Sunday, January 27, 2013

KADA KA TABA ZATON DAN SHI'AH YANA KARANTA AL-QUR'ANI



KADA KA TABA ZATON DAN SHI'AH YANA KARANTA AL-QUR'ANI 

'Yan Shi'ah duk inda suke suna kokarin nesanta kansu daga Al-qur'ani mai tsarki, basa karanta shi, kuma basa son mai karanta shi, kai hasalima basu yarda da wannan al-qur'anin da mu Musulmi meka karantawa dare da rana ba. Manzon Allah Salallahu alaihi Wasallam shine cikamakin annabawa wanda ALLAH ya turoshi ga dukkan talikai, kuma ya bashi littafinsa (al-qur'ani) wanda yana shafe zanen dukkan wani littafi da ya gabace shi ne. Al-qu'ani zance ALLAH ne da ya turo ta hannun ManzonSa Salallahu Alaihi Wasallam. Shi kuma Manzon Allah ya karantar da al-majiransa Al-qur'ani wato sahabbai, wadannan sahabbai da wadan da suka biyo bayansu sune wadan da suka yi hidima wa al-qur'ani mai tsarki, har ya kawo garemu.

Saninmu ne cewa Shi'ah Mabiya Dan Saba'i suna matukar nuna kiyayya a bayyane ga wadannan sahabban, Kuma shi wannan Alkur’ani Sahabbai ne su ka zo da shi daga wurin Manzon ALLAH Salallahu Alaihi wasallam su kuma ba su yarda da Sahabbai ba. Daga cikin wadan da sukayi hidimar tattara al-qur'ani dan game shi waje guda musamman Usman Bin Affan shine mutum na uku da shi'ah suke kafirtawa, kuma suke matugar gaba da dukkan zurriyarsa da dangoginsu wato banu Umayya, Idan kaji Dan Shi'ah yana zagin Mu'awiyya ko Yazeed wannan kada ya dameka, domin sun sagi wadan da suka fi su Mu'awiya da yazeedu kima da daraja wato khulafu'r Rasheedun Al-mahdiyyen, haka har aka gangaro kan irinsu Sarkin Musulmi Hajjaju Bin Yusuf wanda tarihi ya tabbatar da cewar yayi matukar hidima wa al-qur'ani, domin shine ya sanya aka wasalce al-qur'ani.

Haka Kuma, a lokacin da Al-qur’aninmu ya ke da ayoyi 6236 Kulini daya daga cikin gumakan shi'ah ya ruwaito a mafi ingancin littafan shi’a daga Abu Abdullahi (Daya daga cikin ma’asumai a gurinsu) cewa Al-qur’anin da Jibrilu ya zo da shi ga Muhammad aya 17000 ne” duba (Alkafi, 2/634). Dan haka, Idan ka ji dan shi’a ya na son ya ja hankalinka ya na musanta abin da littafansu su ka fada kuwa, to, ka sani cewa yana takiyya ne, ita kuma takiyya farilla ce a cikin addininsu kamar sallar farilla (Duba littafin Alkafi na kulini 2/217 da Al’amali na Tusi shafi na 229).

A takaice dai ya zama dole a bayyana wa jama’a cewa, addinin shi’a wani addini ne na jabu wanda makiyan musulunci suka taru suka kitsa shi, sannan suka kutso da shi a cikin musulunci da nufin rusa shi, amma abinda basu sani ba Addini na ALLAH ne, kuma shine zai kare kayansa. Kuma su na jingina kansu ga Ahlul Baiti domin su yaudari jama’ar musulmi. Iyalan gidan Manzon ALLAH Salallahu Alaihi Wasallam bayan kuwa barrantattu ne daga akidun shi’a kamar yadda da dama daga cikin magabatansu suka fada.

Dan haka ya dan uwa kada ka rudu da 'yan Shi'ah basu da wata alaka ko ta kusa ko ta nesa da littafin ALLAH al-qur'ani ko addinin ALLAH. Dan ka sake gane haka bari na baka wani misali. A baya yadda masu yin maulidi suke yi, shine akan yi gadan aba'i ko Mimbari yara suna karatun al-qur'ani da karanta sirar manzo, amma yanzu da shi'ah suka silalo cikn lamarin sai suka dauke hankalin mutane daga yin karatun da suke yi a baya, inda suke zaga gari suna kide-kide da wake-wake na batsa. Kaga daga Karanta al-qur'ani ankoma kada bajujala, alhali Manzon ALLAH Al-qur'ani ya zowa da al'ummarsa da shi. To irin haka ne shi'ah suke yin amfani domin raba mutane da addini da kuma al-qur'ani.

Sunday, January 20, 2013

DANGANE DA BATUN KAIWA MAIMARTABA SARKI HARI


DANGANE DA BATUN KAIWA MAIMARTABA SARKI HARI

Akwai wasu tambayoyi da dama da JTF ya kamata su bayar da amsa. Kai hari a unguwar Zoo Road ba wannan bane na farko, shin ya akayi masu aikata wannan aika-aika suke labe a zoo road aka kasa gano maboyarsu? 

Lokacin da aka kaiwa marmairataba Sarki hari rahotanni sun ce babu jimawa JTF suka zo wajen kuma suka yi musayar wuta da 'yan bindigar, shin ya akayi JTF suka bari 'yan bindigar suka sulale basi bi sawunsu ba?

Lokacin da aka kai hari kan ofishin kamfanin Airtel dake Malam Kato Square ananma rahotanni sun tabbatar da yin musayar wuta tsakanin JTF da 'yan bindiga, shin me ya sa ba'a kama ko mutum daya ba, ko kuma gano maboyarsu?

Lokacin da aka kai harin IBB way na kusa da katangar masallacin Idi na cikin gari, nanma rahotanni sunce anyi musayar wuta da JTF da 'yan bindiga, shin anya kuwa wadannan 'yan bindigar da gaske 'yan ta'adda ne, ba rigarsu ake shiga ayi aika-aika da sunansu ba?

A 'yan kwanakin da suka gabata rundunar JTF ta bayyana wasu mutum biyu da ake zargi da kai hari a cikin coci dake barikin sojoji na JAJI, abin mamaki anbayyana wani mutum mai sayar da Kifi ko Doya ina zaton, da wani yaro dan shekara 18 suka sadada suka kai wannan hari, Ina amfanin gogewar jami'an tsaron JTF idan har Yaro karami da mai tallar kifi zasu iya shiga har cikin bariki su kai hari kuma su gudu salin alin, ba a iya ganesu ko kama su ba? Lallai akwai alamar tambaya ga Rundunar JTF!(?)

Sannan a Kano muna kira ga gwamnati da ta sallami dukkan wasu jami'an tsaro dake kan hanya musamman JTF, domin babu abinda suke yi illa cutar da talakawa bayin Allah, dan kasancewarsu akan tituna bata hana 'yan fashi shiga cikin kasuwar WAPA da tsakar rana su kwashi makudan kudi su gudu ba, haka kuma, bata hana kaiwa maimartaba sarki hari da tsakar rana ba. Dan haka basu da wani amfani akan hanyoyin cikin birni.

Tabbas dakarun JTF sune matsalar tsaro yanzu, kuma muddin aka debesu daga kan tituna al'amuran tsaro zasu inganta kamar yadda Shiekh Dr. Ahmad Gumi ya taba bayar da shawara. Kuma mu a wajenmu JTF ababen tuhuma ne akan hare-haren da ake kaiwa.

Friday, January 18, 2013

ZUWA GA COMR. BILYAMINU ABDULLAHI ADANJI


ZUWA GA COMR. BILYAMINU ABDULLAHI ADANJI

Da sunan Allah mai gamammiyar rahama mai jinkai tsira da amincinSa sukara tabbata ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad salallahu alaihi wasallam da sahabbansa da iyalan gidansa da wadan da suka bi tafarkinsa har yazuwa ranar sakamako, ina shaidawa babu abin bautawa bisa cancanta sai Allah tsarki ya tabbata a gareshi.

Lokacin da na fara kiranka a waya Comrade Bilyaminu Abdullahi Adanji baka dauka ba na sake sannan ka kashe na kuma a karo na uku ka sake kashewa, ko shakka babu Raina yayi matukar baci a wannan lokaci daga baya, nayi tunanin watakila kana cikin wani Uzuri ne da ba zai baka damar amsa waya ba, bayan wani lokaci sai ga kiranka Bilya, kamar bazan dauka ba sai dai kawai na dauka na amsa maka cikin murya mai nuna damuwa nace "MENE" abin da na fara fada sannan kace TUBA NIKE DAN MUTAN GWALE, don Allah kayi hakuri, na amsa maka da cewa babu matsala comrade, ko shakka babu munyi tattaunawa mai tsawo a wannan lokaci kuma mun fahimci juna sosai da gaske, kuma wani abu da bazan manta da shiba shi ne tun a wannan lokaci duk sanda mukayi waya Bilya ka kan kirani da "Danmutan Gwale", kusan a wajenka na fara jin wannan suna, haka kuma duk wanda ya kirani da wannan suna acikin 'yan kungiyar Muryar Talaka to yajine daga bakinka, kuma wannan sunan yabini har gidanmu.

Mun fara hada ido da juna nida kai Bilya lokacin taronmu na farko a shekarar 2010, kuma abin da Bilya ka cemin shi ne "Nice to meet you Danmutan Gwale" nima na amsa maka da "I'm Pleased to meet you my dear comrade", daga nan ka bani wayarka na saka maka ita a chaji, muka ci abinci tare sannan kuma muka shiga cikin hada-hadar al'amuran kungiya, na iya tuna bayan gari ya waye Zaidu Bala da tawagarsa sunyi wanka zasu tafi gurin taro, sun tafi da wuri domin yin shirye-shirye, ina zaune a daki sai ga Bilya ka dawo ka ce dani Danmutan Gwale don Allah ina zan samu Weeklytrust? Na amsa maka da cewa zan taho maka da ita, Bilya ya kalleni yayi murmushi yace sai ka taho danmutan Gwale.

Hakika munsami fahimtar juna sosai da Bilya domin yana turamin sakon tunasarwa kusan duk ranar Juma'a 'karta kwana' kuma nima ina tura maka, ko shakka babu zan dade ina tunawa da kai Comrade Bilyaminu Abdullahi Adanji. Bana manta ranar wata Litinin na shiga makarantar CAS Kano, sai ga Kiran Zaidu Bala a lokacin ba daga dan banji alamar wayata ta yi ruri ba, sai bayan da na fito zan hau dan acaba sai na dauko waya ta na duba lokaci, nan naga kwantaccen kiran Zaidu Bala, nan na mayar masa da kira ina mai bashi hakuri, kawai sai ji nayi Zaidu yayi salati, take gaba na ya fadi domin nasan sakon da alama na rashi ne, amma kuma ban san ko waye ba, cikin murya mai ban tausayi Zaidu Bala ya sanar da ni cewa Abokinmu Comrade Bilya! Nace me ya faru da shi? Nan muryarsa ta sake raurawa ya ce Yasir Allah ya yiwa Bilya rasuwa yana hannun mahaifiyrsa! Hakika na kadu matuka da samun wannan labari, ban mantawa acabar da na kasa hawa kenan tsawon lokaci ina ta salati tare da maida lamari ga Ubangijin talikai.

Bilya kasani wallahi baka yi gaggawa ba kuma inda ka tafi muma muna nan zamu biyoka komai tsawon zamani, ya zuwa lokacin da zamu zo nasan kazama dan gari mu kuma zamu zo a baki tunda karigayemu. Bilya ka tafi a daidai lokacin da kake begen ganin rayuwar 'yan najeriya ta kyautatu dan talaka ya ci moriyar arzikin kasarsa, Hakika ina yima bushara da cewa Allah zai cika maka burinka na ganin an sami kyautatuwar rayuwa a Najeriya. Bilya na dauki alkawarin duk lokacin da na tunaka zanyi maka Addu'ar samun Rahama a wajen mahalicci.

Bilya rahamar Allah ta yalwaci kowa, inayimaka fatan samun wannan rahama kamar yadda nake yiwa kai na fata Allah ya sadamu a Aljanna baki daya. Allah ya jikanka ya gafarta maka.

Wassalamu Alaikum.

Daga Naka Yasir Ramadan Danmutan Gwale

Monday, January 14, 2013

WA YE ZAI HANA GOODLUCK JONATHAN TSAYAWA TAKARA?


Wani zubin idan wadan da suke kiran kansu sune shugabannin 'yan Adawa suka yi magana akan siyasa sai kaga tsiraicin siyasarsu. A kwanakin da suka gabata rahotanni suka ce anga fastocin shugaban kasa a Abuja dauke da bayanan da suke nuna cewa zai sake neman zabe a 2015. Na sausari wata hira da akayi da Farouk Adamu Aliyu a BBC yana cewa su fatansu Allah ya sa shugaban kasa ya sake fitowa neman zabe . . . Ban san wanne shiri suke da shi na tunkudeshi ba. 

Amma Shakka babu babban aikin da ya kamata a dukufa haikan akansa shine ayi dukkan mai yuwuwa wajen hana wannan mutumin tsayawa takara a 2015, kamar yadda aka kashe 3rd Term na Obasanjo a kakar zaben 2007. Bahaushe ya ce "ba a iya yashe rijiya sai anshiga cikinta" ko dai ka shiga ka yaso dukkan dattin da yake cikinta, dan samun tsabtataccen ruwa, ko kuma ka tsaya daga waje kana kwarfe ruwa mai kyau amma dattin yana kasa.

Dan haka, dukkan zaratan yakin siyasa irinsu Atiku Abubakar da suka hana Obasanjo sakat, suka fatattakeshi da shi da 3rd term dinsa, irinsu muke fata su hana wannan mutumin tsayawa takara a 2015. Amma muddin muka ce zamu sake yin irin kasassabar cewa zamu iya kada shi a babban zabe maimaikon zaben fitar da gwani to lashakka Garin Zubar da Ruwan Wankan Yaro to zamu zubar da ruwan har da Yaron, mai makon a zubar da ruwan kawai.

PDP da gaske suke yi akan wannan zabe zasu iya kashe ninkin baninkin abinda suka kashe a 2011 domin samun zabe ko ta halal ko ta haram, kuma sunyi shiri akan hakan, duk wata satoka sa katse da 'yan PDP suke yi karya ce, kuma yaudara ce, domin zabe yana zuwa sai ka tarar bakinsu ya zo daya. Kowa yaga irin yadda aka bada labarin tsamin dangantaka tsakann Atiku Abubakar da Gwamnan Murtala Nyako amma da zaben Nyako ya zo Atiku sai da ya fita ya kira jama'a su zabi Nyako.

Lallai abinda zamu tambayi kawukanmu shine, Shin waye zai hana shugaban kasa sake tsayawa zabe Idan har ya nace akan haka?

Tuesday, January 1, 2013

BOKA SHAIDANIN AL'UMMA


Da can mukanji labarin cewa mata ne suke cin kasuwarsu a wajen bokaye. Sannan babban dalilin da yake kai mata wajen Boka galibi bai wuce wasu batutuwa guda biyu ba, wato KISHIYA da kuma MALLAKAR MIJI, mafiya yawancin mata da suke zuwa wajen boka wannan shine dalilin zuwansu. Bokaye da dama sun halakar da mata da yawa kuma sun kashe aure da yawa akan wannan batu, bayan wannan abunda suke yi, Bokaye sun shahara da FASIKANCI da matan da suke zuwa wajensu, wannan kuma zamu Iya cewa alhaki kuikuyo ne, bayan kasancewarsu Sun sabawa ALLAH da ManzonSa, Sannan sunci amanar Aure da mazajensu. Allah ne kadai yasan adadin mazajen da suka sha jike-jiken bokaye ko suka sha-ruwan tsarkin mata a cikin al'ummarmu, wasu a abinci wasu kuma a cikin abun-sha.

Matan da suke zuwa wajen Bokaye sunyi Imani da maganganunsu sosai, domin suna ganin duk abinda boka ya fada mai faruwa ne. Amma Alhamdulillah, Malamai suna ta yin wa'azi sosai da karantarwa akan hadarin da yake tattare da zuwa wajen Boko da kuma bayanin fushin ALLAH akan mai zuwa wajen Boka, domin Boko Mushiriki ne. Allah ya yafewa wadan da suka tuba suka dena.

Yanzu kuma abin ya sauya salo, Inda bayanai suke nuna cewa Adadin matan da suke zuwa wajen Boka yana raguwa, amma kuma Na mazan da suke zuwa wajen Boka yana karuwa. Yanzu dai masu neman Mulki ta kowacce hanya sune suke daurewa bokaye Gindi suke tsula tsiyarsu ganin dama, satar mutane ya karu alfasha ta karu domin duk wannan yana daga cikin Sharrin Bokaye, domin bayanai sun nuna cewa suna baiwa masu zuwa wajensu umarnin samo wasu sassan jikn dan Adam domin hadawa da su a yi Tsafi, Haka kuma, bokaye kan dora mutane akan mummunar hanyar Yin jima'i da mahaukata, sai kayi mamaki kaga Mahaukaciya da kurtsetsen ciki ita ba Aure ba kuma ita ba Hankali ba balle a tambayeta ina ta samu ciki! Sannan sukan dora mutane akan hanyar yin Luwadi, kamar yadda bayanai suke nunawa duk domin samun Mulki ko direwarsa ko kuma karuwar arziki.

Idan me zuwa wajen Boko yaje wajensa, Bokan ya gaya masa cewa zai zama Shugaban kasa ko gwamna ko shugaban karamar hukuma ko kuma zai kudance sai mutumin yayi Ammana da maganar Bokan. Amma kuma da Bokan zai gaya masa cewa bazaka zama Shugaban kasa ba, amma zaka zama SARKI nan take zai karyata Boka, dan yasan Babu yadda zai a yi ya zama Sarki. Idan da masu zuwan suna amfani da hankali da tunani ko basu san addini ba, nan take zasu karyata Boka ko me yace musu zasu zama, amma da yake Boka wakilin Shaidan ne a tsakanin mutane, kuma Shaidan yayi alkawarin Halakar da al'umma dan haka suke ta samun karin Tagomashi. 

Allah kuma yayi alkawarin cika Wuta da Duwatsu da mutane. Dan haka Bokaye da masu zuwa wajensu muddin basu tuba sun bi Allah ba, muna yi musu albishir da cewa Wutar Jahannama Itace makomar dukkan wani mushuruki. Tir da wannan makoma, muninta yayi yawa. Allah ka tsaremu ka tsare mana Imaninmu. Masu zuwa wajen Bokaye daga cikin mata da maza Allah ka shiryesu.