SU WAYE MAK’IYAN SAUDIYYA?
Sau da dama masu gaba da Sunnah kan fake da zagi da aibanta kasar Saudiyya a matsayin wata boyayyar hanya da zasu yi sukuwa su yi zamiya akan Ahlussunnah. A tunaninsu idan suka zagi kasar saudiyya kamar sunci fuska ne ga Ahlussunnah. Shi ya sa ko a bara da Saudiyya ta hana wasu daga cikin Alhazan Najeriya damar sauke farali saboda matsalar Muharrami wasu daga cikin masu wannan maruru a cikin zukatansu suka fito da maitarsu a fili, idan suka yi ta rubuce-rubuce na cin-fuska ga kasar ta Saudiyya, ba dan komai ba sai bayyana gabarsu da Sunnah sannan kuma suna da masaniyar cewa kasar ta Saudiyya na da wani matsayi na musamman a wajen Ahlussunnah.
Saudiyya na da muhimmanci a wajen Musulmi ne kasancewar anan manyan biranan duniya guda biyu mafiya tsarki suke wato MAKKAH da MADINA, sannan kuma garin Makkah mai tsarki yake zaman AL-QIBLA ga dukkan Musulmin duniya, haka kuma, nan ne tsatson Addinin Musulunci wanda Annabi Ibrahim Alaihissalam ya fara Assasawa yake; sannan kuma, saudiyya din ce mahaifar fitaccen malamin nan wanda ya jaddada ilimin TAUHIDI ya bayyana tsantsar AQIDAH ta AHLUSSUNNAH wato Sheikh Muhammad Ibn Abdulwahab, kana ya rushe bid’ah, abinda ya sa kullum masu bid’ah ke aibata shi, tare da gainin baikensa akan bayyana gaskiyar Tauhidi da ya yi.
Baya ga wannan kuma, kasar ta saudiyya itace kasa kwaya daya tilo a duk fadin duniya da ta dauki gabarar yada wannan Ilimi na Tauhidi da kadaita Allah da bauta. Saudiyya ta taimakawa Da’awar Sunnah, haka kuma sun taimakawa Da’awar Sheikh Muhammad Bin Abdulwahab wanda MU ahlussunnah ake jinginamu zuwa gareshi inda ake kiranmu da “WAHABIYAWA” saboda rike ilimin Tauhidi da Ahlussunnah muka yi, muna rokon Allah ya kara tabbatar da mu akan Tauhidi da bin Sunnar ManzonSa Salallahu Alaihi Wasallam.
Kasar Saudiyya ita ce kasar da ta dauki nauyin malamanmu da suke karantar da MU addini. Ta basu guraran karo karatu ta dauki dawainiyar karatunsu da bukatunsu, suka kwankwado ilimin Aqida da Tauhidi suka yada mana a nan cikin gida Najeriya, Allah ya saka musu da alheri. Sannan kuma Saudiyyar ke amfani da dumbin dukiyar da ALLAH ya huwace mata wajen ganin ta taimaki wannan Da’awa ta Sunnah.
Irin wannan ta sanya masu gaba da Tauhidi, kan fake da siyasar da ke tsakanin Saudiyya din da kasashen Turai da Amerika wajen cimata zarafi. MU musulmi tuni Allah ya bamu labari a cikin littafinSa mai tsarki al-qur’ani cewar Yahudu da Nasara makiyanmu ne, ba zasu taba yarda da mu ba har sai mun narke mun zama su, wannan kam abu ne da duk Musulmin kirki ya sani kuma ya yi Imani. Haka kuma, a bisa kaddarawarsa Subhanahu-Wata’ala ya sanya rayuwa bata yuwuwa sai da taimakekeniya tsakanin juna, wannan ta sanya sau da dama Musulmi suna da bukatuwa zuwa ga wadan da Ba musulmi ba, haka suma wadan da ba Musulmin ba suna da bukatuwa zuwa ga Musulmi. Duk yadda mutum ya kai ga kiyayya ga Saudiyya ya san da cewa alakar da ke tsakaninta da Turai da Amerika alaka ce da ta shafi harkokin tattalin arziki da wasu mas’uliyyoyi na duniya, babu wata alaka da ta shafi Aqidah ta Addini a tsakaninsu. Allah kuma cikin hukuntawarsa bai haramta yin mu’amala ta kasuwanci tsakanin bangarorin Musulmi da wadan da ba Musulmi ba.
Manyan abokan gabar Saudiyya na farko sune ‘yan SHI”AH. Shakka babu Majusawa mabiya addinin SHI’AH masu bautar son zuciya da kafircewa duk inda gaskiya take basu boye kiyayyarsu da adawarsu ga Saudiyya din ba, ta yadda a kullum suke neman hanyoyin da zasu yi amfani da su wajen yi mata jafa’I da nuna kurakuranta dan sanya shakka ga Musulmi. Shi ya sa masu bidi’ah kan rudu da irin abubuwan da ‘yan SHI’AH kan yada na karairayi da cin mutunci da shaci fadi ga Saudiyya, wanda a bayyane take cewar adawarsu ba wai da Saudi bane adawarsu ga SUNNAR MANZON ALLAH ce.
Yan Shi’ah sune munafukan cikin musulmi sun fake a cikin riga ta Musulunci suna yi masa zagon kasa da fatan rusa shi. Allah kuma ya fada mana cewar ko a cikin Jahannama munafukai sune a can-karkashin wutar Jahannama, wannan yake nuna maka cewa Illar da shi’ah ke da ita har tafi ta Yahudu da Nasara, domin su Yahudawa a Nasarawa baka da wani haufi domin Allah ya gaya mana makiya ne, kuma suma basa boye kiyayyarsu ga addinin Musulunci a mafiya yawancin lokuta, amma su kuma ‘yan Shi’ah suna kokarin nunawa duniya cewa suna tare da Musulmi amma kuma irin yadda suke rusa addinin Musulunci ko Yahudu da Nasara basa rusa addini haka.
Su kuma wadan da suka gafala daga cikin masu bidi’ah suka ksa fahimtar gaskiyar lamura dangane da shi’ah. A kullum kallo suke matsalar Shi’ah tsakaninsu da Ahlussunnah ne kawai, ba matsala bace da ta shafi Musulunci, wanda wannan shine babban kuskuren da suka yi, domin abinda ke cikin kundin Addinin Shi’ah shi ne zubar da jinin duk wani mutum wanda ba dan Shi’ah bane, wannan ya halatta a wajensu, amma da yake suma masu bautar son zuciya ne idonsu ya gafala da ganin zahirin yadda gaskiya take sun kasa fahimtar hakan idanunsu sun makancewa gaskiya. Shi yasa sai kaji mutum yana ikirrin cewa har gara ya karbi umarni daga Washington akan ya karba daga Saudiyya, Wal-Iyazubillah! Amma kuma duk da wannan ikirari bai isa ya tafi Warshington aikin Umra ko Hajji ba.
Mu a gurinmu mabiya dariku ba abokan gabar Sunnah bane na din-din-din. Yan darika ‘yan uwanmu ne Musulmi muna sallah tare da su muna Azumi tare da su muna kuma aikin hajji tare, illa iyaka mun sha bamban a fannoni da dama musamman akan batun Aqidah, domin mu Ahlussunnah munce kada a riki kowa sai Allah, babu wani tsani tsakanin Allah da bawansa a yayinda masu bidi’ah ke ganin ba haka ban e, dole ka riki wani a matsayin tsani, Subhanallah.
Duk da irin wannan gabar ta ‘yan Shi’ah ga Sunnah basu isa su ce aikin Umra ko Hajji a biranen Karbala da Najaf za’a yi ba, dole suke zuwa Makkah da Madina ba wai dan Addinin ne ya kaisu ba, said an yin dodo-rido ga Musulmi su nuna cewa suna tare da Musulmi, alhali duk wani abu da Musulmi suka yi said an Shi’ah ya saba, hatta tsuguno a bandaki a Makkah ko Madina idan Ahlussunnah ya shiga bayan gida to Dan Shi’ah sai ya saba.
Dan haka kamar yadda ‘yan Shi’ah suka kasa boye gabarsu da kiyayyarsu ga Sunnah, muma bama boye kiyayya ga duk wanda ya kaucewa gangariyar koyarwar Addinin Allah ya kaucewa Tauhidi, ya kutso da son zuciya da bautar wani Allah ya yi masa kwaskwarima da sunan cewa addini ne, muna gaba da duk mai irin wannan aqida, zamu yaki wannan Aqida da aka jingina ta ga addini dan rusa Musulunci. Dan haka, duk wanda yake da shakku ya sani a shirye muke mu taimakawa duk wanda zai yaki miyagun mutane ‘Yan shi’ah zamu taimaki duk wanda zai kawar da shi’ah ko waye shi, ko da kuwa idan ya gama yakar Shi’ah kanmu zai dawo; domin gara ka yi yaki da abokin gaba na zahiri wanda ka sanshi ya sanka, da ace kana yaki da abokin gaba, sannan a gefe guda kuma ga wani a tare da kai yana taimakawa abokin gabarka wajen rage masa aiki na rusa addinin Allah.
Daga karshe, Na sake dawo da wanna tambayar SU WAYE MAKI”IYAN SAUDIYYA? Anan ina nufin Saudiyya ba masarautar Saudiyya ba, Sarakunan mutanene kamar sauran jama’a suna da dai-dainsu suna da kurakuransu. Fatanmu shine Allah ya tabbatar da mu akan gaskiya duk inda take, Allah ka hada fuskokinmu da ma’abota gaskiya. Ya Allah ka rusa shirka da Bid’ah.
Yasir Ramadan Gwale
05-08-2013
No comments:
Post a Comment