Thursday, August 27, 2015

Malamai Masu Ci Da Addini


MALAMAI MASU CI DA ADDINI 

Wannan hoto ne na Matthew Hassan  daya daga cikin manyan Malamai masu fada aji a addinin kirista. Yayin da ya kaiwa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ziyara a fadarsa Shekaranjiya. Yanzu mu dauka cewa Sheikh Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ne ya kaiwa Goodluck Jonathan ziyara a lokacin da yake Shugaban kasa, me muke zaton mutane zasu ce? Na tabbata da babu irin zagi da cin mutunci da ba za ai masa ba a dalilin wannan ziyara, sabida muna da karancin tarbiyya da ladabi ga Malamanmu na addini.

Har yanzu banga wani kirista da ya fito yana zagin Kuka ba akan wannan ziyara da sunan cewar yana ci da addini ko yana yiwa kiristoci dodorido. Amma mu da yake mun ragewa kanmu matsayi da daraja, mu kan dauka Malamai ba su da wani ruwa da tsaki a harkar mu'amana da Gwamnati da masu Mulki. Lokacin da aka hasko hoton wasu Malamai na Musulmi sun karya kumallo da Azumi tare da Tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan babu irin zagi da cin mutunci da ba ai musu ba a dalilin wannan ziyara.

Idan Shugaban kasa ya zama Musulmi kowa fatan sa a yi Gwamnati da mutanan kirki kamar yadda muke gani yanzu a Gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari, amma a zamanin mulkinsa  (Goodluck Jonathan) fatan mutane da yawa da burinsu ba haka bane, kullum fata ake Jonathan yayi Gwamnati da mutanan Banza, barayi miyagu yadda za ai ta tsine musu, idan mutanan kirki masu amana suka shiga sai suma su zama abin zargi da tozartawa. 

Tilas mu sani cewar Gwamnatin Najeriya ta dukkan al'ummar Najeriya ce Musulmi da kirista. A kan wane dalili zamu tozarta mu aibata Malamanmu kawai dan sun gana da shugabanni, Musulmi ne ko wadan da ba Musulmi ba, alhali ga Malaman Kiristoci suna ta bibiyar Shugabanni Musulmi babu wanda muka ji yana zaginsu ko yana tozarta su daga cikin kiristoci. Allah ka nuna mana gaskiya ka bamu ikon binta, ka nuna mana karya ka bamu ikon kauce mata.

Yasir Ramadan Gwale 
28-08-2015

Friday, August 14, 2015

ADAMAWA: Gwamna Bindow Jibrila Umaru Ya Fara da Hauni


ADAMAWA: GWAMNA BINDOW JIBRILA YA FARA DA HAUNI 

Affaferatan, Jaridar Punch ta ranar Juma'a 14 ga watan agusta ta ruwaito cewar sabon zababben  Gwamnan Jihar Adamawa Bindow Jibrila Umaru ya amince da fitar da zunzurutun kudi Naira Miliyan Dari Biyu  (N200m) daga asusun hadaka na Gwamnatin jiha da kanana hukumomi dan yin addu'ah ta musamman akan Allah ya baiwa Jihar Adamawa zaman lafiya.

Ba shakka, jihar Adamawa na bukatar adduar samun zaman lafiya daga ba kuna masu tsarki,  na Allah ya dawo musu da dawwamammen zaman lafiya da ba shida casgaro daga barazanar 'an Boko Haram.

Gwamnan Jihar Adamawa ya daga farashin addu'ah da kaso fiye da dari. A lokacin da ake maganar fatara da rashin aikin yi sun addabi mutanan yankin Arewa Maso Gabas. Amma dai ba shakka Malamai a Adamawa zasu more wannan garabasa  da wannan zunzurutun kudi.

Yasir Ramadan Gwale
14-08-2015

KATSINA: Gwamnan Canji Masari Ya Fara Da Aika Aika


KATSINA: MASARIN CANJI YA FARA AIKA AIKA 

Jaridar Daily Trust ta ranar Juma'a 14 ga watan agusta ta ruwaito cewar sabon zababben Gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masar ya amince da fitar da kudi Naira Biliyan Daya da Miliyan dari takwas dan yin Kwaskwarima ga Gidan Gwamnatin Jihar Katsina.

Gwamna Masari na wannan aiki ne a daidai lokacin da yake kalubalantar tsohon Gwamna Ibrahim Shehu Shema da yin almubazzaranci da dukiyar al'ummar jihar, a kuma lokacin da ake cewa ana tsuke bakin aljihun Gwamnati dan rage kashe kudin al'umma ba gaira babu dalili.

Ashe dai na Gwamnan Kano Ganduje Nafila ne, a lokacin da muka kalubalance shi kan kashe Naira Miliyan 180 dan yiwa sabuwar turakar mataimakinsa kwaskwarima. Allah ya kyauta.

Yasir Ramadan Gwale 
14-08-2015

Tuesday, August 11, 2015

KANO: Gwamna Ganduje Ya kaddamar Da Mummunan Yaki Akan Kwankwaso


KANO: GANDUJE YA KADDAMAR DA MUMMUNAN YAKI KAN KWANKWASO

Jaridar Vanguard ta ranar asabar 9 ga watan Agusta, ta ruwaito cewar, wani mummunan yakin cacar baki ya kaure tsakanin gwamnan Kano magabaci Sanata  Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso​ da kuma Gwamna mai ci Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR​. Wannan mummunar musayar yawu dai ta zo ne a lokacin da kungiyar daliban Arewacin Najeriya da ke karatu a kasar Masar suka kaiwa Gwamna Gandujen ziyara a ofishinsa a makon da ya wuce.

Gwamna Ganduje yace, tsohon mai gidansa Sanata Kwankwaso ya kai yara 'yan asalin jihar Kano Karatu kasashen waje daban daban, amma ya yi tafiyar ruwa da kudinsu  kimanin Naira Biliyan uku. Gwamna yace halin da daliban suke ciki na rashin biya musu kudi ba laifinsa bane, laifin Kwankwaso ne.

 Wannan batu dai a cewar Vanguard ya janyo wani kazamin Martani daga bangaren tsohon Gwamna Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, wanda tunda ya tafi Abuja bai sake zuwa Kano ba. Wasu bayanai sun nuna cewar Gwamna gwanduje ya sha alwashin fede biri har wutsiyarsa game da wannan batu na kudin daliban da Kwankwaso ya tura waje Karatu.

Yasir Ramadan Gwale
09-08-2015

Friday, August 7, 2015

Sabon Ofishin Mataimakin Gwamnan Kano


SABON OFISHIN MATAIMAKIN GWAMNAN KANO DA YAKE JIRAN LAMUSHE MILIYAN 180

Wannan ne fa sabon ofishin Mataimakin Gwamnan Kano da Gwamnatin Kwankwaso da Ganduje ta gina watanni hudu da suka wuce akan kudi Naira Miliyan dari uku da uku (N303m) wanda yanzu sabon Gwamna kuma tsohon mataimakin Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje yace zai lakume zu zunzurutun kudi Naira Miliyan Dari da tamanin (N180m). Kai Jama'a!  Gwamna Gandujen Kwankwasiyya watansa biyu ka call a wannan sabon ofishi ya fice ya baiwa sabon mataimakinsa,  abin tambayar shin a iya zaman Gwamna na wata biyu a wannan ofishi har yayi masa illar da zai ci wannan zunzurutun kudi?

Satar Kud'in Gwamnatin Kano A Bainar Jama'a!!!


SATAR KU'DIN GWAMNATIN KANO A BAINAR JAMA'A!!!

Jaridar Premium Times​ ta Juma'a 7 ga watan Auguta, ta ruwaito cewar, Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR​, ya amince da fitar da kudi wuri na gugar wuri har naira Miliyan dari da Tamanin (N180m) domin yin kwaskwarima a sabon ofishin mataimakin Gwamnan da gwamnatin kwankwaso da ta gaba ta gina shi akan kudi Naira Miliyan 303 watanni hudu da suka shude.

Wannan fa sabon office ne da aka gina aka kawata shi da dukkan kayan alatu watanni biyu kafin saukar Gwamnatin Rabiu Musa Kwankwaso​ wadda Ganduje shi ne mataimaki, kuma shi ne ya shiga wannan sabon office da aka gina, watansa biyu kacal a office din Gwamnatin ta shude. Dan Allah wannan wace irin satar dukiyar al'umma ce haka a bainar Jama'ah ko kunya babu?

Shin wannan ba abin kunya bane a wajen Gwamna ace ya amince da fitar da wadannan zunzurutun kudi dan yin kwaskwarima ga ofishin da ya bari watanni biyu da suka gabata. A daidai lokacin da ake cewa ana tsuke bakin aljihu sabida gwamnatoci ba su da  kudi, a daidai wannan lokacin ne gwamna zai yi wannan muguwar facaka da almubazzaranci da dukiyar al'umma!

Rahotanni suka ce hatta albashi Gwamnoni sun kasa biya, sai da gwamnatin tarayya ta taimaka musu da kudade sabida matsalar kudi da suka shiga, babu kudi a asusunsun gwamnatocin jihohi! A wannan yanayin ne Gwamnan Kano zai taka wannan mugun ta'adi da dukiyar al'Umar da suka zabe shi dan samun saukin lamura. Haba Gwamna, Wannan fa sata ce.

Duk da haka kuma, wai Gwamna ya bayar da umarnin korar ma'aikata 2000, wanda idan laifi akai na daukansu har da shi tunda gwamnatin da yake ciki ce ta dauke su aiki... Ya kamata Gwamna yaji tsoron Allah ya dawowa da al'umma dukiyarsu sannan a dawo da ma'aikatan da aka kona babu gaira babu dalili.

Lallai Gwamna ya sani, mu al'ummar Kano a yanzu matsalar samar da tsabtataccen ruwan sha da magunguna a asibiti da samarwa da manoma taki a farashimai rahusa, da inganta Ilimin Furamare da sakandare da karasa ayyukan Gwamnatocin da suka gabata suka bari sune abubuwan da suka dame mu, ba facaka da almubazzaranci  da kudin gwamnati da sunan aikin baban giwa ba.

Da yawan unguwanni an farke musu tituna,  da zummar yin aikin titi amma an barsu haka ruwan damuna yana musu ambaliya, wannan su ne irin misalin ayyukan da suka damu al'umma suke bukatar Gwamna ya fitar da kudi dan karasawa ba wannan satar da sunan aikin Gwamnati ba.

Yasir Ramadan Gwale​
07-08-2015

Wednesday, August 5, 2015

Me Ya Sa Ake Kiran Gwamna El-Rufai Da Me rusau?


ME YASA AKE KIRAN GWAMNA EL-RUFAI DA ME RUSAU?

Na tambayi kaina wannan tambayar akan dalilin da yasa ake yiwa Gwamna Malam Nasir El-Rufai da sunan 'Me Rusau', a Madadin a kira shi da Mai Ginawa? Rushewa ai ba ginawa bane, domin ginawa shi ne aiki, rusawa kuwa aika-aika ne! Ba mamaki nine ban fahimta ba. Watakila a lokacin da el-Rufai yayi Ministan Abuja ya rushe gidajen jama'a da yawa shi yasa ya samu wannan suna.

Amma ni a fahimtata el-Rufai ma'aikaci ne, kuma yazo domin ya hidimtawa al'umma a matsayinsa na Gwamna ba kuntatawa ba. Ba mamaki mutanen da aka ce za'a rushewa gidaje a Zaria sunyi ba bisa doka bane. Daman kuma hakkin hukuma ne tsare doka, yana da kyau a wasu lokuta a nunawa al'umma cewar ba fa kara zube kawai ake rayuwa ba, akwai doka, kuma akwai hukuma.

Bana ko shakkar cewar mutanan da aka basu notis na su tashi za'a rushe gidajensu, sunyi kasassabar sayan filayen gwamnati da yin gini a inda bai kamata ba. Amma abin tambayar shi ne, me yasa Gwamna ya zabi wannan lokaci na damuna dan ya rsuhe wadannan gine gine da ake cewar anyi ba a inda ya dace ba?

Hakkin Gwamnati ne ta tsare tare da kula da al'umma ta dukkan janibin rayuwarsu. Gwamnati ita yafi kamata ta nunawa al'umma jin k'ai da tausayawa sama da kowa, a irin wannan yanayi na damuna da ake samun ruwa mai yawa, wad'an da suke da gidajen tabo hankalinsu a tashe yake idan ruwa ya tsawaita, a wannan lokacin za'a ce wasu su tashi za'a rushe gidajensu, saboda dawo da hakkin hukuma? Haba Gwamna!

Inama a ce gwamnati ta yiwa wad'annan mutane rangwame zuwa lokacin girbi bayan damuna ta jima da wucewa sannan a yi batun wannan Rusau! Nayi ta mamakin yadda masu baiwa Gwamna Shawara basu bashi shawara akan ya maida hankali wajen inganta harkokin lafiya da noma da samar da taki a wannan lokacin na damuna ba. Amma sai suka bada shawarar Rushe inda ba shuka za ai ba.

Wadannan mutanan sunyi kuskuren sayan filin hukuma sukai gidaje. Amma a zance na gaskiya, ya akai hukumomin baya suna gani ana yin gini ba inda ya dace ba, amma suka kasa tsawatarwa? Ina hukumar tsara birane masu sawa gini jan fenti? Ina ma'aikatan kasa da safiyo? Duk suna ina aka sayarwa da al'umma inda bai kamata ba. Ana maganar wasu sunfi shekaru 20 da mallakar fulotai a wajen!

Ya kamata Gwamnan Kaduna ya tausayawa wadannan mutane, ko da kuwa da basu diyyar da bata kai k'imar gidajensu ba, dan sauk'ak'a musu radadin halin da suke ciki. Babban burinmu shine muga Gwamna Nassir el-Rufai yana ginawa ba rushewa ba, akwai abubuwa muhimmai da suke da bukatar hanzarin hukuma na gaggawa da suka fi wannan Rusau a wannan lokaci.

Suma kuma al'umma ya kamata kowa ya shiga taitayinsa, musamman masu san banza na sayan filaye a gurare masu tararrabi. Dillalai da suke kasuwancin irin wadannan haramtattun filaye ya kamata suma a dinga kamasu ana yi musu Shari'ah, domin da yawa su ke zuga mutane su sayi waje me hadari irin wannan. Allah ya kyauta.

Yasir Ramadan Gwale
05-08-2015