MUGUN NUFIN 'YAN SHIAH AKAN MUSULMI DA SUNAN AIKIN HAJJI
Su 'yan Shiah ba gaskya bace da su, ba kuma gaskiya suke bi ba, illah kawai makauniyar biyayya da suke yiwa kasar IRAN. Shi yasa sau da yawa zaka samu mabiya Shiah suna b'oye shi'ancinsu, sai fa wadan da asirinsu ya tonu babu yadda zasu yi. Sabinin mu mabiya Sunnah bamu tab'a b'oye Aqidarmu ba, bama shayi ko shakkar wani ko wasu su kiramu da sunan Aqidarmu ko su jinginamu zuwa gareta, ba zaka tab'a ganin wani Ahlussunnah yana kyamar a ce masa 'Dan Izala ko Wahabi ba, domin munyi Imani da Allah kuma mun kyautata masa zaton cewar ba zai tabar da mu ba, dan haka ne muke da yakini cewar ba'a kan hanyar b'ata muke ba.
Ko su kiramu Wahhabiyawa ko 'yan Izala ko duk wani suna da zasu jingina mana, mun yarda kuma mun Amince cewar mu din mabiya Sunnah ne, bama b'oyewa, bama kuma, kin amsawa. Amma har anan Facebook mun sansu da yawa, suna Shiah amma suna b'oyewa, basa son ko kadan a sani. Kaga wannan hujja ce ta cewar sun yi Imani Aqidarsu ba gaskiya bace, kuma b'ata ce, domin indai gaskiya mutum yake bi, baya tab'a shakkar bayyana hakikanin abinda yake bi na Aqidah.
A sabida haka, mabiya Shiah sun san ba gaskiya suke bi ba, kuma ba suda wata manufa, Illa ta kare muradun kasar Iran da yin biyayya ga duk abinda ta zo musu da shi; yasa suka dauka kowa ma haka ne. A dan haka ne, sai suke kokarin Jinginamu ga Sa'udiyya a matsayin masu biyayya a gareta Ido rufe kamar yadda suke yiwa Iran Biyayya Ido rufe.
Amma a zahirin gaskiya mu mabiya gaskiya ne, mabiya Sunnah, ba wai Saudiyya muke wa biyayya Ido rufe ba. Sai dai a bayyane take a zahiri a garemu cewar kasar Sa'udiyya kasa mai tsarki, kasa ce ta Sunnah, kuma tafi kusa da kwatanta gaskiya da bin Sunnah da yada da'awar Sunnah, dan haka muke tare da su a duk wasu abubuwa da basu sabawa Sunnah ba.
Kasancewar Daular Sa'udiyya daula ce ta Sunnah, shi yasa a mafiya yawancin lokaci al'amuransu sukan dace da koyarwar Sunnar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam. Sanin kowa ne, kasar Sa'udiyya bata goyi bayan Gwamnatin Mursi a Masar ba, amma da yawanmu mukai hannun riga da ita akan batun Mursi. kuma kusan kowa yaji matsayarmu ta bakin Sheikh Dr. Sani Umar Rijiyar Lemo dan gane da abinda akaiwa mursi.
Amma duk da haka su 'yan shiah sai basa ganin wannan, suke nunawa duniya cewar mu din ido rufe muke biyayya ga Sa'udiyya kamar yadda ba suda wata manufa sai abinda Iran tace, SUNA MATA BIYAYYA DA DUK ABINDA TA ZO DA SHI. yana daga cikin manufar Iran mayar da Musulunci yayi kamanceceniya da Kiristanci, domin dusashe haskensa, wannan shi ne mugun nufinsu, shi yasa mukaji a wannan lokacin, suka dinga kiran tilas aikin hajji ya koma karkashin kulawar dukkan musulmi ba wata kasa guda daya ba. Duk wanda kaji da wannan furuci, ya sani ko bai sani ba, da yawun Iran yake magana.
Asali su kiristoci mafiya rinjaye suna karkashin Fadar Vatican ne, wadda Paparoma yake jagoranta. Wato Paparoma ba wai kawai shugaban addini bane, domin ita kanta Vatican kasa ce, kuma duk wani Paparoma shi ne shugaban kasar Vatican, a sabida tsarin da suke da shi na yin hadakar kiristoci baki daya wajen tafiyar da duk wani al'amari da ya shafi fadar vatican, shi yasa zaka ji an wayi gari mutumin kasar ARgentina ko Germany ko Poland zai iya zama Paparoma kuma Shugaban kasar vatican.
To misalin irin wannan shi ne manufar Iran akan Musulunci, su mayarda musulunci kamar Kiristanci, ta yadda za'a wayi gari watan wata rana ace mutumin IRAN, HEZBOLA shi ne zai zama shugaba ko sarki da yake kula da biranen Makkah da Madina, shi yasa a wannan lokaci 'yan korensu da 'yan kanzaginsu ke ta yayata cewar tilas shiryawa da gudanar da aikin hajji ya zama mas'uliyya ce ta dukkan musulmi ba Sa'audiyya ita kadai ba. Wannan ita ce manufarsu.
Me kake jin zai faru idan Makkah da Madina suka kasance karkashin jagoranci 'yan Shiah mutanen Iran? Dan haka duk wani me kururwar cewar tilas shirya gudanar da aikin hajji ya zama karkashin kulawar musulmin duniya, to wallahi ya sani ba tunaninsa bane, kuma ba ra'ayinsa bane, wannan shiryayyen al'amari ne da Iran ta shirya, take amfani da 'yan barandanta na sarari da na boye, suke yad'a wannan kururuwar da masu raunin tunani zasu ji kamar akwai gaskiya a cikinta. Babu gaskiya ko ta kwabo illa kokarin sauya tafarkin addinin Allah na gaskiya.
Domin duk lokacin da aka ce ai musulmi ne gaba daya zasu saka hannu akan gudanar da Hajji, to za'a wayi gari kuma, suce ai makkah da madina na musulmi ne duka, dan haka dole musulmi su yi musharaka wajen tafiyar da jagorancin wadannan birane masu tsarki. ya Allah kada ka cika musu wannan buri nasu, ya Allah kada ka basu dukkan wata dama akan al'ummar musulmi. Allah ka taimaki Sunnah da Ahlussunnah ka rusa Shianci da kafurci da duk masu mara musu baya, na sarari da na boye.
Yasir Ramadan Gwale
12-10-2015