Saturday, August 24, 2013

El-Zakzaky Ne Babbar Matsalar Tsaro A Najeriya!!!

EL-ZAKZAKY NE BABBAR MATSALAR TSARO A NAJERIYA!!!

Sanin kowa ne cewar ana matukar fama da matsaloli na tabarbarewar tsaro a Najeriya musamman Jihar Arewa inda Musulmi ke da rinjaye. Labaran kashe-kashe da tashin hankali da barazanar salwantar rayuka da dukiyoyi a kusan dukkan jihohin Arewacin Najeriya ba wani sabon abu bane, musamman a wannan mawuyacin lokaci da muke ciki, wanda al'amura kullum sai kara jagulewa suke yi, zubar da jini sai karuwa yake yi, a kullum sai yanka mutane ake yi kamar yadda ake yankan dabbobi a Abbatuwa. Kusan wannan matsalar ta shafi ko ina, yanzu ya zama babu wani waje da yake da Aminci a Arewacin Najeriya, domin tundaga Masallatai da gidajen jama'a da kasuwanni da guraran haduwar jama'a babu wani waje da bai taba samun barazanar tsaro ba, anbi mutane har cikin Masallaci suna Sallah an kashe su kuma WAI an tsere, ba'a kama kowa ba; haka zalika kasuwanni sun sha fama da tashin hankula iri-iri; haka ma, dai-dai kun mutane an sha binsu har cikin gidajensu a yankasu kamar awaki kuma a gudu ba tare da anga ko da kurar mutum ba. Duk wannan barazana da tashin hankali a Arewa ba bakuwa bace kusan idan ana sabo da barazanar tsaro irin wannan to zamu iya cewa wannan to zamu iya cewa an saba da ita.

Zance na gaskiya Barazanar tsaro mafi girma ga Musulmin kasar nan Shine wani mutum da ake kira Ibrahim El-Zakzaky. Hukumomin tsaro ya kamata su yi hattara kuma su shiga taitayinsu, su kuma san abinyi akan wannan mutum, da yake jagorantar tarin marasa Ilimi da wawaye da Talakawa da ba su da cin yau balle na gobe, ga tsananin jahilci. Tabbas Zazzaki barazana ne, domin ya tara mutane a karkashinsa basa yin aiki da umarnin kowa sai nasa, basa jin maganar kowa sai tasa, Shugabannin Siyasa da Sarakuna da Suhagabannin tsaro maganganunsu ba abakin komai suke ba a wajen mabiyan Zazzaki, domin basa karbar umarni daga garesu face abin da Zazzaki ya umarcesu. Bil hasali ma, suna ganin dukkan wadancan bangarorin shugabanni na al'umma a matsayin DAGUTAI, haka shima Zazzakin yana yin gaban kansa wajen bijirewa dukkan wani abu da yake doka ne a kasarnan gabansa gad'i.

Sanin kowane a Arewacin Najeriya, mabiyan Zazzaki basa bin dukkan wata doka da hukumomi suka sanya, walau dan kare dukiya ko kuma dan kare rayukan al'umma. Mabiyan Zazzaki suna karya doka kan su tsaye ba tare da tunin doka ta yi aiki akansu ba, kuma hukumomin tsaro da al'hakinsu ne su tsaya tsayin daka wajen ganin al'umma na bin doka da oda, amma sun zurawa mabiyan zazzaki ido suna yin iya shege da tsakar rana babu kunya babu tsoron Allah suna taka dukkan wata doka da aka sanya. Lallai muna kiran hukumomin tsaro da masu mulki da shugabanninmu, wajibi ne agaresu su takawa Zazzaki birki, akan irin wannan cin kashi da karan tsaye da suke yiwa dokoki. Kuma lallai hukumomi su sani cewar babu yadda za'a yi a zauna lafiya matukar wani bangare na al'umma an barsu suna iya shege da taka doka, hukunci baya hawa kansu. Lallai a kama tare da tuhumar dukkan wanda ya taka dokokin hukuma ko waye shi.

Haka kuma, sanin kowa ne cewar Zazzaki a Azumin da ya gabata ya saba da dukkan Musulmin kasarnan, domin ya dauki Azumi ba tare da iznin hukuma ba, ya kuma baiwa mabiyansa umarni suka bi umarninsa, duk da cewa al'haki ne na sarkin Musulmi ya bayar da sanarwar daukan Azumi ko ajjiyeshi. Amma zakzaky ya kekasa kasa ya yi kunnen uwar shegu ga bin umarnin fadar Sarkin Musulmi. Wannan karara yana nuna cewar Zazzaki zai iya umartar mabiyansa da dukkan abinda yaga dama, duk mutanan da yaga dama yana iya cewa a farmusu kuma ayi hakan, lallai ne hukumomi su ankara su san matakin dauka akan wannan mutum.

Muna gani duk kasarnan babu wani mutum da yake kiran jama'a su fito kantituna kwai da kwarkwata kamar yadda zakzaky ke yi. Zazzaky yana umartar mabiyansa da fitowa a duk lokacin da yaga dama, har da basu umarnin yin tattaki da kafa daga nisan gurare, wanda wannan karara ya sabawa HAKKIN BIL-ADAMA amma anaji ana kallo aka yi shakulatun bangaro da batunsa. Lallai wajibi ne jama'a su fadaka, su sani cewar dole ka kula da 'ya 'yanka wajen ganin basu bi wannan mutumin da yake halakar da su ba, yake raba su da IMANI na hakika, wajen cusa musu wani abu daban da sunan Addini. Sannan kuma, wajibin hukumomi ne su dauki tsauraran matakai akan Zazzaki domin samun zaman lafiyar al'ummar kasarnan. Rashin hakan kuwa jefa kasarnan ne cikin tashin hankalin da yafi duk wanda aka taba fuskanta a baya. Idan kunne yaji . . .!

Yasir Ramadan Gwale
23-08-2013

Sunday, August 18, 2013

HASSADA: Sheikh Abdulwahab Abdallah Kano Ya Ce:


HASSADA: Sheikh Abdulwahhab Abdallah Kano Yace:

Wata rana an tambayi Sheikh Abdulwahab Abdallah dangane da HASSADA. Sai Malam ya yi bayani kamar haka: Ita Hassada wani ciwo ne wanda dukkan 'ya 'yan Adam da Hauwa suna dauke da ita. Malam ya yi bayanin cewar akwai Hassadar da zata iya kai mai yinta zuwa Al-Jannah, Malam ya buga misali da Abubakar Ibnu Abi-Kuhafa RA da Umar Bin Khattab RA, ya ce sun kasance suna yin rige rige wajen aikata ayyukan alkhairi, domin faranta ran Manzon Allah SAW da kuma neman yardar Allah, haka suka dinga rigegeniya wajen ciyar da dukiyarsu. Malam ya kara da ce, akwai daya bangaren Hassada wanda yana kai mai aiktawa zuwa ga Halaka da tashin hankali a ranar kiyama, Malam ya cigaba da cewa, daya bangaren shi ne mummunar Hassada wadda ta ke dauke da kyashi da bakinciki da mummunar niyya, ya ce, mummunar Hassada kusan a yanzu ita ta fi damun wannan al'ummar tamu, ta yadda Malamai da Sarakuna da 'yan Siyasa da Masu kudi da Dalibai da Masu yin Facebook da sauransu da dama kanci duniduniyar juna dan ganin bayan juna wajen aikata alkhairi, Malam ya cigaba da cewar hanyar da Mutum zai rage radadi da kafin Hassada a tare da shi shi ne ya dinga kokarin tunawa zuciyarsa Allah da shagaltar da ita zuciyar da zikiri da karatun al-kur'ani da tadabburi da shi. Daga karshe Malam ya kara Jaddada cewar dukkanmu muna da dauke da Hassada a zukatanmu sai dai wani yana iya danne zuciyarsa a duk lokacin da Hassadarsa ta motsa, wani kuwa baya iya jurewa har sai ya bayyana Hassadarsa a Fili, ta yadda Jama'a zasu dinga cewar wane kaza yana da Hassada. Allah ka bamu ikon danne zukatanmu.

Yasir Ramadan Gwale
18-08-2013

Gabas Ta Tsakiya: Anya Za A Zauna Lafiya Israela Na Kallo?

GABAS TA TSAKIYA: ANYA ZA'A ZAUNA LAFIYA ISRAELA NA KALLO?

Zai yi wahala a samu zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya alhali kasar Israela na wajen. Kada ka ji da wai duk wata rikita rikita da ke faruwa a kasashen larabawa akwai hannun Israela da uwar gijiyarta Amerika a ciki. Sanin kowa ne cewa Israela wata tsokar Nama ce a jikin Amerika, wacce Amerika ba zata iya wani amfani ba tare da aikin wannan tokar naman ba, zaka iya kwatanta ta da "zuciya", a takaice ana tafiyar da harkokin Siyasar Amerika ne kai tsaye daga Warshington da New York kamar yadda ake baiwa Amerika umarni kai tsaye daga Tel Aviv su karba ba tare da wata tirjiya ba, su biyun sashinsu yana taimakawa sashi. Israela ba zata taba bari a zauna lafiya ba a yankin gabas ta tsakiya, domin kuwa suna da masaniyar cewar Indai kasashen Larabawa suna zaune lafiya, tilar ayi maganar samar da 'yantacciyar kasar Palasdinu, domin kaucewa wannan batu da baya yiwa Tel Aviv da Warshington dadi, ya sa dole su shirya yadda yankin zai yamutse da rikici da hayaniya. Sannan su kuma rarraba tsakanin kasashen a siyasance.

Da farko idan ka kalli kasar Siriya, kusan shekara biyu kenan ana yin abu guda daya, mutum daya dan isaka ya zama masifa! Wato abin da yake faruwa a Siriya shine, su Turai da Amerika da Israela basa son rikicin Siriya ya zo karshe nan kusa, haka kuma, basa son ko da rikicin ya kare a samu wanda yayi galaba akan wani, Basa son Assad dan Ta'adda ya samu Nasara duk da suna tare da shi a bayan fage, sannan kuma basa fatan Free Syrian Army su sami nasara akan Assad, domin a tsarinsu kamar kware musu bayane tunda sun ayyana goyon bayansu a garesu, wanda goyon baya ne mai cike da yaudara, da jan kafa. Duk da wannan abin da yake faruwa a Siriya Israela da Amerika sun gwammace Assad ya cigaba da kasancewa a matsayin shugaban Siriya domin ko babu komai suna da masaniyar ba zai tayar da batun tsaunukan Golan da Israela ta mamaye ba; sannan suna tsoro kada su mara cikakken goyon baya ga FSA su kafa gwamnati a samu mai kishin addinin da zai saba da manufofin Israela a gabas ta tsakiya, wanda wannan shine hakikanin abinda zai faru, amma idan banda haka awanni ashirin da hudu sunyi yawa Amerika ta hambarar da Assad.

Na biyu kuma, idan ka kalli Masar, suna tsoron samun Nasararsar Muhammad Mursi a matsayin halastacce shugaban Masar bisa doron Dimokaradiyya, wanda hakan babban koma baya ne ga Israela. Domin ba tare da wani boye boye ba, Mursi ya nuna baya tare da Israela, kamar yadda tsohuwar Gwamnatin Sadat da ta Mubarak suka d'asa da Isreala, dan haka suka yi dukkan mai yuwuwa dan kifar da gwamnatinsa. Kuma kifar da gwamnatin Mursi ba shi kadai ne abinda zasu yi su koma su zauna ba, zasu kasa su tsare su tabbatar kasar ta yi rincabewar da duk wani mai kishin Addini bai samu irin damar da Mursi ya samu ba. Dan haka duk wannan abin da yake faruwa wanda ake amfani da su Sisi da Bublawai da ElBaradie an riga an gama shirya shi dan rikita kasar. Allah ya kawowa Misrawa dauki cikin kaddararwarsa.

A gefe guda kuma sauran kasashen Larabawa suma suna bayar da nasu taimakon wajen ganin, Masar bata samu Nutsuwar da zata baiwa Ikhwan dawowa kan karagar Mulki ba, domin suma suna da masaniyar cewar Matukar MB suka samu nasarar gwamnati a masar kashin kasashen Saudiyya, da Kuwaiti, da Qatari, da Bahrain, da Abu Dhabi ya bushe, dole guguwar siyasa ta kada a kasashen, abinda ba zai taba yi musu dadi ba, dan haka ba zai taba yuwuwa ba su nade hannu su kyale Ikhwan ta samu Nasara a Masar! Allah ya basu Nasara.

Sannan kasashen Gabas ta tsakaiya gabaki dayansu ba suda gaskiya. Musamman akan siyasarsu ta Diplomasiyya wadda ake kira Foreign Policy, domin dukkansu babu kasar da take da wata manufa ta Allah da kuma kare addinin Allah a bisa hakikanin lamura, ko da akwai manufar addini to siyasarsu ta kashin kansu ta rinjayi siyasar Addini. Wannan wani al'amari ne mai girma kuma mai fadi! Watakila wani ya zargi Alakar wadannan kasashe da Amerika, Eh kana da 'yancin zarginsu akan alakarsu da Amerika, amma abu ne sananne cewar Amerika tana da bukata a gabas ta tsakiya, kuma sannan tana da kudi a gindinta; suma haka kasashen suna da bukata ga Amerika domin suna da haja da suke samun kudi suke juya siyasar Khalij yadda suka ga dama.

Babu yadda Israela zata kasa wanzuwa a yankin gabas ta tsakiya matukar Akwai Amerika. Idan kana bukatar kawar da kasar Israela daga doron kasa sai ka tabbatar ka share Amerika sannan ka iya kawar da Israela, amma duk wani abu da ba wannan ba, to sunansa dodo-rido, anan zaka zargi kasar IRAN kasan cewar duk ihun da suke yi karyar banza ce akan Israela babu wani abu da zasu iya yi, hasalima bakinsu daya da Israelar wajen rikita lamura da kuma rikita kasashen sunni da sanya musu rashin Nutsuwa, haka kuma, duk da gazawar kasashen Sunni sunyi rawar gani a wasu fannoni sun kuma dirka abin kunya a wasu fannonin, amma dai sunfi IRAN nesa ba kusa ba.

Waye zai iya yakar Amerika? A wannan zamani da muke cikin karni na 21 karfin soja ya zama zancen banza. Yanzu lokacin karfin soja ya wuce, domin ana aiki da karfin fasaha ne, Soja yana zaune a cikin bairiki zai tura jirgin sama mara matuki ya kashe duk mutanan da yaga dama ya dawo, kaga duk rawar daji da tsalle-tsalle na soja sun zama zancen banza, domin abokin karon nasa ma baya ganinsa amma shi yana hangoshi. Babu wata kasa da zata iya yakar Amerika alhali bata da iko akan Bankin Duniya, da IMF da Majalisar Dinkin Duniya da kuma NATO. Babu wata kasa da zata iya karawa da Amerika ta yi galaba akanta matukar bata da ikon mallakar wadannan janibai da muka zayyana. Amerika kuwa na da iko akansu sama da kowacce kasa. Ko Rasha da take ganin sunyi kafada da Amerika sai dai su yi kare jini biri jini.

Fatanmu shi ne Allah ya zama gatan bayinsa na gari a duk inda suke. Allah ka taimaki Addinin Musulunci da masu taimakonsa a zahiri da fake. Allah ka Amintar da mu a cikin kasashenmu.

Yasir Ramadan Gwale
15-08-2013

Friday, August 9, 2013

SHEIKH (Dr.) MUHAMMAD SANI UMAR RIJIYAR LEMO: Bijimin Malamin Sunnah!!!



SHEIKH (Dr.) MUHAMMAD SANI UMAR RIJIYAR LEMO: Bijimin Malamin Sunnah!!!

Tun da nake ban taba ganin mutumin da Marigayi sheikh Jaafar yake girmamawa a gaban idonsa da bayan idonsa kamar Dr. Sani ba.Tun lokacin da Allah ya yiwa Dr. Sani dawowa gida Najeriya daga Saudiyya, Sheikh Jaafar ya gabatar da shi gabatarwa mai kyau a Masallacin Usman BIn Affan, ya yaba masa ya kuma nunawa jama'a irin kwazo da fikra da baiwa da Allah ya yiwa wannan bawan Allah, ta ilimin Hadisi da sauran Ilmai. Sannan kuma, na lura da yadda Malam Jaafar yake girmama Dr. Sani matukar girmamawa, girmamawa ta Ilmi, ban sake tsinkewa da al'amarin wannan bawan Allah ba sai ranar wata Asabar Dr. Sani yana karantar da littafin Tajridussareh a Usman Bin Affan Malam Jaafar yazo domin sauraron karatun, a hanyarsa ta shigowa masallaci ya tarar da wasu makusantan dalibansa suna hira basa sauraron karatun a zaune a kan benci, a wannan lokacin Malam ya yi musu fada, yana nuna musu irin hasarar da suke ta Ilimin da Dr. Sani yake bayarwa.

Hakika, duk wanda ya saurari karatuttukan Dr. Sani yasan dacewa Allah ya ajiye Ilimi a cikin kirjin wannan bawan Allah.  Idan yana yi maka tafsirin Al-qur'ani kai ka ce daman can Al-Qur'anin ya karanta. Allah ya yiwa Dr. Sani baiwa mai yawan gaske, wadda wasu da dama daga cikin daliban ilimi sun sani, wasu kuma sai nan gaba zasu fahimta; Allah ya huwacewa Dr. Balagar iya tsara zance, a cikin hikima da nutsuwa da kwanciyar hankali. Dr. Sani shi ne mutumin da zai daureka da Ilimi da hujjoji da nassoshi wadan da wallahi baka isa ka kunce ba. Zaka rantse da Allah Dr. Sani daman can karatun Tafseer ya yi a iyakar zamansa a Madina, irin yadda yake yin Tafsiri da Ilimi da fayyace bayani dalla-dalla; haka idan ka dauki bangaren Fiqhu sai ka dauka gaba daya rayuwarsa ilimin fiqhu ya karanta, domin duk fatawarda Dr. Sani ya bayar zai yi wahala wani ya kayar da shi a kan wannan fatawa da Ilimi sai dai da son zuciya; wata rana ina Masallacin Al-furqan wani Bawan Allah ya zowa da Dr. Bashir Aliyu Umar da fatawa a daidai lokacin da akace za'a yi hawan arfa a Makkah, sannan za'a yi Idin Layyah a Najeriya, abinda Dr. Bashir yace a lokacin shin meye fatwar Dr. Sani akan wannan matsalar! Wannan ya kara tabbatar da tumbatsar Dr. Sani a fage na Ilimi, duk da cewa Dr. Bashir shima masanin Hadisi ne da fiqhu gangaran, amma sai da ya girmama Ilimin Dr. Sani. 

Haka kuma, duk wanda ya saurarin Khdbar Dr. Sani a ranar da aka kashe Sheikh Jaafar Allah ya kai rahama gareshi, zai san cewa Allah ya baiwa wannan bawan Allah zalakar iya zance da kwantarwa da jama'a hankali a daidai lokacin da hankalinsu ya dugunzuma ya tashi, ya yi maganganu na Ilimi cikin hikima hankalin mutane ya kwanta, ba tare da samun wata hatsaniya ko husuma ba, wallahi samun wanda zai iya shawo kan mutane a wannan lokacin sai an tona. Bayan haka, duk wanda yake sauraron Khudbar Dr. Sani zai sake tsinkewa da al'amarinsa ta yadda yake Khudbah a cikin nutsuwa ga Balagar sarrafa harshen larabci kai ka ce daman can Larabci shi ne harshensa na farko. Dukkan daliban da suke karatu wajen Dr Sani hakika su shaida ne akan irin baiwa ta Ilimi da harshen larabci  da Allah ya huwacewa wannan bawan Allah.

Mutum ne mai saukin lamari, ga saukin kai, ga iya mu'amala da mutane. Zaka jin-jinawa Dr. Sani irn yadda yake da sakin fuska da walwala da jama'a musamman dalibansa, yadda yake kusantarsu da Ilimi, idan kana tattaunawa da shi har baka so wani tsaiko ya shiga tsakaninku, saboda irin yadda yake fayyace maka lamura dalla-dalla, na rayuwa da kuma na ilimi. Wani malami yace wallahi mutanan Kano da sun san waye Dr. Sani wallahi da ba za su taba yin sakaci da bibiyar majalisan karatunsa ba, domin irin yadda yake barin ilimi, abin sai wanda ya gani. Wannan abu ne bayyananne duk wadan da suke da kusanci da Dr. sun san da haka.

Sannan idan ka tabo janibin Aqidah, Ya Salam! Wallahi Dr. Sani gwani ne na gwanye a wannan fage, ya sha ya tumbatsa a fannin Aqidah. Duk wanda ya saurari karatun littafin Al-Ubudiyya zai gasgata wannan zance, wannan karatu kusan yafi tayarwa da 'yan Bidi'ah hankali a baya-bayannan, domin karyar mai karya ya iya kayarda maganganun Dr. Sani da magana ko bayani na Ilimi, wallahi mutum ne ko da me kazo ya sha gabanka, shi yasa da zaka tambayi 'yan Bid'ah gaskiyar lamari wanne Malami ne yafi tayar musu da hankali zasu tabbatar maka cewa Dr. Sani ne, domin baya ga magana ta hankali da zai rudawa rudadde tunani, sannan kuma, ga Ilimi madararsa.

Ya Allah ka tsawaita rayuwar Dr. Sani a duniya, Ya Allah ka amfanar da al'ummar Musulmi da dumbin Ilmin da ka huwacewa wannan bawa naka. Allah ka sanya Albarka a cikin Iliminsa da rayuwarsa da zurriyarsa.

Yasir Ramadan Gwale 
09-08-2013

Sunday, August 4, 2013

Su Waye Makiyan Saudiyya???

SU WAYE MAK’IYAN SAUDIYYA?

Sau da dama masu gaba da Sunnah kan fake da zagi da aibanta kasar Saudiyya a matsayin wata boyayyar hanya da zasu yi sukuwa su yi zamiya akan Ahlussunnah. A tunaninsu idan suka zagi kasar saudiyya kamar sunci fuska ne ga Ahlussunnah. Shi ya sa ko a bara da Saudiyya ta hana wasu daga cikin Alhazan Najeriya damar sauke farali saboda matsalar Muharrami wasu daga cikin masu wannan maruru a cikin zukatansu suka fito da maitarsu a fili, idan suka yi ta rubuce-rubuce na cin-fuska ga kasar ta Saudiyya, ba dan komai ba sai bayyana gabarsu da Sunnah sannan kuma suna da masaniyar cewa  kasar ta Saudiyya na da wani matsayi na musamman a wajen Ahlussunnah.

Saudiyya na da muhimmanci a wajen Musulmi ne kasancewar anan manyan biranan duniya guda biyu mafiya tsarki suke wato MAKKAH da MADINA, sannan kuma garin Makkah mai tsarki yake zaman AL-QIBLA ga dukkan Musulmin duniya, haka kuma, nan ne tsatson Addinin Musulunci wanda Annabi Ibrahim Alaihissalam ya fara Assasawa yake; sannan kuma, saudiyya din ce mahaifar fitaccen malamin nan wanda ya jaddada  ilimin TAUHIDI ya bayyana tsantsar AQIDAH ta AHLUSSUNNAH wato Sheikh Muhammad Ibn Abdulwahab, kana ya rushe bid’ah, abinda ya sa kullum masu bid’ah ke aibata shi, tare da gainin baikensa akan bayyana gaskiyar Tauhidi da ya yi.

Baya ga wannan kuma, kasar ta saudiyya itace kasa kwaya daya tilo a duk fadin duniya da ta dauki gabarar yada wannan Ilimi na Tauhidi da kadaita Allah da bauta. Saudiyya ta taimakawa Da’awar Sunnah, haka kuma sun taimakawa Da’awar Sheikh Muhammad Bin Abdulwahab wanda MU ahlussunnah ake jinginamu zuwa gareshi inda ake kiranmu da “WAHABIYAWA” saboda rike ilimin Tauhidi da Ahlussunnah muka yi, muna rokon Allah ya kara tabbatar da mu akan Tauhidi da bin Sunnar ManzonSa Salallahu Alaihi Wasallam.

Kasar Saudiyya ita ce kasar da ta dauki nauyin malamanmu da suke karantar da MU addini. Ta basu guraran karo karatu ta dauki dawainiyar karatunsu da bukatunsu, suka kwankwado ilimin Aqida da Tauhidi suka yada mana a nan cikin gida Najeriya, Allah ya saka musu da alheri. Sannan kuma Saudiyyar ke amfani da dumbin dukiyar da ALLAH ya huwace mata wajen ganin ta taimaki wannan Da’awa ta Sunnah.

Yana da kyau al-ummah su sani kuma su fahimta Saudiyya kasace kamar sauran kasashen Duniya. Kamar yadda kowacce kasa take da harkokin gudanarwa da yanayin siyasarta da tattalin arzikinta da huldodinta na jakadanci, haka itama saudiyya na da nata harkokin gudanarwar na cikin gida da kuma na kasashen waje. Mu Ahlussunnah ba muna kare siyasar kasar Saudiyya bane musamman alakarta da kasashen Yamma ko Turai da Amerika, muna amfani da mizani na Adalci wajen kallon irin kokarin da kasar ta saudiyya take yi wajen yi mata hukunci da kuma bata uzuri a wasu lokuta.

Irin wannan ta sanya masu gaba da Tauhidi, kan fake da siyasar da ke tsakanin Saudiyya din da kasashen Turai da Amerika wajen cimata zarafi. MU musulmi tuni Allah ya bamu labari a cikin littafinSa mai tsarki al-qur’ani cewar Yahudu da Nasara makiyanmu ne, ba zasu taba yarda da mu ba har sai mun narke mun zama su, wannan kam abu ne da duk Musulmin kirki ya sani kuma ya yi Imani. Haka kuma, a bisa kaddarawarsa Subhanahu-Wata’ala ya sanya rayuwa bata yuwuwa sai da taimakekeniya tsakanin juna, wannan ta sanya sau da dama Musulmi suna da bukatuwa zuwa ga wadan da Ba musulmi ba, haka suma wadan da ba Musulmin ba suna da bukatuwa zuwa ga Musulmi. Duk yadda mutum ya kai ga kiyayya ga Saudiyya ya san da cewa alakar da ke tsakaninta da Turai da Amerika alaka ce da ta shafi harkokin tattalin arziki da wasu mas’uliyyoyi na duniya, babu wata alaka da ta shafi Aqidah ta Addini a tsakaninsu. Allah kuma cikin hukuntawarsa bai haramta yin mu’amala ta kasuwanci tsakanin bangarorin Musulmi da wadan da ba Musulmi ba.

Manyan abokan gabar Saudiyya na farko sune ‘yan SHI”AH. Shakka babu Majusawa mabiya addinin SHI’AH masu bautar son zuciya da kafircewa duk inda gaskiya take basu boye kiyayyarsu da adawarsu ga Saudiyya din ba, ta yadda a kullum suke neman hanyoyin da zasu yi amfani da su wajen yi mata jafa’I da nuna kurakuranta dan sanya shakka ga Musulmi. Shi ya sa masu bidi’ah kan rudu da irin abubuwan da ‘yan SHI’AH kan yada na karairayi da cin mutunci da shaci fadi ga Saudiyya, wanda a bayyane take cewar adawarsu ba wai da Saudi bane adawarsu ga SUNNAR MANZON ALLAH ce.

Yan Shi’ah sune munafukan cikin musulmi sun fake a cikin riga ta Musulunci suna yi masa zagon kasa da fatan rusa shi. Allah kuma ya fada mana cewar ko a cikin Jahannama munafukai sune a can-karkashin wutar Jahannama, wannan yake nuna maka cewa Illar da shi’ah ke da ita har tafi ta Yahudu da Nasara, domin su Yahudawa a Nasarawa baka da wani haufi domin Allah ya gaya mana makiya ne, kuma suma basa boye kiyayyarsu ga addinin Musulunci a mafiya yawancin lokuta, amma su kuma ‘yan Shi’ah suna kokarin nunawa duniya cewa suna tare da Musulmi amma kuma irin yadda suke rusa addinin Musulunci ko Yahudu da Nasara basa rusa addini haka.

Su kuma wadan da suka gafala daga cikin masu bidi’ah suka ksa fahimtar gaskiyar lamura dangane da shi’ah. A kullum kallo suke matsalar Shi’ah tsakaninsu da Ahlussunnah ne kawai, ba matsala bace da ta shafi Musulunci, wanda wannan shine babban kuskuren da suka yi, domin abinda ke cikin kundin Addinin Shi’ah shi ne zubar da jinin duk wani mutum wanda ba dan Shi’ah bane, wannan ya halatta a wajensu, amma da yake suma masu bautar son zuciya ne idonsu ya gafala da ganin zahirin yadda gaskiya take sun kasa fahimtar hakan idanunsu sun makancewa gaskiya. Shi yasa sai kaji mutum yana ikirrin cewa har gara ya karbi umarni daga Washington akan ya karba daga Saudiyya, Wal-Iyazubillah! Amma kuma duk da wannan ikirari bai isa ya tafi Warshington aikin Umra ko Hajji ba.  

Mu a gurinmu mabiya dariku ba abokan gabar Sunnah bane na din-din-din. Yan darika ‘yan uwanmu ne Musulmi muna sallah tare da su muna Azumi tare da su muna kuma aikin hajji tare, illa iyaka mun sha bamban a fannoni da dama musamman akan batun Aqidah, domin mu Ahlussunnah munce kada a riki kowa sai Allah, babu wani tsani tsakanin Allah da bawansa a yayinda masu bidi’ah ke ganin ba haka ban e, dole ka riki wani a matsayin tsani, Subhanallah.

Duk da irin wannan gabar ta ‘yan Shi’ah ga Sunnah basu isa su ce aikin Umra ko Hajji a biranen Karbala da Najaf za’a yi ba, dole suke zuwa Makkah da Madina ba wai dan Addinin ne ya kaisu ba, said an yin dodo-rido ga Musulmi su nuna cewa suna tare da Musulmi, alhali duk wani abu da Musulmi suka yi said an Shi’ah ya saba, hatta tsuguno a bandaki a Makkah ko Madina idan Ahlussunnah ya shiga bayan gida to Dan Shi’ah sai ya saba.

Dan haka kamar yadda ‘yan Shi’ah suka kasa boye gabarsu da kiyayyarsu ga Sunnah, muma bama boye kiyayya ga duk wanda ya kaucewa gangariyar koyarwar Addinin Allah ya kaucewa Tauhidi, ya kutso da son zuciya da bautar wani Allah ya yi masa kwaskwarima da sunan cewa addini ne, muna gaba da duk mai irin wannan aqida, zamu yaki wannan Aqida da aka jingina ta ga addini dan rusa Musulunci. Dan haka, duk wanda yake da shakku ya sani a shirye muke mu taimakawa duk wanda zai yaki miyagun mutane ‘Yan shi’ah zamu taimaki duk wanda zai kawar da shi’ah ko waye shi, ko da kuwa idan ya gama yakar Shi’ah kanmu zai dawo; domin gara ka yi yaki da abokin gaba na zahiri wanda ka sanshi ya sanka, da ace kana yaki da abokin gaba, sannan a gefe guda kuma ga wani a tare da kai yana taimakawa abokin gabarka wajen rage masa aiki na rusa addinin Allah. 

Daga karshe, Na sake dawo da wanna tambayar SU WAYE MAKI”IYAN SAUDIYYA? Anan ina nufin Saudiyya ba masarautar Saudiyya ba, Sarakunan mutanene kamar sauran jama’a suna da dai-dainsu suna da kurakuransu. Fatanmu shine Allah ya tabbatar da mu akan gaskiya duk inda take, Allah ka hada fuskokinmu da ma’abota gaskiya. Ya Allah ka rusa shirka da Bid’ah.

Yasir Ramadan Gwale
05-08-2013


Saturday, August 3, 2013

ME FADAR SARKIN MUSULMI ZATA CE DANGANE DA MUSULUNTAR AISHA OZEOCHINA!!!


MUNA JIRAN JIN TA BAKIN FADAR SARKIN MUSULMI DANGANE DA MUSULUNTAR AISHA UZOECHINA

Kusan bamu gama bankwana da batun nan na Auren kananan yara ba a 'yan makwannin nan sai kuma ga wani al'amari ya sake kunno kai wanda shima ya yake da Alakala kai tsaye da Musulmi da Musulunci a Najeriya, wato batun Musuluntar wata matashiya Charity da yanzu take amsa sunan Uwar Muminai Nana-Aisha Allah ya kara yarda a gareta. Kamar yadda kowa ya sani a Najeriya ba sabon abu bane aji Kirista ya karbi addinin Musulunci, a kusan ko ina a fadin kasarnan musamman jihohin da suke da rinjayen Musulmi. Haka kuma, kamar yadda kundin tsarin Mulkin kasarnan ya baiwa duk dan Najeriya dama yana da ikon bin duk addinin da yaga dama ba tare da tsangwama ba a cewar kundin Mulkin, wannan ya sanya Musulmi zai iya gina gurin Ibadarsa a duk inda yaga dama, haka suma wadan da ba Musulmi ba, suna da dubban guraran Ibadunsu a cikin garuruwan Musulmi suna ibadunsa ba tare da wata tsangwama ba.

A tarihin Najeriya an shaida al-ummar Musulmi da san zaman lafiya da kwanciyar hankali. Musulmi ba shi da wata damuwa akan kowa matsawar zai samu damar yin ibadarsa da kuma neman abincinsa a fadin kasarnan, haka kuma, Musulmi a Najeriya an shaidesu da kawar da kai da kuma yakana, ana yin abubuwa da dama na takalar Musulmi fada a kasarnan amma Musulmi muna kawar da kai, duk kuwa da cewar mune muke da sama da kashi 65 na al-ummar kasarnan, amma bamu taba tayar da hankalin kowa ba, ka zalika babu inda Musulmi suka je wani garin wadan da ba musulmi ba suka tursasa musu bin koyarwar addinin Musulunci. Sau da dama wadan da kan shiga Musulunci kan bayyana cewa kyawawan Dabi'u da halayya ta Musulunci da hasken Imani da ke tattare da Musulmi ya basu sha'awar shiga Addinin Musulunci, da kuma wani fatahi daga Allah.

Irin wannan kyakykyawar Mu'amala ta Musulmi ta baiwa 'yar uwa Charity sha'awar shiga addinin Islama ba tare da wani ya tursasa mata ba kamar yadda ta bayyana. Amma al'amarin Musuluntar tata yana neman zuwa da wani irin salo da bamu taba ganin irinsa ba a tarihin masu karbar Addinin Musulunci a wannan kasar. Haka kuma, kiri-da-muzu ake neman yiwa Musulmi kwace. Watakila kasancewar Malama Aisha diyar Malamin Addinin Kirista ce shi ya sa batun ya zo da wani irin sabon salo, inda karfi da yaji babu kunya babu tsoron Allah shugaban Kiristocin Najeriya yake maganganu na gatsali da rainin wayo da cin-fuska ga Musulmi akan wannan batu. Oritsejafor ya fito balo-balo yana ikirarin cewar Maimartaba ETSU NUPE Alhaji Yahaya Abubakar ya tursasawa wannan yarinya da Allah ya nufa da shiriya da karbar Addini Musulunci, kuma aka rike ta a fadar maimartaba sarkin, wanda a bayyane yake cewar ita wannan baiwar Allah ta yi bayani cewar babu wanda ya tursasa mata Musulunta, kuma ta nemi mafaka ne a fadar Etsu Nupe dan abinda tace mahaifinta zai halaka ta idan har ta kuskura ta koma gidansa a matsayin Musulma.

Kwatsam kuma sai muka ji Shugaban Kasa ya saka baki akan wannan al'amari na cewa lallai a mayar da wannan yarinya hannun mahaifinta. Wanda sanin kowane sa-bakin shugaban kasa cikin wannan al-amari baya rasa nasaba da ruwa da tsakin da Pasto Oritsejafor ya yi akan batun cewa lallai sai an mayar da wannan yarinya wajen iyayanta, kuma ta Musulunta ne ba akan son ranta ba. Wanda muna da masaniyar cewa yau da Musulmi ne ya zama kirista babu yadda zaka ji Shugaban kasa ya sanya baki a cikin al-amarin, bil-hasali ma sai dai kaji sun fito suna kururwar tsarin Mulki ya bayar da kariya ga mai bin duk addinin da yaga dama.

Hakika Addinin Musuluci ya baiwa Iyaye martaba da darajarsu, Musulmi yana kima tare da martaba Iyayansa ko da ba Musulmi bane, wannan koyarwar Islama ce, amma babu wanda yakai wannan baiwar Allah sanin halin mahaifinta, tunda shi ya haifeta ta kuma taso a hannunsa, ta yi ikirarin cewar zai halaka ta, danme Oritsejafor zai yi ruwa yayi tsaki akan wannan lamari? Dalili saboda diyar dan uwansa Pasto ce, da kuma nuna tsananin gabarsa da kiyayyarsa ga Musulmin kasarnan.

A dan haka muna kira da Babbar Muryar ga fadar Mai Al-Farma Sarkin Musulmi Sultan Sa'adu Abubakar III cewa lallai ne ya sanya baki a cikin wannan al-amari tunda yake wannan baiwar Allah a halin da ake ciki Musulma ce, tana da hakki wajen ganin ankareta daga fadawa halakar da tace ka iya samunta. Haka kuma, Rashin sanya bakin Sarkin Musulmi akan wannan al-amari mummunan hoto yake bayarwa na shugabancinsa a matsayin jagoran Musulmi a wannan kasa. Dan haka ya zama wajibi ga Masarautarsa ta shiga cikin wannan lamari tayi ruwa tayi tsaki wajen ganin ba'a canzawa wannan baiwar Allah tunani da ra'ayi akan abinda ta yi Imani da shi ba. Muna yi mata addu'ah Allah ya tabbatar da Ita akan Addinin Musulunci ya karfafi Imaninta. Allah ya hadamu a cikin Al-Jannarsa madaukakiya gabaki daya.

Yasir Ramadan Gwale
03-08-2013

LABARIN ALHAJI KABIRU TANIMU MAI TAYAR DA HANKALI


WANI LABARI MAI TAYAR DA HANKALI

Alhaji Kabiru Tanimu, mutum ne da Allah ya yiwa arziki, ya mallaki abin duniya fiye da duk yadda mai misali ya kai da iya misaltawa. Alhaji Kabiru Tanimu, yana kasuwancin Gahawa, Citta, Kanimfari, Masoro, Tafarnuwa, Ganyen-Shayi da zobo-rodo a kasashen Kenya, Afurka-Ta-Tsakiya, Nijar, Tchadi, Sudan, Indiya, Chana, Singarore, Malaysiya da kuma kasashen Turai da Amerika, Alhaji Kabiru Tanimu, yana da manyan gonakin Noma wadannan kayan da yake kasuwancinsu a kasashe da dama, haka kuma, yana da manyan dakunan adana wadannan kaya a Najeriya da Nijar da sauran kasashe da dama, sannan kuma yana da kamfanunuwa na sarrafa su a Chana da Singapore da Indiya da kuma Najeriya, wannan ta sanya Alhaji ba shi da wani lokacin kansa, shi yasa kullum yana kan hanya daga wannan kasa zuwa waccan kasa.

Allah cikin kudurarsa ya sanyawa Alhaji Kabiru Tanimu zuciyar taimako. Yana da san taimakawa masu karamin karfi da gajiyayyu da masu bukata, yana kyauta baya gajiyawa, kullum hannunsa a bude yake, duk wad’an da suka san Alhaji sun shaideshi akan haka; sannan kuma mutum ne mai kula da Sallah, baya sake da lokacin Sallah a duk inda yake, haka idan lokacin Azumi ya zo gidan Alhaji kan cika makil da mutane daga masu karbar buhun-hunan kayan abinci zuwa masu karbar kudi da kayan sawa da dai sauransu.

Alhaji Kabiru Tanimu, yana da matan aure guda uku, dukkanninsu suna zaune a kasashe daban-daban, domin matarsa ta farko tana birnin Kano a Najeriya, ta biyu na Saudi Arebiya ta ukun kuma na kasar Malaysiya. Saboda irin yanayin kasuwancin Alhaji ya sa, sai ya shafe tsawon watanni hudu zuwa biyar bai tako Najeriya ba, gidansa kuwa babu wani abun bukata da iyalansa suke nema da yake yankewa, ga motoci na Alfarma ga dukkan abubuwan bukata na rayuwa, ‘yan aiki kuwa kowanne yana yin hidimar gabansa, tun daga masu share gida, wankin mota, ban ruwan fulawa, masu gadi da sauransu.

Hajiya Samira itace matar Alhaji ta farko, sun shafe kusan shekaru goma sha biyar da Aure, amma d’a d’aya Allah ya albarkace su da shi mai suna Faisal dan shekaru takwas, wannan yaron na Alhaji shine babban dansa yana samun kulawa ta musamman daga wajen Alhaji yana matukar ji dashi, ana kula da karatunsa da dukkan bukatun rayuwarsa, yaro ne dan lukurkuti daga ka ganshi kasan ya sha madara babu wata alamar wahala ko gajiya a tare da shi; shima Faisal duk da kasancewarsa Yaro ya dauko halin mahaifinsa wajen sakin fuska da wasa da dariya da san yin mu’amala da sauran yara, domin Faisal ko abinci baya yarda ya ci shi kadai sai ya gayyato sauran yara abokansa, suci su sha su yi kokaye-kokayensa na kuruci dangin hauka.

Wani babban tashin hankali da Hajiya Samira matar Alhaji Kabiru Tanimu take ciki shi ne na rashin samun sukuni tare da mijinta wajen debe mata kewa, da kuma samun sukunin aure tsakaninsu, ko shakka babu wannan al’amari yana matukar damun Samira, domin zata ci dukkan irin nau’I na kayan dad’i  da abinsha dole ne kuma idan wadannan abubuwa suka samu ta bukaci wanda zai dauke mata bukatuwa irin na ma’aurata. Wannan ta sanya Hajiya Samira ta kasa jurewa rashin Alhaji a lokacin da ta bukace shi, inda ta fara kokarin shawo kan Hamza Muhammad daya daga cikin manyan yaran Alhaji. Hakika Alhaji ya aminta da Hamza kamar dansa na cikinsa, domin Hamza yasan sirrikan Alhaji sosai wani zubinma ita kanta Hajiya Samira a wajensa take samun labarin wasu al’amuran na mijin nata, domin babu daya daga cikin kasashen da Alhaji  yake zuwa face sun je da Hamza.

Hajiya Samira ta ringa nunawa Hamza irin bukatunta a gareshi, tun baya ganewa har yazo ya fara fahimtar halin da ake ciki. Daga lokacin da Hamza ya fahimci halin da Hajiya ta shiga na tsananin bukatarsa, hankalinsa ya yi matukar tashi, domin babban abinda yake tunani shi ne dangantakarsu da Alhaji Kabiru Tanimu, tayaya mutumin da ya daukeshi tamkar d’an da ya Haifa, amma ya ci Amanarsa. Ana cikin tsaka da wannan mawuyacin hali da Samira da Hamza suka shiga ne sai shi Hamza ya lura da wasu kawayen Hajiya Samira da suke yawan zuwa gidanta a kullum musamman da daddare cikin mummunar shiga, ganin wadannan mata hankalinsa ya kara tashi, domin bai gamsu da yawan zuwa da suke wajen Samira ba, da ya matsa bincike akansu aka tabbatar masa da cewar wadannan mata mafiya yawancinsu ‘yan Neman mata ne!

Jin wannan labari ya sa Hamza ya fashe da kuka hankalinsa yayi matukar tashi, domin kuwa yasan rayuwar Hajiya zata shiga wani irin mummunan gararin da Allah ne kadai ya san irinsa. Hamza yana tunanin ga Samira na kawo masa hari, yana kaucewa tare da mayar da kansa bagidaje duk dan ya nuna mata shi bai fahimci abinda take nufi ba, sannan kuma a gefe guda ga wasu kartin mata suna kawowa Hajiya Samira hari babu dare babu rana! Wannan abin ya dugunzuma Hamza ainun. Bincikensa ya nuna masa cewa ita Hajiya bata san manufar wadannan kawayen da suke zuwa wajenta ba.

Daga nan shima Hamza ya shiga wata tsaka mai wuya ta gaba kura baya siyaki, domin yana tunanin shin ya yi watsi da bukatun Hajiya ya kyaleta ta fada hannun wadancan batagarin mata, ko kuwa ya kare ta daga fadawa waccan halaka, ta hanyar cin amanar mai-gidansa Alhaji Kabiru Tanimu! Wannan al’amari ya tayar da hankalin Hamza matuqa, babban abinda yake damunsa shine Alhaji mutum ne da babu wanda zai zargeshi da cewa d’an duniya ne, a bisa abin da ya bayyana na zahiri dangane da rayuwar Alhaji Kabiru Tanimu mutumin kirki ne, ana kyautata masa zato, amma kuma ga irin halin da ya jefa iyalinsa a ciki.

Hamza yace ina matkar jin tausayin Alhaji Kabiru Tanimu, domin shakka babu Allah ya yi masa arziki mai tarin yawa, amma ni Hamza banga alamun cewa Alhaji yana jin dadin dukiyarsa ba, a cewar Hamza, domin suturar da yake sanyawa ba wata mai tsada bace, haka duk da irin jibga-jibgan motocin da suke cikin gidajensa a Ahmadu Bello Way, da GRA Tarauni da NNDC Quarters da Tal’udu a Kano amma sai ka samu motar da Alhaji ke hawa daga Akori-kura Hillux, sai wata karamar Tayota Karina, idan kaga Alhaji ya hau daya daga cikin manyan Marsandinsa to ko dai zaije daurin aure ne, ko kuma zaije Abuja ko Kaduna, sannan gashi duk sadda yake gida abincinsa daga Tuwan Gero miyar kuka sai kunun tsamiya, shine cin dafaffiyar gyada da gujjiya da zogale da rama, wadannan da wasu abubuwa da nake gani ya sa nake tunanin anya Alhaji yana jin dadin wannan dukiya tasa kuwa? Hamza yana tattauna irin wadannan abubuwa a cikin ransa.

Wani Karin abin mamaki dangane da Alhaji, idan yana Najeriya jama’a basa barinsa ya sake kullum mutane ne ke zuwa wajensa shi kuma baya korafi, kuma baya korar mutane, indai ka samu ganin Alhaji tabbaci hakika ba zaka fito daga falonsa hannu rabbana ba; mutanan da Alhaji ke daukar dawainiyar ratyuwarsu suna da yawan gaske, yara da mata da matasa da dalibai masu karatu a jami’a, bugu da kari Alhaji mutum ne mai tsananin son yara kanana, domin a yanzu haka a cikin gidan Alhaji ba zaka rasa kekunan yara sama da guda hamsin ba wadan da yake saya kawai dan rabawa yara kanana, da sauran kayayyakin wasanni na yara; Faisal dan Alhaji kuwa duk sadda Alhaji ke gari to tare zaka gansu duk inda Alhaji zai je tare suke tafiya.

Ire-iren wannan rayuwa ta Alhaji Kabiru Tanimu ya sanya Hamza ke tausaya masa, sannan kuma yake ganin tayaya zaici Amanar wannan bawan Allah, a gefe guda kuma itama Hajiya Samira ta shiga cikin wani irin mawuyacin Hali, nan Hamza yake ta neman Mafita shin ya bayar da kai bori ya hau a wajen Hajiya dan kare ta daga wadancan fandararrun mata masu kawo mata farmaki, ko kuwa ya kyaleta komai ta fanjama fanjam, wannan tunanin ya sanya Hamza zubar da hawaye.

Yasir Ramadan Gwale
03-08-2013

Thursday, August 1, 2013

ME YA HANA 'YAN SHI'AR NAJERIYA ZUWA QUDUS NE HAR YANZU?


ME YA HANA 'YAN SHI'AR NAJERIYA ZUWA QUDUS NE HAR YANZU?

Duk shekara ya zama addini a wajen 'yan SHI'AH su fito kan tituna da tutoci da kwalaye rike suna rera wakokin nuna cewa Masallacin Qudus nasu ne, kuma sai sun je har Qudus din sun kwato kayansu daga mamayar da Yahudawan Israela suka yi masa. Shekaru masu yawa El-Zakzaky yake ta wahalar da matasa da mata da yara cewa wai zasu je su kwato masallacinsu, tun daga lokacin da suka fara wannan harmagazar har yau basu taba tsallaka kan iyaka ba dan zuwa Aqsa ba. Amma watakila ina zaton ko basu san hanya bane. Bari na yi musu kwatance tunda sun shahara da yin tattaki a kasa, hanyoyi ne guda biyu daga Najeriya zuwa Masallacin Qudus ko Aqsa, ko dai su bi ta Nijar, su keta saharar dake Agadez su shiga ta Arlit a Algeria su bi ta Tamariset su keta hamadar Algeriya sannan su isa har Libya daga nan su dangana zuwa birnin Benghazy dake da iyaka da kasar Masar daga nan sai su shiga mashigar nan da ake kira RAFAH sai Qudus; idan wannan hanyar ta yi musu tsawo su bi ta Iyakar Najeriya da Chadi, su keta kasar gaba daya su shiga ta El-fashir a Sudan daga nan su dangana Nehud kan iyakar Sudan da Masar, suna shiga Masar sai mashigar RAFAH, daga Najeriya duk wanda zaiyi tattaki zuwa Qudus wadannan su ne hanyoyinsa. Idan basu san hanya ba ga shi nan mun yi musu kwatance, Idan suka fita a gobe kafin bad'i war haka tuni sun Isa Qudus, kaga daga nan sai su fara gwagwarmayar dawo da Massalacin Qudus.

Yahudawa na can na kashe Musulmi a Palastine babu dare babu rana, amma Jahilan suna Gyallesu suna cewa zasu kwato masallacin Qudus. Me ya hana IRAN kai sojojinta QUDUS don taimakon Palasdinawa da kuma kwato Qudus kamar yadda suka tura sojojin su kasar Syriya suna kashe Musulmi da basu san hawa ba, basu san sauka ba, suna rurrusa masallatai tun wadan da Sahabbai suka gina, amma saboda rashin kunya, makirai sai su ce ai IRAN ke baiwa 'yan HAMAS makaman da suke yakin ISRAELA, mu duk wannan babarodon ba zamu gane ba, muna son kamar yadda aka tura sojan IRAN yankunan QUSAYR a SYRIA muna jiran muga sojan IRAN a yankunan GHAZZA da WEST BANK da sauran yankunan Palasdinawa da Israela ta mamaye.

Kuma daman su 'yan SHI'AH sun shara da 'batar da sawun tarihi, domin kuwa shi kansa wannan hoton da suke yawo da shi mai kubba ruwan zuma ai ba shine Majid Aqsa ba, Massalacin Quds na ainihi yana da Bakar Kubbah ne ba wannan bane mai ruwan zuma da shi'ah ke yawo da shi suna san jirkita tarihi su rudi jahilai wadan da basu fahimci yadda lamarin yake ba.

Mu MUSULMI mun san da cewa Masallacin AQSA daya ne daga cikin Manyan masallatan MUSULUNCI guda uku da Manzon Allah ya ce su kadai ne za a iya nikar gari domin tafiya ziyara, kuma mun kyautata zato ga ALLAH cewa wannan Masallaci ko ba da'de ko bajima sai wannan Masallaci ya koma mallakar Musulmi amma ba 'yan SHI'AR da ake sarrafawa daga TEL AVIV da NEW YORK ba, 'yan shi'ar da suke yiwa su NETANYAHU aiki wajen kashe dubban al'ummar Musulmi babu gaira babu dalili.

Yasir Ramadan Gwale
01-08-2013