Thursday, May 1, 2014

Zagi Da La'antar Shugabanni A Musulunci!


ZAGI DA LA'ANTAR SHUGABANNI!

Baya daga cikin TARBIYYAH da LADABI na Musulunci da aka samo daga magabata nakwarai tun daga kan SAHABBAN ANNABI S.A.W da kuma wanda suka biyo bayansu da kyautatawa.

Hakika la,antar shuwagabanni koda kuwa ba nagari bane yana tasiri matuka wajen kara lalata sha,aninsu da rashin dai daituwarsu, atarbiyya ta musulunci ko dabba ko abin hawa babur ko mota ba,a bada damar ala,ance su ba domin la,antar zata iya tasiri agaresu.

Hadisi ya tabbata wata rana wani mutum daga cikin sahabbai suna tafiya tareda Manzon Allah s.a.w sai abin hawansa wato rakumin wannan mutumin yake masa gardama da mutumin nan yaga haka sai yace: "ALLAH YA LA,ANCI WANNAN ABIN HAWA NAWA" nan take manzon Allah s.a.w yace asaurara, sai yace da mutumin tunda ka tsinema abin hawanka to sai ka sakeshi ya shiga jeji mu kam bazamu tafi da LA,ANANNE ba, haka dole mutumin nan ya rabuda rakuminsa sabilida ya tsine masa.

To dan uwa wannan fa dabba ce haka ta faru, to ina ga MUTUM? Kuma mutum dinma JAGORA SHUGABA wanda maslaharka mai yawa take hannunsa.

Hakika mu munsan shuwagabanninmu sunyi nesa da adalci sun rungumi zalunci amma kuwa wannan ba dalili bane na zaginsu da la,antarsu! A,a dalili ne na yi musu ADDU,AH akan Allah ya shiryesu ya sanyasu zama masu adalci, ko kuma mu roki Allah ya musanya mana da mafi alkhairinsu.

Wani babban malamin musulunci daga cikin magabata yake cewa: " idan da inada tabbacin wata addu,ah guda daya tak da za,a amsa min idan na roka, to da akan shuwagabanni zanyi wannan addu,ah domin idan shuwagabanni sun gyaru to al,ummah ta gyaru."

Haka nan kada mu manta da cewa in har munason ingantattun shuwagabanni nagari to dole mu mabiya talakawa sai mun inganta kanmu mun zama nagari, hakika alkwarin Allah tabbatacce ne, idan muka gyara to tabbas Allah zai gyara mana, idan kuma muka lalace muka manta da adalci akawunanmu to dole mu samu shuwagabanni kwatankwacinmu, wannan haka Ayoyin Alqur,ani da Hadisan Manzo s.a.w suka tabbatar.

Hakika munyi nesa da adalci akan kanmu, to ta ina kuwa zamu samu shuwagabanni masu adalci? Kowa fa so yake ya samu dama ya dama! Anya kuwa da gaske muketa wannan kururuwa ta rashin adalcin shuwagabanninmu?

Hakika mu gyara sai a gyara mana. Allah ya shiryardamu ya bamu shuwagabanni nagari.

Jibwis Nigeria 
01-05-2014

Taya Murna Ga Dakta Ibrahim Disina


TAYA MURNA GA DAKTA IBRAHIM DISINA

Amadadina da Zainab muna taya Dan uwanmu Malaminmu Sheikh Dakta Ibrahim Disina murnar kammala "munakasharsa" ta Daktora a Jami'ar Usman Dan Fodio UDUS a yammacin wannan rana. Allah ya sanya alheri ya yi masa jagora a rayuwarsa.

Yasir Ramadan Gwale
01-05-2015