Saturday, August 3, 2013

ME FADAR SARKIN MUSULMI ZATA CE DANGANE DA MUSULUNTAR AISHA OZEOCHINA!!!


MUNA JIRAN JIN TA BAKIN FADAR SARKIN MUSULMI DANGANE DA MUSULUNTAR AISHA UZOECHINA

Kusan bamu gama bankwana da batun nan na Auren kananan yara ba a 'yan makwannin nan sai kuma ga wani al'amari ya sake kunno kai wanda shima ya yake da Alakala kai tsaye da Musulmi da Musulunci a Najeriya, wato batun Musuluntar wata matashiya Charity da yanzu take amsa sunan Uwar Muminai Nana-Aisha Allah ya kara yarda a gareta. Kamar yadda kowa ya sani a Najeriya ba sabon abu bane aji Kirista ya karbi addinin Musulunci, a kusan ko ina a fadin kasarnan musamman jihohin da suke da rinjayen Musulmi. Haka kuma, kamar yadda kundin tsarin Mulkin kasarnan ya baiwa duk dan Najeriya dama yana da ikon bin duk addinin da yaga dama ba tare da tsangwama ba a cewar kundin Mulkin, wannan ya sanya Musulmi zai iya gina gurin Ibadarsa a duk inda yaga dama, haka suma wadan da ba Musulmi ba, suna da dubban guraran Ibadunsu a cikin garuruwan Musulmi suna ibadunsa ba tare da wata tsangwama ba.

A tarihin Najeriya an shaida al-ummar Musulmi da san zaman lafiya da kwanciyar hankali. Musulmi ba shi da wata damuwa akan kowa matsawar zai samu damar yin ibadarsa da kuma neman abincinsa a fadin kasarnan, haka kuma, Musulmi a Najeriya an shaidesu da kawar da kai da kuma yakana, ana yin abubuwa da dama na takalar Musulmi fada a kasarnan amma Musulmi muna kawar da kai, duk kuwa da cewar mune muke da sama da kashi 65 na al-ummar kasarnan, amma bamu taba tayar da hankalin kowa ba, ka zalika babu inda Musulmi suka je wani garin wadan da ba musulmi ba suka tursasa musu bin koyarwar addinin Musulunci. Sau da dama wadan da kan shiga Musulunci kan bayyana cewa kyawawan Dabi'u da halayya ta Musulunci da hasken Imani da ke tattare da Musulmi ya basu sha'awar shiga Addinin Musulunci, da kuma wani fatahi daga Allah.

Irin wannan kyakykyawar Mu'amala ta Musulmi ta baiwa 'yar uwa Charity sha'awar shiga addinin Islama ba tare da wani ya tursasa mata ba kamar yadda ta bayyana. Amma al'amarin Musuluntar tata yana neman zuwa da wani irin salo da bamu taba ganin irinsa ba a tarihin masu karbar Addinin Musulunci a wannan kasar. Haka kuma, kiri-da-muzu ake neman yiwa Musulmi kwace. Watakila kasancewar Malama Aisha diyar Malamin Addinin Kirista ce shi ya sa batun ya zo da wani irin sabon salo, inda karfi da yaji babu kunya babu tsoron Allah shugaban Kiristocin Najeriya yake maganganu na gatsali da rainin wayo da cin-fuska ga Musulmi akan wannan batu. Oritsejafor ya fito balo-balo yana ikirarin cewar Maimartaba ETSU NUPE Alhaji Yahaya Abubakar ya tursasawa wannan yarinya da Allah ya nufa da shiriya da karbar Addini Musulunci, kuma aka rike ta a fadar maimartaba sarkin, wanda a bayyane yake cewar ita wannan baiwar Allah ta yi bayani cewar babu wanda ya tursasa mata Musulunta, kuma ta nemi mafaka ne a fadar Etsu Nupe dan abinda tace mahaifinta zai halaka ta idan har ta kuskura ta koma gidansa a matsayin Musulma.

Kwatsam kuma sai muka ji Shugaban Kasa ya saka baki akan wannan al'amari na cewa lallai a mayar da wannan yarinya hannun mahaifinta. Wanda sanin kowane sa-bakin shugaban kasa cikin wannan al-amari baya rasa nasaba da ruwa da tsakin da Pasto Oritsejafor ya yi akan batun cewa lallai sai an mayar da wannan yarinya wajen iyayanta, kuma ta Musulunta ne ba akan son ranta ba. Wanda muna da masaniyar cewa yau da Musulmi ne ya zama kirista babu yadda zaka ji Shugaban kasa ya sanya baki a cikin al-amarin, bil-hasali ma sai dai kaji sun fito suna kururwar tsarin Mulki ya bayar da kariya ga mai bin duk addinin da yaga dama.

Hakika Addinin Musuluci ya baiwa Iyaye martaba da darajarsu, Musulmi yana kima tare da martaba Iyayansa ko da ba Musulmi bane, wannan koyarwar Islama ce, amma babu wanda yakai wannan baiwar Allah sanin halin mahaifinta, tunda shi ya haifeta ta kuma taso a hannunsa, ta yi ikirarin cewar zai halaka ta, danme Oritsejafor zai yi ruwa yayi tsaki akan wannan lamari? Dalili saboda diyar dan uwansa Pasto ce, da kuma nuna tsananin gabarsa da kiyayyarsa ga Musulmin kasarnan.

A dan haka muna kira da Babbar Muryar ga fadar Mai Al-Farma Sarkin Musulmi Sultan Sa'adu Abubakar III cewa lallai ne ya sanya baki a cikin wannan al-amari tunda yake wannan baiwar Allah a halin da ake ciki Musulma ce, tana da hakki wajen ganin ankareta daga fadawa halakar da tace ka iya samunta. Haka kuma, Rashin sanya bakin Sarkin Musulmi akan wannan al-amari mummunan hoto yake bayarwa na shugabancinsa a matsayin jagoran Musulmi a wannan kasa. Dan haka ya zama wajibi ga Masarautarsa ta shiga cikin wannan lamari tayi ruwa tayi tsaki wajen ganin ba'a canzawa wannan baiwar Allah tunani da ra'ayi akan abinda ta yi Imani da shi ba. Muna yi mata addu'ah Allah ya tabbatar da Ita akan Addinin Musulunci ya karfafi Imaninta. Allah ya hadamu a cikin Al-Jannarsa madaukakiya gabaki daya.

Yasir Ramadan Gwale
03-08-2013

No comments:

Post a Comment