Sunday, January 20, 2013

DANGANE DA BATUN KAIWA MAIMARTABA SARKI HARI


DANGANE DA BATUN KAIWA MAIMARTABA SARKI HARI

Akwai wasu tambayoyi da dama da JTF ya kamata su bayar da amsa. Kai hari a unguwar Zoo Road ba wannan bane na farko, shin ya akayi masu aikata wannan aika-aika suke labe a zoo road aka kasa gano maboyarsu? 

Lokacin da aka kaiwa marmairataba Sarki hari rahotanni sun ce babu jimawa JTF suka zo wajen kuma suka yi musayar wuta da 'yan bindigar, shin ya akayi JTF suka bari 'yan bindigar suka sulale basi bi sawunsu ba?

Lokacin da aka kai hari kan ofishin kamfanin Airtel dake Malam Kato Square ananma rahotanni sun tabbatar da yin musayar wuta tsakanin JTF da 'yan bindiga, shin me ya sa ba'a kama ko mutum daya ba, ko kuma gano maboyarsu?

Lokacin da aka kai harin IBB way na kusa da katangar masallacin Idi na cikin gari, nanma rahotanni sunce anyi musayar wuta da JTF da 'yan bindiga, shin anya kuwa wadannan 'yan bindigar da gaske 'yan ta'adda ne, ba rigarsu ake shiga ayi aika-aika da sunansu ba?

A 'yan kwanakin da suka gabata rundunar JTF ta bayyana wasu mutum biyu da ake zargi da kai hari a cikin coci dake barikin sojoji na JAJI, abin mamaki anbayyana wani mutum mai sayar da Kifi ko Doya ina zaton, da wani yaro dan shekara 18 suka sadada suka kai wannan hari, Ina amfanin gogewar jami'an tsaron JTF idan har Yaro karami da mai tallar kifi zasu iya shiga har cikin bariki su kai hari kuma su gudu salin alin, ba a iya ganesu ko kama su ba? Lallai akwai alamar tambaya ga Rundunar JTF!(?)

Sannan a Kano muna kira ga gwamnati da ta sallami dukkan wasu jami'an tsaro dake kan hanya musamman JTF, domin babu abinda suke yi illa cutar da talakawa bayin Allah, dan kasancewarsu akan tituna bata hana 'yan fashi shiga cikin kasuwar WAPA da tsakar rana su kwashi makudan kudi su gudu ba, haka kuma, bata hana kaiwa maimartaba sarki hari da tsakar rana ba. Dan haka basu da wani amfani akan hanyoyin cikin birni.

Tabbas dakarun JTF sune matsalar tsaro yanzu, kuma muddin aka debesu daga kan tituna al'amuran tsaro zasu inganta kamar yadda Shiekh Dr. Ahmad Gumi ya taba bayar da shawara. Kuma mu a wajenmu JTF ababen tuhuma ne akan hare-haren da ake kaiwa.

No comments:

Post a Comment