ADAMAWA: GWAMNA BINDOW JIBRILA YA FARA DA HAUNI
Affaferatan, Jaridar Punch ta ranar Juma'a 14 ga watan agusta ta ruwaito cewar sabon zababben Gwamnan Jihar Adamawa Bindow Jibrila Umaru ya amince da fitar da zunzurutun kudi Naira Miliyan Dari Biyu (N200m) daga asusun hadaka na Gwamnatin jiha da kanana hukumomi dan yin addu'ah ta musamman akan Allah ya baiwa Jihar Adamawa zaman lafiya.
Ba shakka, jihar Adamawa na bukatar adduar samun zaman lafiya daga ba kuna masu tsarki, na Allah ya dawo musu da dawwamammen zaman lafiya da ba shida casgaro daga barazanar 'an Boko Haram.
Gwamnan Jihar Adamawa ya daga farashin addu'ah da kaso fiye da dari. A lokacin da ake maganar fatara da rashin aikin yi sun addabi mutanan yankin Arewa Maso Gabas. Amma dai ba shakka Malamai a Adamawa zasu more wannan garabasa da wannan zunzurutun kudi.
Yasir Ramadan Gwale
14-08-2015
No comments:
Post a Comment