Saturday, April 27, 2013

A KAI-KAICE SHUGABA JONATHAN YANA AIWATAR DA MUGUWAR MANUFAR OBASANJO TA RAGE YAWAN MUSULMI A AREWA!!!




A KAI-KAICE SHUGABA JONATHAN YANA AIWATAR DA MUGUWAR MANUFAR OBASANJO TA RAGE YAWAN MUSULMI A AREWA!!!
Duk da irin tsanani da mawuyacin hali da Musulmi muke ciki a Arewa ko Najeriya, baza mu taba mancewa da muguwar manufar Obasanjo ba. Shakka babu gwamnatin tsohon shugaba Olushegun Obasanjo mu mutanan Arewa ba zamu taba mancewa da ita a tarihi ba, bisa irin yadda ta gallaza mana ta saka al'ummar Arewa Musulmi cikin wani irin mawuyaci kuma matsanancin hali. Halin k'a'ka nika yi, da ni 'yasu, banda fatara da mugun talaucin da aka kakaba mana ta karfi da yaji, aka kashe mana dubban mutane a Shagamu da sauran sassan kudancin kasararnan ba, aka kashe mana masana'antu ta karfi da yaji dan a gurgunta tattalin arzikinmu a nakastamu ta yadda za'a kwantar da tattalin arzikinmu kasa ya kasa motsi, aka talauta manyan 'yan kasuwarmu, masu shigo da kaya daga waje da kuma masu sana'anta kayansu anan cikin gida ta hanyar kashe masana'antun da rashin samar musu da wutar lantarki da sauran abubuwan bukata nay au da kullum.

Obasanjo a wancan lokacin, yayi amfani da hukumar kwastam, domin nakasta kasuwancinmu. Bahaushe zai shigo da kaya na dubban miliyoyi kasarnan zuwa Arewa tundaga saukarsu akan ruwa, ya biya kudin futo da dukkan haraji da ake biyawa haja, sai ya kawo kayansa ya kasa a kasuwa a Kano ko a Kaduna, sannan jami'an kwastam zasu biyoshi har kantinsa su kwashe masa kaya su kone su kurmus, da sunan kayan da gwamnati ta hana shigo da su! Duk wannan yana nan rubuce cikin kundin tarihinmu, bazamu taba mancewa da shi ba. Allah ne kadai yasan irin adadin mutanan da aka talauta ta wannan hanyar a Arewa; daman ba'a maganar kankanan masana'antumu da kuma manyan da suke a tsakanin Kano da Kaduna wadannan duk sun zama tarihi sai dai tsaffin gine-gine da suka zama sansanin batagari da sauran kwari da suke washshagare walle a cikin wadannan gine-gine.

Sannan kuma, a lokacin gwamnatin Obasanjo da ta gabata aka kone mana manya manyan kasuwannin da suke Arewa Misali kasuwar Galadima Road da take Kano, da kasuwar 'yan magani da take a Kaduna da babbar kasuwar dake birnin Jos wadda kaso 90 ciki 100 Musulmi ne suke juya dubban miliyoyin Nairori a ciki, duk wadannan manyan manyan kasuwanni ne da kudi suke kewayawa a ciki a kullum ranar Allah, wadda ankonesu tun zamanin tsohuwar gwamnatin Obasanjo, Yanzu Alhamdulillah wasu sun tashi wasu kuwa har yanzu suna nan a kwance. Banda mutananmu da aka dinga dorasu a jirgin sama ana rikito da jirgin mutanan su mutu, duk wannan muna sane.

Yanzu idan ka dauki babbar kasuwar Jos, Allah ne kadai yasan adadin miliyoyin da aka yi hasara a wannan kasuwa, 'yan kasuwar da aka karya aka durkusar dasu, Allah ne kadai yasan adadinsu, bayan an durkusar da kasuwancinsu aka dinga binsu har gida ana kashewa, Obasanjo ya kasha, sannan Dariye da magoya bayansa suma su kasha, sannan a kashe matansu bayan anyi musu fyade ana ribace 'ya 'yansu kanana ana mayar dasu bayi a kasarsu ta haihuwa.

Idan bamu manta ba, tun bayan da Obasanjo ya zo a matsayin shugaban kasa na goma sha uku (13) ya fito da kiyayyarsa a fili balo-balo ga Musulmin Arewacin kasar nan. Tun bayan zuwansa ne, ya fara aiwatar da mummunan nufinsa na rage adadin musulmi da suke cikin soja da 'yan sanda, ta hanyar kashe wasu daga cikinsu a jirgin sama, ko kuwa a yi musu ritayar karfi da yaji, sannan dukkan wani babban soja ko dansanda da aka sauke ana maye gurbinsa ne da kirista ko na Arewa ko na Kudu, sannan a wasu jihohi da suke da kiristoci kamar Bauchi da Gombe da Borno da Adamawa da Taraba da Kaduna ake raba daidai tsakanin Musulmi da kirista wajen daukan sabbin sojoji da 'yansanda, wannan abun ko shakka babu haka gwamnatin Obasanjo ta aiwatar tun a wancan lokacin! Kai hatta jihohin da suke da Musulmi 99.9 sai da aka dauki Kiristoti a aikin soja da dansanda irin Zamfara da Jigawa.

Ma'aikatan gwamnatin tarayya kuwa kusan sai da (arna kiristoci) suka kusan mamaye dukkan ma'aikatan gwamnatin tarayya. Kaje Babbar sakatariyar gwamnatin tarayya dake Abuja kai zaka dauka a Idiyaraba kake ko a Onica arnan sun mamaye ta gabaki daya, kwata-kwata ba'abi tsarin daukar ma'aikata da ake kira "quota system" ba. Anyi masa fyade a nan wajen. Idan ka shiga wata ma'aikatar a Abuja sai kaga Hausawa 'yan Arewa Musulmi basu fi cikin 'yan yatsunka ba, kuma wai sunan Babban birnin tarayya yana yankin Arewa inda Mulsulmi suke da rinjaye kenan, dukkan wadan da suka isa suyi Magana suna kallo babu wanda yace uffan! Wadan da suka iya rashin kunya daga cikin shugabbani marasa kishi sune zasu ce wai mu 'yan Arewa ne bamu da 'Qualification' kamar yadda aka ruwaito kakakin rundunar sojojin Najeriya yana fada.

Haka kuma, muguwar gwamnatin ta Obasanjo ta kirkiri wani shiri wanda shine kashin bayan mayar da Musulmin kasarnan saniyar ware, ta kira wani abu waishi Babban taron makomar kasa ko 'Supreme National Conference' wanda aka yi mana rainin wayo iyakar rainin wayo, amma daga cikin 'yan bokonmu da wadan da suke kiran kansu sune manya da yaku bayin da masu rike da mukaman babu wanda ya iya kalubalantar abin. Domin a cikin mutum 382 da aka ce zasu halarci wannan taro mutum 150 ne kacal Musulmi sauran 217 gabaki dayansu kiristocine, kuma masu ilimin gaske, wadan da suka san kan-tsiya da makirci. Mu kuma a namu bangaren siyasa ta damamala abin inda gwamnoni suka yi ta bada sunayan wasu rafkanannun mutanen da sun gaji suna bukatar hutu wai sune zasu wakilcemu a wajen wannan taro. Allah ya isa!

Sannan aka zo aka shirya WAI kidayar jama'a 'census' inda akayi mana wakaci ka tashi, aka kwashe mana kafafu. A wannan kidaya akace za'a kirga yawan gidaje da mutane, aka kaskantar da wasu jihohin irinsu kano da Kaduna da Katsina da Sokoto da Borno aka rage musu yawan jama'a. Sannan daga bangaren kudu aka daukaka darajar wasu jihohin ta fuskar yawan jama'a irinsu Bayelsa da Delta da Ekiti da Akwa Ibom da sauransu, wadan da a zahiri basu kai yawan mutanan cikin irnin kano ba. Duk fa, wadannan Obasanjo yayi wannan ne damin share fagen kakkabe Musulmi daga rike wasu dukkan manya manyan mukamai na gwamnati irin yadda Shugaba "Poul Biya" na kamaru yayi na zare hannun Musulmi daga cikin dukkan wasu al'amura na hukuma. Wannan shine irin abinda Obsanjo yaso aiwatarwa Allah ya watsa aniyarsa. Shakka babu wadannan kadan ne daga cikin irin mugayan manufofin Gwamnatin Obasanjo akan Musulmin kasaranan, musamman na Arewa.

Kamar yadda dukkanmu muka sani, Obasanjo shine kashin bayan wannan shugaba na yanzu Goodluck Jonathan wanda shine shugaba na goma shabiyar (15). Kafin wannan shugaban da yawan 'yan Arewa sun san da cewa bayan da Allah ya kashe tazarcen Obasanjo! Domin babu wasu 'yan Arewa da zasu yi mana burga cewa sune suka kashe tazarcen Obasanjo, wallahi mun sani Allah ne ya hana Obasanjo tazarce, domin acikin duk masu cewa su suka kashe tazarce babu wanda yake yiwa Obasanjo baranza, ya riga yaga wallensu, yasan 'yan iska ne mazinata 'yan luwadi mashaya giya! Idan banda 'yan kadan da sukayi dan Allah, dan al'ummar kasa. Dan haka kar yake kallonsu shi(Obasanjo).

Dan haka ne shi Obasanjon ya dauko Marigayi Malam Umaru Musa YarAdua a matsayin wanda zai gajeshi. Da yawan 'yan Arewa sun sani cewar Obasanjon ya dauko Umaru ba da kyakykyawar niyya ba ne, Allah masani! Amma dai yanzu mai aukuwa ta auku, ko da niyya ko babu niyya ya zuwa yanzu Obasanjo ya ci nasarar aiwatar da mummunan nufinsa ta wata kaikaitacciyar hanya. Duk kuwa da ana ta ruwaitowa a Jaridu cewa akwai tsamin dangantaka ko alaka tsakanin tsohon shugaba Obasanjo da wannan shugaba maici, mun san cewa duk wannan wasan kwaikwayo ne ake yi da hankulan wasu daga cikinmu, Obasanjo yana kawar da hankulan mutane daga kan irin muguwar barnar da ya aikata, ta hanyar nuna mana shi yana kalubalantar wannan gwamnati, amma kuma a cikin sirri sai a ruwaitoshi yaje ya gana da wannan shugaban sun tattauna a kebe ba tare da bayyanawa 'yan jarida abubuwan da suka tattauna ba.

Shakka babu, wannan shugaban, Goodluck Jonathan, shine wanda yake biyewa Obasanjo wajen tabarbarewa da lalacewa. Haka kuma, muna da masaniyar cewar dukkan abinda yake yi muguwar manufar Obasanjo ce da bai samu dama ba, yake aiwatarwa a halin yanzu, inda yake ta kakkabe hannun musulmi daga manya manyan madafun iko da lalata tattalin arzikin Arewa da tabarbara harkar ilimi da dangoginta; daman kuwa tsaro yanzu ba'a Magana, Allah ne kawai yake kare rayukan bayinsa muminai, domin anci nasarar kakaba mana wasu kungiyoyi da sunan Musulmi ko Musulunci da bayar da mummunan hotanmu a duniya da nuna cewa mu din ba masu san zaman lafiya bane. 

Sannan kuma, akayi amfani da dakarun tsaron da mafiya yawancinsu kiristane suke dinga kahsemu babu ji babu gani da sunan farautar masu aikata laifi. A duk duniya babu wata doka da tace a kashe mai laifi, shi mutumin da ya aikata laifi, duk abinda yayi zargi ne har sai ankaishi kotu ta tabbatar masa da laifinsa sannan ya zama mai laifi, a bisa tsarin doka cewa aka yi idan har ta kama za'a harbi mai laifi to a harbeshi d harsashin ROBA ba kashe shi za'a yi ba,  Idan kuma har ta kama za'a yi amfani da harsashi mai RAI to za a harbeshi ne a kafafuwansa, amma mu kam babu ko daya da ake aiwatarwa, soja arne mashayin giya zai harbi Musulmi a kai ko a kirji ya kashe Musulmi bisa hujjar mai laifine, kuma ya kashe banza a wajensu, dan babu wani abin da za'a yi. Yawanmu ya zama na tsintsiya babu shara, masu iliminmu da dattabanmu basu iya amfanar da mu da komai ba, illa kara jefa mu cikin kaskanci da wahala da wulakanci.

Yana daga cikin mugun gadon da Obasanjo ya barwa wannan shuguban haddasa manya manyan rigingimu guda biyar (5) a Arewa, wadan da idan aka ci nasarar aiwatar dasu to shugaban zai samu damar cigaba da mulkinsa har illa masha Allah. A'azanallah! Idan bamu manta ba shugaban sojojin Najeriya Burgediya Ihejirika yayi wata ritaya ta babu gaira babu dalili ga manya manyan sojoji musulmi inda aka maye gurbinsu gabaki daya da kiristoci 'yan kudu, kuma duk surutunmu ya tashi a maho, dan bai hanasu aiwatar da nufinsu ba. Daga cikin rikice-rikicen da aka barwa wannan shugaban dan yayi dukkan maiyuyuwa wajen ganin ya ruruatsu sune:

1- Abu na farko, shine kokarin haddasa fada ko rikici tsakanin Musulmi da Kirsta a Arewa. Wanda wannan abu ne sananne kuma bayyananne cewa anci nasarar haddasa wannan fadan, da kuma sanya muguwar gaba tsakanin Musulmi da kirista a Arewa. Kusan kullum kiristoci takalar musulmi suke yi da fitina a kasarnan, eh! Tabbas takalar fada suke yi, ina nufin kiristan Arewa, wannan abu ne da baya bukatar buga wani misali domin duk wanda ya kwana ya tashi a Arewa yasan da haka.

2- Abu na biyu, shine haddasa fada ko rikici tsakanin 'yan Arewa da mutanan kudu maso gabas (yankin Inyamurai)  Shakka babu suna nan suna yin aiki dare da rana wajen ganin an hadamu fada. Domin duk mutanan kudancin kasarnan babu wadan da suka kai Inyamurai sakewa a Arewa suyi kasuwanci babu tsangwama. Wannan ce ta sanya a kwanakin baya suka kai harin Bom a tashar Mota a sabon garin kano inda galibin Inyamurai ne ke safarar fasinja daga kudu zuwa Arewacin kasarnan, anyi wannan mummunan aiki da gayya ne da nufin hadamu fada dasu, saboda alakar dake tsakaninmu ta kasuwanci ta wargaje.

3- Abu na uku, shine kokarin assasa wata muguwar kiyayya da gaba tsakanin mutanan Arewa da mutanan yankin kudu maso kudu. Wanda tarihin siyasar kasarnan ya nuna cewa akwai kyakykyawar dangantakar siyasa da mutanan kuryar kudancin kasarnan da 'yan Arewa. Haka ta sa a kullum ake ruwaito 'tsagerun yankin suna takalar mutanan Arewa da fitina da tashin hankali da munanan kalamai, masu barazana ga tsaro, amma babu ko mutum guda da aka taba kamawa da sunan tuhuma dan tayar da tarzoma. Edwin Clack da tsagerun kungiyar MEND wadanne irin barazana ce basa yi a kullum? Wadanne irin kalaman takala ne basa yi a kullum? Idan banda lalacewa ta 'yan Arewa 'yan iska 'yan daba da ko suturar kirki basuda, 'yan fatsa masu kamun kifi, wai sune suke takalarmu da fitina da tashin hankali, mu kuma kullum muna ta kokarin kare kanmu da nuna cewa ba haka abin yake ba. Allah ya sawwake.

4- Abu na hudu, shine kokarin assasa muguwar fitina tsakanin Talakawa 'yan Arewa da shugabannin Arewa. Tabbas, akwai shirin da suke yi na ganin an hada talakawa fada da shugabanninsu, misali, kullum ana ruwaito jaridun kudancin kasarnan suna cewa 'yan Arewa ne suka mallaki kaso 80 ko wani abu makamancin haka na rijiyoyin manfetur a yankin kudancin kasarnan! Kamar hannunka mai sanda ake yi mana mu farmusu. Da kuma nuna cewa 'Yan Arewa sune suke da Mataimakin Shugaban kasa, da Shugaban majalisar Dattawa, da Kakakin Majalisar wakilai da sauran manyan masu rike da mukamai barkatai, dan hadamu fada dasu! Amma kuma sun mance da cewa dukkan wadannan mutanan da ake fada gabaki daya shugaban kasa shi kadai ya rinjayesu, basu isa su hana komai aiwatuwa ba. Sai dai abinda shugaban baiyi Nufi ba. Bil Hasalima majalisar kasarnan ta gayyaci shugaban kasa yaje yayi mata bayanin akan halin da ake ciki na tsaro a daidai lokacin ya sa kafa ya fice yabar kasarnan, har yau kuma bai amsa wannan gayyatar ba, kuma babu wani abu da ya biyo baya.

5- Abu na biyar kuma na karshe, shine aiwatar da kisan kare dangi akan talakawan Arewa musulmi ne ko kirista. Wanda wannan shima yana daya daga cikin abin da aka fara aiwatarwa a garin BAGA na jihar Borno a 'yan kwanakin da suka gabata. Banda mutanan da ake kashewa a kullum ta Allah a jihar Plateau. Haka kuma, su Arnan kudu su Obasanjo da tawagarsu ta su wannan munafukin shugaban Jonathan hatta kiristocin Arewa ba burgesu suke yi ba, suna tare da sune kawai a lokacin da Kiristan Arewa yake kashe Musulmin Arewa, amma banda wannan wallahi basa kaunar wani kiristan Arewa, a wajensu duk Hausawa ne 'yan Arewa.

A ganina wadannan kudurori guda biyar sune mummunan kayan gadon da Obasanjo ya barwa wannan munafikin shugaban, shi kuma yake aiwatarwa. Kuma ana amfani da rubabbun cikinmu wajen dannemu da nuna cewa mu Musulmi mune bamu da gaskiya bama son zaman lafiya, ga mari kuma ga tsinka jaka! Wato a dokemu a hanamu kuka. Lallai Ina kira garemu mu Musulmi 'yan Arewa mu tashi tsaye mu fahimci irin muggan kulle-kullen da aka yi mana danganin mun warwaresu mun fitar da kanmu daga cikin halin kangi da bauta da fatara da wahala da tsoro da firgicin da muke ciki.

Idan har wannan shugaban yaci nasarar aiwatar da wadancan munanan kudurori guda biyar, to ya samu damar cigaba da mulkin kasarar nan a bagas ko 'yan Arewa sun so ko basu so ba. Kamar yadda yanzu bayanai suke nunawa cewa a karon farko 'yan Arewa zasu dunkule dan su yaki wannan gwamnati maici kuma su hana mata wucewa ko ta halin kaka! Idan shugaban yaga babu mafita to idan ba Allah ne ya kiyaye ba, zai yi ta haddasa rikice-rikice ne a nan Arewa babu kakkautawa daga karshe shugaban kasa yace ya kafa dokar ta-baci a Najeriya gabaki daya, ya rushe majalisar kasa ya rushe gwamnonin Jihohi da shugabannin kananan hukumomi, ya kakkafa wadan da yake so, har tsawon wata shida kamar yadda doka ta tanada, shi kuma yayi amfani da karfin ikonsa ya hana kasar zama lafiya dan cigaba da bakin mulkinsa na zalunci da danniya da shan-jinin al'umma. Allah ya kiyaye! Ko mu yarda ko kar mu yarda wannan itace mummunar niyyarsu akan Musulmin wannan kasar. Ya rage namu kodai mu tashi haikan wajen yakar wannan al'amari da dukkan karfinmu da kuma dagewa da addu'o'I a masallatai da cikin sallolin farilla da na nafila ko kuma mu ci gaba da zama cikin kaskanci da wahala har tamu ta zo ta same mu.

Har yanzu, duk da mun san da cewa wadannan shugabanni namu na Arewa sune suka kaimu suka baro, su sani, suna da kima a idanunmu suna da sauran burbushin mutunci a idanunmu mu talakawa. Dan haka suji tsoron Allah su yi mana kyakykyawan jagoranci, mun yarda cewa babu wata al'umma da zata ci gaba ba tare da jagoranci ba. Dan haka wajibinsu ne su tsaya tsayin daka wajen kare mana martabarmu da martabar Addininmu da al'ummominmu. Idan kuma ba haka ba, wallahi duk wata guguwa da zata taso a nan gaba su zata fara yin awon gaba dasu. Dan kuwa sune zasu yi asara! Allah ya kiyaye.

Dan haka a matsayinsu na shugabanni kuma jagorori wajibine su kula da bukatun wannan al'umma tamu wajen ganin ansamar mana da cikakke kuma ingantaccen tsaro na rayuka da dukiyoyinmu. Kuma, lallai ne, wajibinsu ne, su matsawa wannan gwamnati idan har da gaske suke cewa yanzu ruhin kishin al'ummar Arewa ya dawo jikinsu wajen samar mana da abubuwa guda bakwa(7) wadannan abubuwan sune:

1-   Samar mana da ingantaccen Ilimi ga dukkan al'ummarmu. Ilimi tundaga matakin firamare har zuwa karama da babbar sakandare da kuma jami'ah, ya kasance kyauta ga dukkan al'ummarmu kuma wajibi ga kowanne Yaro.

2-   Samar mana da cikakken tsaro na rayuka da dukiyoyinmu da dukkan guraran sana'o'inmu, da matattarar mutane da makarantu da gidajenmu da guraran Ibadarmu da guraran tarurrukanmu, ba tare da tsanantawa ko muzgunawa mutane ba.

3-   Samar mana da tsaftatacce kuma ingantaccen ruwan sha, ga dukkan al'ummarmu birni da kauye, da kuma samar mana da ruwan da zamu yi noman rani dashi da wadataccen taki da kuma samar mana da ruwan da dabbobinmu zasu sha.

4-   Samar mana da kyawawan hanyoyin zurga zurga na motoci da na mutane, tundaga Jaba har zuwa kwangwalam da dukkan sauran yankunanmu. Hanyoyi Masu inganci da karko a dukkan biranenmu da kauyukanmu.

5-   Samar mana da tsayayyar wutar lantarki wadda bata yankewa. Wutar lantarki mai karfi ba manja ba, wadda zata dauki dukkan wani nau'I na kayan latironi.

6-   Samar mana da ingantaccen tsarin kiwon lafiya. Tsarin da zai inganta asibitocinmu da muke da su, tare da samar mana sababbi da suka kunshi dukkan wasu na'urori na zamani da manyan injina. Sannan kuma da samar mana ingatatttun dakunan shan magani, da kankanan dakunan shan magani a kauyuka.

7-   Samar mana da ingantaccen tsarin habakar tattalin arzikin kasa. Tsarin da zai kula da harkokin noma da kiwo a dukkan yankunanmu, tare da tayar da komadar dukkan masana'antunmu da suka durkushe wanda zai baiwa jama'armu damar samaun aikin yi bayan sun kamala karatu.
Wadannan sune abubuwan da muke son ganin sun yi tsayin daka da su da Gwamnoni da 'yan majalisun dattawa da na wakilai da shugabannin kananan hukumomin wajen tursasawa wannan azzalumar gwamnati ta samar mana da su. Tunda Ai shugaban kasa ba shugaban 'Yan kudu maso kudu bane, shugaban Najeriya ne, kuma muma 'yan Najeriya ne.
Idan kuwa ba haka ba, Ina kara tabbatarwa da wadannan shugabanni namu cewa wallahi a nan gaba guguwar da zata taso, su zata fara lakumewa a karon farko. Allah ya kiyaye. Daga karshe, ina rokon Allah ya bamu zaman lafiya mai dorewa a Arewa da Najeriya baki daya, Ya Allah wannan shugaban kasa kada ka bashi ikon aiwatar da wadannan munanan kudurori akan al'ummar Musulmin wannan kasa. Ya Allah ka hada kan musulmi bisa kan tutar gaskiya da Adalci, Ya Allah ka cecemu, kajikan yara da mata da tsofaffi da gajiyayyu da matasa.

Yasir Ramadan Gwale
26-04-2013  

No comments:

Post a Comment