Yadda Za A Magance Al’amuran Tsaro A Najeriya
Hakkin kowace gwamnati ne ta kare tsaron rayuka da lafiya da kuma dukiyar al’ummarta. Gwamnati itace ke da alhakin kulawa da dukkan al’amuran mutanan da suke karkashinta baki ne ko ‘yan kasa. kula da dukkan dangogin tsaro yana kan hukuma tuna daga tsaron kan iyaka, kula da shige da fice ta sama da ta ruwa. Tunda dukkan masu kayan sarki ko aikin damara suna karkashin hukumane kuma da dukiyar al’ummar kasa ake biyansu albashi. Kamar kuma yadda muka sani shugaban kasa shi ne shugaban kwanmandan askarawan kasarnan baki daya dukkan wani abu da yake da alaka da tsaro shugaban kasa shine mutum na farko akan wannan al’amari.
Sanin kowane dan Najeriya ne cewa sha’anin tsaro ya tabarbare a wannan lokaci da ake fuskantar matsin rayuwa. Al’amura na kara dagulewa a yayin da aikin yi ya yi karanci, jami’o’I da kwalejoji kuma suna ta kara kyankyasar sabbin masu kammala karatu, haka kuma jama’a na ta kara aure da haihuwa, al’umma na karuwa ita kuma gwamnati na ta kara fadada tunani wajen Karin samun hanyar kudin shiga. A daidai wannan lokaci ne kuma al’ummar kasa suka shiga cikin wani hali na zullumi da fargabar abubuwan da ka iya zuwa su zo wadan da suka shafi sha’anin tsaron rayuka da dukiyoyi.
Sanin kowa ne a ‘yan shekarun da basu wuce 15 ba ansamu hasarar rayuka da dukikoyi masu dimbin yawa ko dai ta hanyar fashi da makami ko rikicin kabilanci ko rikin addini ko sanadiyar tashin bam ko hadurra akan manya da kana nan hanyoyinmu koma ta wasu hanyoyin da ba wadannan ba wanda Allah ne ka dai yasan adadinsu a wannan kasa tamu mai al’umma kusan miliyan 167 da kuma kabilu daban da ban, bayaga tashe-tashen hankula da rigingimun kabilanci dana addini da suka sha faruwa kuma suke faruwa a daidai lokacin da kasar ta samu dimbin dukiyar da ba’a taba samuba tunda aka samu Najeriya a shekarar 1914, lokacin da aka hade kudu da Arewa a matsayin kasa daya al’umma daya.
Sannan ga kuma wata sabuwa da ke faruwa kamar yadda mukaji a makon da ya gabata cewa wasu kafofin yada labaran kasar nan suka ruwaito labarin yadda wasu tsagerun ‘yan kungiyar OPC masu rajin kare muradun yarbawa suka yi barazanar yaki da kungiyar boko haram a birnin Ikko. Hakanan a makon da ya gabatar ne muka ji ‘yan tsagerun yankin Neja Delta suka yi tattaki da niyar yin zanga zanga a babban birnin tarayya Abuja, duk da jami’an tsaro sun yi nasarar dates su a garin Lokoja, hedikwatar jihar Kogi. Suma yan kungiyar MOSSOB, masu fafutukar ganin kasar Biafra sun kara nanata kudurin su na ganin ko dai dan kabilar Ibo a bashi dama a shekara ta 2015 domin ya hau kujerar shugabancin kasar nan ko kuwa a basu dama su kafa kasar su domin su cika burin jagoran su, Ojukwu da ya kwanta dama a yan kwanakin baya.
Duk dan Najeriya yasan da cewa kullum ana kara samun yawan aukuwar al’amura da suke nuna cewa tsaro yayi karanci a kasar nan. Kama daga abin da ya shafi fashi da makami da fyade da tashin bamabamai da karuwar hadurra akan manya da kana nan hanyoyi, dama rikicin kabilanci da na addini da ya ki ci yaki cinyewa. Duk wannan ‘yan Najeriya na sane dasu, kuma ana ta dogon turanci akan yadda ya kamata wadan da al’amarin yashafa su fuskance shi. Idan ana so ayi maganin tabarbarewar tsaro a Najeriya to kuwa kamata ya yi gwamnati ta dauki mataki kamar haka.
Abu na farko, dole ne duk inda aka samu labarin fashi da makami ko fyade ko daba ko kalare ko tashin Bam ko fadan kabilanci ko na addini, garkuwa da mutane, fasa bututun mai, da ta’addacin tsagerun Neja Delta, OPC, MASSOB, Boko Haram. Tilas ne gwamnati ta kame wandan nan mutane kamar haka, na farko Mai unguwa da kansila da dagaci da shugaban karamar hukuma da DPO na ‘yansanda da darakta ‘yansada na farin kaya na wannan karamar hukuma ko kuma yankin da abin ya faru. Akan cewa tilar su bada bayanin ya akayi abin da ya faru wanda yake da alaka da tsaro ya auku, saboda duk al’amarin tsaron wannan yanki yana karkashin kulawarsu ne, saboda sune wakilan hukuma ta wannan bangare a kuma wannan yanki. Domin a matakin farko wadan nan sune wa ‘yanda suke da hakkin kula da shiga da fitar mutane na yankin da suke ciki, wajibi ne gwamnati ta tuhumesu akan cewa kodai sunyi sakaci wani mugun mutun ko wasu miyagun mutane azzalumai sunzo da nufin cutar da al’umma, ko kuma dama da hadin bakinsu aka aikata dukkan ta’asar da ta afku. Tunda sune suke shugabantar al’umma a wannan yanki duk abin da ya faru su ake tunkara.
Abu na biyu, wajibi ne gwamnati ta gudanar da binciken na gaggawa kuma bisa gaskiya da adalci akan dukkan rahotannin da suka shafi tsaro. Dole ne kuma a hukunta dukkan wanda aka kama da laifi komai girman mukaminsa akuma bayyanawa jama’a suji. Sannan hukuma ta gargadi jami’anta akan sakaci da aiki da kuma hukuncin duk wanda aka samu yayi sakaci da aikinsa har aka samu Baraka ta gefensa.
Abu na gaba kuma, dole ne gwamnati ta samarwa jami’anta ina nufin na tsaro cikakkun harkokin jindadi da walwalarsu da ta iyalansu. Tundaga kyakkyawan albashi da kuma kayan aiki wadan da sukayi dai dai da zamani, wanda wannan shi ne zaiyi maganin cin hanci da rashawa akan harkar tsaro.
Idan har gwamnati ta gwada daukar wadannan matakai al’amura basu kyautata ba to tabbas kamar yadda masu Magana suke cewa da akwai lauje cikin nadi, akwai wadan da sukewa gwamnati zagon kasa ta fuskar tsaro, akwai baragurbi kuma dole gwamnati ta binkitosu tare da hukunta su ko su wane kuma komai girman mukaminsu.
Domin munyi imani dukkan wasu makamai ko na harbi ko masu fashewa da suke yawo acikin kasa gwamnati tana da masaniyar daga inda suka fito. Domin makami ba kamar abinci bane da ake shukawa a gona haka kuma ba kamar kaya bane da kowane dan kasuwa zai iya sana’antawa a masana’antarsa, tabbas duk inda kaga makami yana da alaka da hukuma ko ta kusa ko ta nesa domin yarjejeniyar mallakar makamai da kasashen duniya suka cimma ta Kyoto Da kuma ta Geneva ta tabbatar da haka. Ashe kaga kenan babu yadda za’ace hukuma batada masaniyar yadda makamai suke yawo acikin kasa ko a hannun jami’anta ko a hannun daidaikun mutane.
Idan kuwa aka bi dukkan wadan nan matakai al’amura basu kyautata ba to tabbas gwamnatin da kanta itace kanwa uwar gami, kawai ana yaudarar al’ummar kasa ne akan sukurkucewar tsaro amma da saninta akayi wasarari da harkokin tsaro don baiwa wasu dama suci karensu babu babbaka alabasshi daga baya a cimma wata boyayyar manufa. Dadin dadawa munsan cewa al’amuran da suka shafi tsaro a kowace kasa suna da bukatar sirri to wajibin hukuma ne ta san irin dabarun da za’abi wajen kyautata al’amura da suka shafi sha’anin tsaro kuma suke da bukatar sirri wanda munsan gwamnati tana nata kokarin. Munsan akwai dokar da gwamnati ta sanyawa hannu kwanakin baya ta ‘yancin neman bayanai wato Freedom of information Bill, munsan da cewa duk inda mutum ya kaiga neman labarai bazai binciki ya ake gwamnati take da makamai ba kuma nawa aka siya nawa aka batar.
Mun san da cewa duk wani makami da yake a Najeriya idan ba na gwamnati bane wanda ita keda al’hakin mallakarsa da kuma kulawa da shi, kuma babu ta yadda za’a yi ya fita batare da masaniyar wadan da abin ya shafa ba. To kuwan babu ta yadda zamu yarda cewa makamin nan ba shigo da shi akayi kodai takan iyaka ko kuma ta gabar teku ko ta amfani da jirgin sama wanda duk wadan nan gurare al’hakin gwamnati ne ta kula da su, idan kuwa tayi sakaci da wannan bangare to tabbas wannan ko wace irin gwamnati ce bata cancanci acigaba da bata goyon baya ba tunda bata iya tsarewa al’umma kasaba ta fuskar tsaro. Haka kuma babu wani mutum da zai iya kera makami ba tare da gwamnati tana da masaniya ba domin dukkan wani abu da ya shafi tsaro babu wanda yake da karfin iko akansa sama da hukuma.
Kamar yadda mukajicewa hukumomi na kokarin sanya na’urar binciken a kofar shiga majalisa mai gani har hanji wadda ake kira Fulbody scanner don kare ‘yan majalisa. To suma al’ummar kasa suna bukatar wannan na’ura don kare rayuwarsu da dukiyarsu, domin ‘yan majalisa ba su kadai bane ‘yan Najeriya ba muma talakawa muna da hakkin gwamnati ta kula damu ta dukkan bangarori ba sai ta fuskar tsaro ba kawai. Kuma bisa yadda mukaji shugaban kasa ya gabatar acikin kasafin kubin shekarar nan mai kamawa anware kudi kusan Naira Biliyan N921.91 a sha’anin tsaro muna fatar al’amura su kyautata wanda a cikin wannan halin ne abun takaici zaka iske ba wanda suka fi cutuwa da rashin tsaro da mummunan talauci da rashin aikuin yi da rashin hadin kai da shugabanci irin alummar Arewacin Najeriya.
Lallai muna kira ga gwamnati ta yi iyakar iyawarta wajen kawo karshen tashin bamabami da kuma rikicin kabilanci dana addini da yaki ci yaki cinyewa a birnin Jos da sauran sassan jihar filato da garkuwa da mutane da fyade da satar jarirai a asibitoci da satar mutane akan hanya da rikicin manoma da makiyaya da wadan nan makudan kudaden da aka fitar wajen sha’anin tsaro.
Idan ba haka ba kuwa abinda Bahaushe yake cewa abinda yaci doma bazai bar awe ba. Wanda wannan yake nuna irin juyin juya halin da yake faruwa yanzu haka a yankin tsibirin larabawa da Arewacin Afrika babu abin da zai hanashi wanzuwa a Najeriya, kamar yadda mukaji kwamitin da shugaban kasa ya kafa akan rikicin bayan zabe karkashin jagorancin dattijo Sheikh Ahmad lemu sunyi gargadi akan wannan batu. Lallai hukumomi su sani duk wadan can abin da suke faruwa a yankin kasashen larabawa rashin Adalci ya janyoshi, don haka adalci shi ne zai zaunar da kasarnan lafiya, kuma shi ne zai cigaba da zaunar da kasar nan a matsayin kasa daya al’umma daya. Muna tabbatarwa da gwamnati kamar yadda suka sani yanzu duniya tana tafiya ne bai daya. Allah ya taimaki kasarmu Najeriya ya bamu lafiya da zama lafiya.
Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@hotmail.com
http://yasirramadangwale.blpgspot.com
No comments:
Post a Comment