SHUGABA
JONATHAN KO TANTAL BATAITE
Tunda aka samar da wannan kasar mai suna
Najeriya a kusan shekaru dari (100) da suka gabata ba'a taba samun kidahumin
shugaba mara mutunci kamar shugaba Jonathan ba. Hakika, wannan shugaban ya nuna
rashin iyawa da kasawarsa karara ta cewa ba zai iya jagoranci wannan kasa bisa
gaskiya da Adalci ba. Shugaban kasar da yayiwa kansa dabaibayi da cin-hanci da
rashawa da kuma muguwar satar da ta zarce hankali. Shugaban wanda kullum yake ta
kokarin ya nunawa duniya cewa gwamnatinsa tana iyakar yinta wajen sauke nauyin
da al'ummar Najeriya me mabambantan kabilu suka dora masa, wanda a hakikanin
gaskiya, dukkanninmu 'yan Najeriya muna san shi (shugaban kasa) katafaren
makaryaci ne mara kan-gado, mugun mutum ne mara tsoron Allah.
A dukkan lokacin da Shugaban zai tattauna
da 'yan jaridu musamman na ketare yana ta kokarin ya nuna musu cewa yana yin
iyakar kokarinsa illa kawai abin nanne da ake cewa, idan dambu yayi yawa baya
jin mai! Wanda a kashin gaskiya su 'yan Najeriya sun san da cewa wannan
hasararriyar gwamnatin bata yin komai wajen sauke wannan nauyi na jagorancin da
yake kanta, face wadaka da warisa da dukiyar kasa. Dukkan wasu surutai da
shugaban kasa yake yi, mun san cewa karya ce tsagwaronta kawai yake shararata a
duk lokacin da sanyin dakin watsa labarai ya doke shi.
Da gangan shugaban da gwamnatinsa suka ki
samar da cikakken tsaro a yankin Arewacin Najeriya ba wai dan abin ya gagaresu
bane. Yau idan gwamnati ta so duk wasu masu tayar da kayar baya da hannu za'a
kamasu ba tare da amfani da muggan makamai ba. Amma da yakke akwai wata
boyayyar manufa wadda ba ta alheri bace da suke son cimmawa, kullum suna nuna
cewa abin yana neman ya gagari kundila (sha'anin tsaro). Kullum suna kira cewa
wai talakawa su taimaka da bayanan da zasu kai ga bin sawun masu aikata laifuka
dan samo bakin zaren, bayan sun manta cewa shi talakan da suke neman agajinsa
shine suke kashewa baiji ba, kuma bai gani ba. Kuma ma idan banda tsabar rainin
wayo da wulakanci, ina amfanin dukkan irin kudaden da ake warewa dan sha'anin
tsaro suke tafiya? Saboda an mayar da mu kamar gidadawa bamu san abinda muke
ba, suna can suna watanda da dukiyar kasa, sannan su dinga bulayin iska bayan
sun kwankwadi barasa wai a taimaka musu da bayanai. Kaji Iskanci! Shugaban da
kusan a kullum sai kara zama wata kwarkwantacciyar 'kura' yake yi ga mutanan
Arewacin kasarnan ta hanyar karya tare da lalata yankin. Daman gari banza ya
aka iya da 'kura' balle ta kwarkwance, kaga kuwa lallai sai wanda Allah ya
tsallakar.
Shugaban kasa ya kidime inda yake ta
bagauniya, kamar wanda ya sha giyar Agogoro, hankalinsa ya tashi, kullum
tunaninsa ya za'ayi ya tsawaita wa'adin mulkinsa bayan 2015. Tabbas, shugaban
kasa da masu bashi shawara da makusantansa musamman irinsu Tony Aneni da Doyin
Akupe da irinsu Ahmed Gulak da su Aku-kuturu (Labaran Maku) da sauransu, duk
suna yi masa ingiza wawa-kwari ne, ta inda zasu kaishi su baro, koma sun riga
sun kaishi sun baro; domin su din bukatar kansu ce kawai a gabansu, ba wai
al'ummar kasarnan ba. Shugaban ya zama rakumi da akala, suna dorashi akan
mummunar turba wadda babu inda zata saukeshi sai dandalin Nadama da kuma
da-nasani a lokacin da bazata amfaneshi ba, domin kuwa, duk cikinsu babu wanda
zai yarda ya tayashi zama a kiri-kiri ko Kurmawa bayan zaben 2015. Kowannensu
ta kansa zaiyi ya kyaleshi, tunda shine Direba sitiyari yana hannunsa lokacin
da motar ta fara neman kakarewa duk fasinjojin ciki arcewa zasu yi su bar
direban da jangwam, alhali shi Direban ko gidan mai be sani ba a jikin motar,
haka nan za'a cimmasa, mugun Arne!
Haka kuma, a rahotannin da muke ji, daga
bakin Aku-kuturu cewa, bazasu lamunci aibanta shugaban kasa da 'yan Najeriya
suke yi ba a kafafen sadarwa na Internet, har wata majiya ta ce shugaban ya
bayar da kwangilar kusan dalar Amurka Miliyan 40 dan a dinga leka masa
akwatunan Email da Status Update na facebook da Twitting din 'yan Najeriya, dan
a tunaninsu zasu fara daukar mataki. Lallai kuwa shugaban kasa ya dauko dala
babu gammo. Amma ni shawarar da zan baiwa su Aku-kuturu shine su fara da kara
yawan dakuna a gidajen yarin kasarnan, domin saboda bacin rana.
Shukka babu, mu mutanan da wannan
shugaban ya zalunta, ya karkashe mana al'ummarmu babu gaira babu dalili, ya
karya mana tattalin arziki dan-mugunta da keta da tsabar bakin ciki. Insha
Allah, zamu yi dukkan mai yuwuwa wajen ganin munkai keyar wannan shugaban kasa
a 2015. Zamuyi addu'ah domin itace matakin farko, kuma malamai sun gaya mana
cewa ita addu'ah takwabin mumini ce; sannan kuma, zamu yi amfani da dukkan wasu
hanyoyi da suka halatta a garemu wajen ganin mun cimma nufinmu, na kakkabe
wannan shugaban ko yaso ko yaki Bi'iznillahi.
Daman mu da muka yi Imani, Allah
ya gaya mana yana taimakon wadan da aka zalunta idan sun yi hakuri kuma sun
tashi da gaske. Hakika munyi hakuri, kuma zamu tashi mu zage dantse a matsayin
wadan da wannan mutumin da 'yan tawagarsa suka zalunta dan-ganin mun taka musu
burki ko da tsiya ko da arziki, kuma Insha Allah muna kyautata zato cewa a
wannan karon Allah zai taimekmu.
Yasir Ramadan Gwale
27-04-2013
Ya allah yaimana canji na alkairi
ReplyDelete