Wednesday, July 29, 2015

Wayar Salula Da Internet Sun Zama Alakakwi


WAYAR SALULA DA INTERNET SUN ZAMA ALAKAKAI 

Yana daga cikin alkhairan da mu al'ummar wannan zamani muka samu shi ne na wayoyin salula da internet da suka saukake mana  al'amura. Kusan yanzu komai mutum zai iya yi da wayarsa, ya shiga duniyar gizo ya wataya. A da wani abun idan ya faru a garinaku da safe karfe goma ba zaka sani ba watakila sai lokacin BBC ko wata kafar watsa labarai ta waje,  amma yanzu cikin sauki mutane na samun dukkan irin labarin da suke so dake faruwa  ko ina a duniya.

Yanzu halin da ake ciki wayar salula ta kashe kasuwar abubuwa da yawa. Yawan masu amfani da computer ya ragu,  domin yanzu duk abinda computer zatai maka wayar salula ma zata iya, sai fa kadan. Yanzu babu bukatar ka jibge tarin kasakasan Radiyo dan jin wa'azi ko disco. Kasset 100 ko 200 da zaka ajiye ya cinye maka guri yanzu dan karamin abu da bai wuce maballin riga ba zai kwashe su duka.

Idan ka kalli wancan janibi sai kaga wayar salula ta kawo nakasu ga kasuwar Radiyo da Computer da kuma masu sana'ar sai da kaset na kida ko na wa'zai. Domin abinda sai ka saya da kudi a da yanzu kusan a bagas zaka same shi, wajen wanda baka sanshi ba be sanka ba, wuyarta kawai kana da Internet. 

Kwanaki dan uwa Malam Hamisu Nasidi Baban Auwaab​ yake bamu labari cewar, suna zaune bayan sun gaida kakarsu sai kowa ya koma gefe ya dauko waya yana latse latse, abinda kakar ta ce musu "ku matasan yanzu bakwa yin lazimi sai latse latsen waya" a hakikanin gaskiya lokacin da naga wannan magana ta tsaya min a Rai, domin yadda naga yadda muke amfani da wayoyinmu abin na neman zamar mana alakakai. 

Kusan yanzu abinda muke fara yi daga tashinmu daga bacci shi ne danna waya, haka kuma abu na karshe da galibi muke yi shi ne danna waya. Da yawa tuni suka dena yin Azkar na safe da yamma, kai yanzu hatta azkar na bayan idar da Sallah wasu sun dena, sabida gaggawa mutum ana idar da Sallah zai dauko waya yana duba Whatsapp ko Facebook​ da sauransu, kuma wannan lamari babu batun su wane, kusan duk munyi tarayya da Limamai da masu bin Sallah da kowa da kowa.

Wayar salula ta ragewa mutane yawan magana. A da sai kaga mutane sun hadu ana tattaunawa, amma yanzu daga an gaisa sai kaga kowa ya dauko wayarsa yana latsawa, hatta a makabarta wajen binne gawa sai kaga mutane na daddanna waya, haka wajen makoki ko gidan biki da sauransu. Wayoyin sun dauke mana hankali da lokaci fiye da yadda muke tsammani. 

Mutane hatta abinci basa iya ci a nitse sai suna danna waya, sabida kowa baya san wani abu ya wuce masa.Aboki sai ka je wajensa amma idan kai lissafi sai kaga yawan danna wayar ku yafi yawan maganarku. Rayuwarmu ta zama kowa ba shi da lokaci, da yawan mutane suna Ikirarin karancin lokaci amma a zahiri lokacin duk yana wayoyinsu. 

Gaskiya dai ga wasu waya ta zamar musu alakakai. Domin hatta sirri yanzu mutane ba su da shi sosai,  domin wani ko ina za shi sai ya rubuta ya sanar, kai wani ko bandaki yake sai kaga ya dauki hoto ya sa a facebook wasu kagansu adakin girki wani a can cikin daki zaka ga ya dau hoto,mata kuwa suyi ta abinci yana konewa sabida waya.

Ni kaina na sha dora girki abincin ya kone sanadiyar dannan waya, wannan ya faru yafi karfin lissafi. Gaba dayan lokutanmu suna Whatsapp da facebook da Twitter da sauransu. Kuma abin mamakin irin wadannan tashoshi na haduwarsa  mutane kullum sabbin ake kirkirowa wani zaure idan ka shiga sai kayi zaton babu kowa, amma sai kayi rajista ka shiga kaga jama’a dankar na ta watayawa. 

Lallai ya kamata mu farga kan yadda babu gaira babu dalili aka dauke mana lokaci. Dalibai basa iya tsayawa suyi karatu da kyau, Malamai basa iya karantarwa da kyau, Kaga Malami na danna waya dalibai ma na dannawa ana shiga shafukan zamunta. Kuma hatta a lokacin Jarabawa duk da gargadi da ake amma sai ka samu wasu suna duba Whatsapp ko Facebook, zakai mamaki mutum ya rubuta cewar yanzu haka ina dakin jarabawa ina neman addu'ar ku. 

Wani yace yanzu hatta hadari idan ya faru maimakon mutane sukai agaji, kawai sai su fara daukar hotuna. Kaga kawai mutane na yada hotuna na tashin hankali dan kawai suna san bada labarin wani hadari da ya afku,  musamman wannan lokacin da Allah ya jarrabemu da tashin Bom mutane daga zarar Bom ya fashi a inda suke, to sun samu aikin daukar Hoto ana yadawa, a wani hoto da na gani a  Gombe da wani Bom ya tashi ga mutum ya a kone da ransa amma naga mutane ba ta shi suke ba daukar too kawai suke.

Yana da kyau mu karawa kanmu lokacin kara kusanta ga Allah. Allah ka shiryemu. 

Yasir Ramadan Gwale​
29-07-2015

Saturday, July 18, 2015

SALLAR BANA : TSAKANIN MUSULMI DA ' YAN SHIAH


SALLAR BANA: TSAKANIN MUSULMI DA 'YAN SHIAH A NAJERIYA!!!

Abin farin ciki ne ainun a wad'annan lakuta ganin yadda kan al'ummar Musulmi a Najeriya ya had'u dangane da batun d'auka da kuma aje Azumi. Hakan babbar nasara ce, kuma alamu ne da suke nuna cin Nasara, domin, a baya mun shaida yadda aka dinga samun sab'ani wajen ganin watan Ramadan da kuma na Shawwal. Inda hukumomi zasu bayar da sanarwa amma wasu su k'ek'asa su ce basu yadda ba, sai sun gani da idonsa,  dan kawai haifar da sab'ani tsakanin Musulmi.

Cikin hukuntawarsa Subhanahu Wata'ala masu wancan ra'ayi sun fara dawowa daga rakiyarsa, inda wannan lokuta ake kara tsuke bakin sab'anin baki daya. Musulmi a kusan gaba d'ayan Najeriya sun d'auki Azumi tare sun kuma yi Sallah tare. Ko Shakka babu wannan zai baiwa Musulmin Najeriya karfi na tunkarar manyan abokan gaba wato SHIAH.

Da yake su mabiya addinin Shiah kullum burinsu shi ne a samu sab'ani tsakanin al'ummar Musulmi,  da burin Kada kai ya had'u. Hakan ta sanya suke kokarin ganin sun tabbatar da sab'anin sun d'auki Azumi daban sun kuma yi Sallarsu daban, sab'anin Musulmi da suka bi Umarnin mai alfarma Sarkin Musulmi Sultan Saad wajen dauka da kuma aje Azumi.  

A har kullum abinda ya kamata mutane su gane kuma su fahimta shi ne cewar, babu wad'an da suke kokarin kawo rarrabuwa ko wargaza zaman lafiya tsakanin al'ummar Musulmi kamar 'yan Shiah. Shugabansu kuma jagoransu Ibrahim El Zakzany shi ne kullum yake ihu da karad'in cewa "HADIN KAI"  amma gashi zahirin sa ya nuna tacacce mayaudari  ne, kullum yaudarar mabiyansa yake da sunan had'in kai, amma kuma ga shi a zahiri yana k'ok'arin tabbatar da samun b'araka da rarrabuwa. 

Daman kuma mun kwana da sanin kokarin cusa rarrabuwa tsakanin Musulmi shi ne abinda 'yan Shia suke ta fatan ganin dorewarsa a kowacce irin al'umma. In sha Allah kuma ba zasu Ci Nasara ba, kamar yadda aka samu wannan had'in kai na al'ummar Musulmin Najeriya, haka za'a  cigaba da samu. Allah ka kara tabbatar da had'in kai tsakanin Musulmi. Ya Allah duk wadan da suke kokarin ganin bayan Musulunci da Musulmi Allah kaga bayansu,  Allah ka bak'anta musu rai da ganin cigaban Musulunci.

Muna addu'ah da sunayan Allah tsarkaka madaukaka Ya Allah ka nesanta mu da zurriyar mu daga Shianci. Allah ka fahimtar da mu addinin Musulunci,  Allah ka bamu lafiya da zaman lafiya. Ya Allah Kada ka baiwa 'yan Shiah nasara a cikin dukkan lamuransu duniya da Lahira. Allah ka taimaki Musulunci da Musulmi.

YASIR RAMADAN GWALE​
18-07-2015

Thursday, July 16, 2015

Ganin Wata



GANIN WATA: Ma'aikatar harkokin addinin Musulunci a Sa'udiyya sun bayar da sanarwa a hukumance cewar a yau alhamis 29 ga Ramadan aka ga Jinjirin watan Shawwal, wanda hakan ke nuna kawo karshen kwanaki Ashirin da tara na watan Ramadan. Dan haka a gobe Juma'a zai zama daya ga watan Sallah In sha Allah.

Labari MARAR Dadi Daga Gombe


LABARI MARAR DADI DAGA GOMBE 

A daidai lokacin da al'umma ke fara shirin Sallah karama a gobe a duk fadin duniya, muka samu mummunan labarin harin Bom da aka kai tsakiyar kasuwa a Jihar Gombe! Wannan babban abin bakinciki ne da takaici ainun, abin akwai Kada zukata a yayin da al'umma ke d'oki da ganin anyi Sallah lafiya, wasu miyagun azzalumai mabiya Tafarkin shedan suke ta kokarin kawo karshen rayuwar mutanan da basu ji ba basu gani ba ta irin wannan mummunar hanya. Allah ya jikan wadan da suka rasu, muna mika ja je da ta'aziyar mu ga Gwamnatin Jihar Gombe da al'Umar jihar baki daya. Allah ka kawo mana karshen wannan tashin hankali da ya addabemu.  

Yasir Ramadan Gwale 
16-07-2015

Tuesday, July 14, 2015

Yakar Boko Haram


YAKAR BOKO HARAM
Babbar matsalar da ta addabi mutanan Nigeria ita ce wannan fitinar ta Boko Haram, har ma da kasashe ma'kwabtan Najeriya. Shi mai aikata laifi musamman irin na ta'addani irin na Boko Haram dabaru gareshi iri iri, a lokacin da jami'an tsaro ko Gwamnati ke k'ara shirin tunkarar wannan Ya'ki gadan gadan, suma a nasu bangaren 'yan Boko Haram ba wai kawai zaune suke suna jiran mutuwa ba.
Kamar yadda bayanai suka nuna cewar itama Boko Haram a yanzu kara shiri suke, domin had'akarsu da k'ungiyar ISIS babbar barazana ce ba ga Nigeria kad'ai ba har da ma'kwabtanmu. Alhamdulillah a yau abinda aka jima ana jira ya tabbata, na sauya jama'an tsaron da PMB ya gada daga Gwamnatin da ta shud'e. Wad'annan sabbin nad'e nad'e da akai an ce galibinsu sun fito daga yankin Arewa Maso Gabas, wanda fatanmu shi ne Allah ya basu ikon murkushe Boko Haram da karfin Allah.
Ba shakka, idan akwai abinda ya kamata mu dage da adduah akansa bai wuce samun zaman lafiya a Najeriya ba. Muna fatan Allah ya baiwa wad'annan jagorori Nasarar dirkake Boko Haram, Allah ka azurtamu da samun zaman lafiya mai d'orewa a kasarmu. Ya Allah Kada ka baiwa 'yan ta'adda nasara komai kaskantar ta. Allah ka baiwa sojojin Najeriya nasara akan wannan Yaki.
Yasir Ramadan Gwale
13-07-2015

Monday, July 13, 2015

Nuhu Ribadu Na iya Zama Sabon Shugaban PDP NA Kasa



MALAM NUHU RIBADU NA IYA ZAMA SHUGABAN PDP NA KASA
Jaridar Leadership Newspapers ta ruwaito cewar tsohon Shugaban hukumar EFCC kuma tsohon dan takarar Shugaban kasa a Rusasshiyar Jam'in yar ACN Malam Nuhu Ribadu na iya zama sabon Shugaban jam'iyyar PDP na kasa nan gaba a babban taron PDP na kasa da zai gudana.
Ba shakka wannan labari ne mai faranta rai, samun mutum irin Nuhu Ribadu a matsayin shugaba zai baiwa PDP damar yaki da cin hanci da rashawa a cikin jam'iyyar, wanda hakan zai bayar da damar samun nagartattun 'yan takara wadan da basu ci amanar kasa ba. Allah ya taimaki Nuhu Ribadu a wannan sabon mukami da zai samu, Allah kai masa jagoranci ka bashi ikon kawo sauye sauye masu alfanu ga rayuwar al'umma.
13-07-2015

Saturday, July 11, 2015

SA'UDIYYA : Sarki Salman Bin Abdulaziz Ya Jagoranci kaddamar da aikin fadada Masallacin Haramin Makkah Da Zai Kunshi Masallata Miliyan Biyu Ba Dubu Maitan


SARKI SALMAN YA K'ADDAMAR DA AIKIN FADADA HARAMIN MAKKAH DA ZAI KUNSHI  MASALLATA MILIYAN BIYU BA DUBU MAITAN 

Ranar Asabar 12 ga watan Yuli bayan da ya sha ruwa a Makkah, Sarki Salman Bin Abdulaziz ya jagoranci kaddamar da aikin fadada Masallacin Haramin Makkah da zai kunshi Masallata Miliyan biyu ba Maitan. Sarkin ya bayyana cewar wannan aikin shi ne zai bayar da damar gagarumin aikin fadada Masallacin da zai kunshi Masallatai Miliyan biyar nan da shekaru goma masu zuwa.

Da yake jawabi a wajen taron Babban Limamin Haram Sheikh Abdurahman as-Sudais (Imam of Masjid alHaraam, Makkah)​ ya bayyana cewa wannan shi ne katafaren aikin fada da Masallacin ka'aba da ba'a taba yin sa ba. Kuma shi ne, na uku a cikin manyan ayyukan fada da Masallacin tun bayan wanda  Sarki Fahad da Abdullah suka yi. Sheikh Sudais ya yabawa Sarki Salman akan wannan aiki tare da yi masa adduar fatan alheri akan kulawar da yake baiwa Masjid al-Haram​, sannan ya kara da cewa kamar yadda kasar Saudi Arabia​ ke kan tsarin Sunnah, ya sha alwashin ci gaba da tafiyar da Masallacin a bisa tsarin Sunnah.


A nasa jawabin Sarkin Kuwait Sheikh Sabah Ahmad Al-Sabah ya gode wa Sarki Salman da kuma Masarautar Sauin a bisa irin wannan kulawa da suke baiwa Haramain dake Makkah da Madina. Sarakunan Bahrain da Dubai​ duk sun aiko da sakon fatan alheri ga Sarki Salman akan wannan katafaren aiki.

YASIR RAMADAN GWALE​
12-07-2015