APC: MUHIMMIN DARASIN SIYASA YARABAWA ZASU KOYAWA 'YAN AREWA!!!
Ba zan taba yarda cewa ba da gayya shugabannin APC na kas suka dinga fusata wasu 'yan Jam'iyyar daga nan Arewa ba, dan a karya kwarin guiwar gamayyar tun kafin al'amura su kankama, dan hanawa wani dan takara mai karfi samun kaiwa gaci daga Arewa ba. A farkon lamarin kafa APC ta shammaci kowa a Nigeria, kuma tunanin mutane da dama ya tafi akan cewa zasu kai labari matukar an dore akan yadda aka taho, amma daga baya duk lamura suka sauya. Abin da yake daure min kai shi ne yadda jam'iyyar da ta ke san kafa gwamnati bata nuna damuwarta akan zogayewar da magoya bayanta suke yi, wasu ma nuna musu ake su kama gabansu idan tsarin bai musu ba, kuma wai masu son karbe gwamnati daga jam'iyya mai mulki.
Wannan ta sanya na fahimci PDP da gaske suke, da suke cewa Mulki zai tabbata a hannunsu har wajen shekaru 60 koma fiye, domin sun iya dinke mafi yawancin barakar da ta taso musu. Shi ya sa basa yin fushi da nasu matukar za'a amfana da shi.
Tarihin siyasar Arewa ya nuna akwai dadadden tarihin alakar siyasa tsakanin yankin Arewa da yankin Kudu maso Gabas da kudu maso kudu. Awolowo daga yankin Yarbawa yana daya daga cikin 'yan siyasar kudu da ya tsani Arewa matukar tsana, kuma galibin Yarabawa suna da irin wannan ra'ayi. Amma sai muka yi wani mugun kwadon da cinsa da wuyar gaske.
A ganina babban kuskuren da 'yan Arewa suka yi a siyasance da suka dauki Amanar siyasa suka mikawa Yarabawa, mutanan da har gobe basu yarda da mutumin Arewa ba, kuma 'yan Arewa suka nunawa Yarabawan dukkan dogaron cin zaben mutumin Arewa na ya zama shugaban kasa ya rataya akan su Yarabawan, dan haka su ke rawa suke murna tarkonsu ya kama burgu.
'Yan Arewa da ke cikin APC kamar sun kidime, suna ji suna gani suka hakura da yankin Kudu maso kudu da kudu maso Arewa a siyasance, sun nuna ba zasu iya yin wani katabus ba a yankin. Shgaban kasa kuma ya fahimci hakan shi yasa yake rawa namansa na jaka, ai daga lokacin da ake yaki ka fara kare kanka to anci nasara a kanka. Tabbas, Yarabawa zasu koyawa mutanan Arewa da suka basu amannar siyasarsu wani muhimmin darasi. Ga shi dai tun a yanzu, munyi babu tsuntsu babu tarko, jam'iyyun da ake gani na Arewa ne, an tattare su an mikawa Bisi Akande da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu kuma dukkan jaridun kasarnan suna kiran Tinubu da sunan Jagoran APC na kasa.
Duk tarihi da kwarewar siyasa da muke takama da su ba su yi mana amfani ba a ganina. Amma na fahimci da yawa wasu a Arewa idansu ya rufe shugabancin kasar kawai suke so ko ta halin kaka, basa yin lissafin me zai je ya dawo. Shi yasa suma basa nuna damuwarsu akan irin yadda jam'iyyar tasu ta ke zagwanyewa a Arewar. Sun manta cewa jarin dan siyasa shi ne jama'a, da me zabe da wanda ake zaba. Amma dai bad'i war haka tuni mai akuwa ta auku, ana jiran 29 ga mayu dan rantsar da shugaban kasa a karo na goma sha shida (16). Allah ya sa muna raye.
YASIR RAMADAN GWALE
22-04-2014
To menene mafita achikin wannan hali da aka samu kai, ta yaya kake gani za a iya ka da jamiyya mai chi?
ReplyDeleteGaskiya Maln Yasir duk abun da ka fada cikin wannan maqala taka haka yake, amma ni shawara ta yakamata mutanen Arewa su farka daga barci don kar ayi musu sakkiyar da ba ruwa
ReplyDelete