Saturday, December 10, 2011

Makarantun kwana: Annobar Madigo da Luwadi daga ina?

Ya ‘yan uwa barkanmu da sake saduwa, da kuma fatan za a gafarceni akan wannan maudu’I maras dadinji. Ya dan uwa mai karatu lokaci ne ya yi na mu fito mu fadi gaskiyar yadda al’amura suke, ina fatar za a yimin kyakkyawar fahimta, kuma za’a gafarceni bias furta wadan nan kalamai masu matukar nauyi . Zance na gaskiya makarntun kwanan kamar yadda muka sansu a lokacin baya yanzu abin ba haka yake ba.

Makarantar kwana, itace makaranta wadda tafi hada zumunci so sai tsakanin dalibai. Kuma idan banyi karya ba zumuncin ‘yan makarantar kwana bai cika baci ba ko lalacewa komai tsawon lokaci bayan kamala makaranta. Kusan idan ka dauki rayuwarmu gabaki daya zumuntace tun ta makarntar sakandare, mafi yawan dalibai basa wasa da wannan zamatakewa da sukayi a makarantun sakandare, musammanma idan akace makarantar kwana ce. Wannan ce ma ta sanya kake jin kungiyoyin tsaffin dalibai na aji kaza a makaranta kaza. Wanda da wuya kaji na daliban makarantu jami’a ko gaba da sakandare ba.

Kusan daliban makarantar kwana sukan ce duk wanda baiyi makarantar kwana ba to da sauransa a harkar karatun Boko. Domin rayuwar makarantar kwana wata irin rayuwa ce da take da tasirin gaske ainun, hakika duk irin yadda za a baka labarin makarantar kwana ba kamar kaje bane. Domin yara galibi wadan da suke gab da lokacin balaga kan samu kansu cikin wata irin rayuwa wadda babu uwa babu uba, sai dai kawai abokai da yayyi da kanne na makaranta. Annan ne akan kulla abota ta hakika kuma mai dorewa domin kuna tare ku kwana ku tashi ku ci-abinci koda yashe tare. Wannan irin rayuwa ba karamin dadi gareta ba.

Da can idan muna hira da yayyinmu mata ko maza idan suna bamu labarin makarantar kwana sai muji wata irin duniya ce mai dadi kamar kayi tsutsu kaje ka risketa, haka kuma idan ana baka labarin “seniority” sai kaji an zare maka sha’awar makarantar kwana, domin ana bada wanki da debo ruwa da wanke-wanke da tsallen kwado da kama kunne da sauransu wannan kan sa yara su tsoraci makarntar kwana.

Hakika lokacin da nayi makarantar kwana na tabbatar da dukka abubuwan da ake ta fadamin a baya lokaci mai tsawo. Na tuna wata rana da shugaban makaranta wato principal ya tara dalibai “juniors” da “seniors” wato manya da kanana inda yace “abin da nake so daku manyan dalibai hukumar makaranta bata hana ku baiwa kannenku wanki ba, amma abinda muke so daku idan kun bada wanki ku bada sabulu” munsha wahalar wanki da debo ruwa a wannan lokacin domin bama iya samun ruwa daga cikin makarantar Unity Karaye sai munje wani kauye da ake kira kusalla ko kuma munzo cikin garin karaye Torankawa ko kuma kofar zango sannan mu samu ruwa; galibi wannan yafi faruwa a zangon karatu na biyu da na uku lokacin da dukkan rijiyoyin makaranta sun kafe ga kuma rani yayi nisa damina bata soma ba.

A irin wannan rayuwa ta makarantar kwana babu lokacin da dalibi ya fi kauna kamar lokacin darussa da kuma lokacin barci domin sune lokutan da babu wanda zai kiraka ballantana ya aike ka. Zaka samu yara wadan da suke ‘yan ajin farko jss 1 zuwa jss 3 basa iya zama cikin dakunan kwananansu domin gudun duka ko kuma aike, dan ajin ss 1 shine wanda ya fara jiyo kanshin ‘yanci sau da yawa zaka samu sukan zauna acikin dakunansu. Laifi kankani dalibi zaiyi ayi masa hukunci kama daga tsallen kwado zuwa kama kunne ko hawan bango da sauransu, munsha tsallen kwado kamar sojoji.

Gaskiya idan zan iya fada makarantar kwana na daya daga cikin makarantun da suke gyara yara a wancan lokaci, domin ananne za’a koya maka gaida “senior” duk safiya haka kuma dole idan ya taho kaima ka taho ka dakata har sai yashige dalibai juniors sukanyi ladabi irin wanda basa yiwa iyayansu ko yayyensu, idan akayi sa’a wani daga haka shi ke nan ya mike da wannan tarbiyya.

Zance na gaskiya makarantun kwana na yanzu abin ba haka yake ba. Idan zan iya tunawa babbar matsalar da akafi fuskantar a lokutan baya bata wuce dalibai masu shan taba sigari ba da kuma dai sauran abubuwa na kuruci dangin hauka da ba a rasa ba a tsakanin dalibai.

A irin yadda nake samun labari yanzu shine duk abin da na sani da akeyi a baya na seniority yanzu ya zama tarihi domin yanzu gwamnatoci kan yi kokarin katange makarantun maza ba kamar da ba kawai da za a yanki daji ba, yanzu bayan katange makarantu akan samarmusu da famfunan tuka-tuka wanda wannan shi ya rage musu babbar matsalar ruwa. Sai kuma wata babbar annaoba da ta kutso kai gadan gadan cikin makarantun kwana kuma take ci kamar wutar daji itace dabi’arnan ta Luwadi ko kuma Madigo a makarantun mata.

A wani rahoton da na karanta yana cewa kusan kaso 12 na daliban Najeriya dake makarantun kwana suna aikata wannan danyan aiki na madigo da luwadi wanda kalmomin basu da dadin fada a baki ina fatar za’a gafarceni. Haka kuma wannan rahoton yace kusan kaso 15 na daliban jami’a suma sukan aikata wannan mummunan aiki na zakkewa juna da nufin biyan bukatar sha’awa. Banida cikakkiyar masaniyar wannan rahoton gaskyane ko kuwa akasin haka.

Kwanakin baya wata yarinya da bansanta ba ta rubutomin wasika daga wata makarantar kwana dake cikin birnin kano tana gayamin don Allah na fadakar akan wannan matsala da take faruwa a makarantun mata, ta fadamin a cikin wasikar cewa Wallahi lokacin da aka kaita hankalinta ya yi matukar tashi domin tace Wallahi rububinta aka ringa yi kamar ‘yartsana, tace ana yaudarar yara da kayan kyale-kyale da kuma nuna masu soyayya, tace idanma kika ki akan yi miki ta karfin tsaya ta hanyar rikeki da toshe miki baki, wannan yarinya ta sahidamin cewa tayi karyar rashin lafiya kawai don ta koma gida ta sanar da mahaifinta abin da ke faruwa, tace amma da tazo gida ta sanar da mahaifinta gaskiyar lamari sai ya karyata ta tare da cewa batason makarantarne shi yasa ta fake da wannan abu.

Tabbas wannan abu ba karya bane. Domin da zakayi hira da daliban makarantun kwana ka tambayesu gaskiyar wannan al’amari zasu sanar da kai cewa lallai wannan abin yana kara samun tagomashi a tsakanin dalibai. Domin binciken da na gudanar ya tabbatarmin da haka. Dalilan da kansa haka yaduwa cikin sauri sune kamar haka.

Abu na farko, kuruciya da kuma karfin balaga domin galibi akan kai yara makarantar kwana adaidai lokacin da suke kan ganiyar balaga ko kuma suke gab da balaga. Kamar yadda masana suka ce mafi yawanci mazakuta takan cika girmanta ne a shekaru 18 zuwa 22 wannan takan sanya galibi sha’awar yara takan motsacikin sauri. Haka kuma abu na gaba shine yanzu zamani yazo inda yawancin yara kan tafi da wayoyin hannu a boye masu dauke da fina-finan batsa masu yawan gaske, me kake jin zai faru alokacin da yara suke kan ganiyarsu ta balaga kuma ga fina-finan batsa a tsakaninsu?

Abu na gaba shine harkar wasan kwallan kafa, itama wata muhimmiyar hanyace da kanjefa mafiyawanci yara fadawa cikin wannan mummunar ta’ada domin ta haka ake yaudarar wasu da daman gaske, sannan itama kwallon kasashen turai ta Champions league da laliga da sirie A da sauransu sun taka muhimmiyar rawa wajen jefa da yawa daga cikin yaranmu cikin wannan yanayi. Domin akan kulla mummunan kawance tsakanin wannan yaro da wancan yaro. Wato abin yakai yanzu hattana irin mukaman da akan nada yara wato prefect sai annemi yaro ya bada kansa sannan akai sunansa domin tantancewa kuma wannan ana hada baki da wasu daga cikin miyagun malamai marasa kishi da tsoron Allah.

Haka suma makarantun ‘yammata suna da nasu hanyoyi na yaudarar kamar sayan kayan kwalliya irin na zamani da suturu masu dankaren tsada da sarka da yari da sauran abubuwan da ka iya jan hankalin yara mata cikin sauri.

Wannan babban kalubale ne ga iyaye. Lallai wajibin kowane uba ne ya tabbata ya kula da tarbiyyar ‘ya ‘yansa, musamman suturarsu da inda suke zuwa da kuma abokanan mu’amalarsu. Kusan yanzu yana daga cikin abinda iyaye basu cika dubawa ba shi ne abokanan mu’amalar ‘ya ‘yansu, domin zaka ga basu cika basu muhimmanci ba, wanda galibin mu Hausawa mukan dora laifin lalacewar ‘ya ‘yanmu akan abokai kowa ka tambayeshi zaice abokai suka lalata masa yaro haka idan da zaka tambayi uban lalatacce zai gayamaka cewa lalatattun yara suka bata masa yaro, amma duk da haka iyaye basa daukar wani mataki akan wannan batu.

Sannan, yana daga cikin hakkin hukuma ta tsarewa al’umma tarbiyya da kuma mutunci, hukuma itace zatayi tsari dangane da wannan abu da yake cigaba da yaduwa cikin sauri, haka kuma ma’aikatar ilimi da malaman makarantu yana da kyau su sanya ido sosai akan dalibai domin amana ce aka basu kuma su kanda sani sai Allah ya tambayi kowa dan gane da amanar da aka bashi tundaga iyaye har zuwa malami, kuma dole ne su duba hanyoyin da za’abi wajen ganin anshawo kan wannan matsalar tare kuma da hukunta duk wanda aka kama da aikata wannan laifi a bainar jama’a, wanda wannan inaganin itace kadai hanyar da zata iya kawo raguwar wannan aika-aika, zai zama darasi ko izna ga duk wanda yake aikatawa yaga yadda aka hukunta mai yi a bainar jama’a koda kuwa bulalace. Domin babu wanda zai so yaji cewa dansa ko ‘yarsa suna aikata wannan danyan aiki. Allah ya shiryi al’ummarmu.

Yasir Ramadan Gwale

yasirramadangwale@hotmail.com

http://yasirramadangwale.blogspot.com

No comments:

Post a Comment