Mallam Ibrahim Shekarau: Babban mai wa’azi!
Dukkan dangin yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah madaukakin sarki, ubangijin talikai, wanda ya dauki wannan al’umma ya fifita ta akan sauran al’ummatai, ya sanya ta jagora ga sauran mutane don ta shiryar da su ga hanyar cin nasara a rayuwarsu ta duniya da lahira. Tsira da aminci su tabbata ga fiyayyen Manzanni, cikamakin Annabawa, wanda Allah ya fifita shi ya ba shi littafi mafi cika da kamala wanda ya ke shafe-zane ne ga sauran littatafai, Annabi Muhammadu da alayansa da sahabbansa dakuma wadan da sukabi tafarkinsu har ya zuwa ranar sakamko. Dukkan wanda Allah ya shiryar shi ne cikakken shiryayye, haka kuma duk wanda Allah ya batar babu mai iya shiryar da shi. Ina shaidawa babu abin bauta bisa cancanta sai Allah kuma Annabi Muhammadu bawansa ne kuma manzonsa ne.
Al’ummar jihar kano a iya tsawon rayuwarta ta gamu da kalubale iri daban-daban wadan da suka shafi wanzuwarta da ci-gabanta. Hakika jihar Kano kusan itace fitila ga sauran jihohin Arewacin Najeriya idan bakace kasar baki daya ba, Allah ya azurta jihar kano da abubuwa masu yawan gaske, misali sanin kowa ne cewa kano kusan itace cibiyar kasuwanci ta kusan Arewacin Najeriya, wannan ce ma ta sanya kanon ta zama sha-kundum ta fuskar kasuwanci, haka kuma jihar kanon ta zama jiha mai hadiye kowane irin mutum, don haka duk wani mutum daga kowace nahiya yake a kasarnan idan yazo jihar kano takan zama gida a gareshi tare da aminci, kuma yakan gamsu kwarai da irin yadda jihar take, ina zaton wannan baya rasa nasaba da irin yadda mutanan kano suke da karamci da girmama bako da kuma taimakawa masu butar taimako a lokacin da suke nema. Lallai wannan tarbiyya ta mutanan Kano ta dace da koyarwar addinin Islama!
Haka kuma, jihar kano bayan wancan bangare da tayi fice da shi na kasuwanci da saye da sayarwa, kuma jiha ce kusan zakace ta malamai masu wa’azi Allah ya albarkace mu da malamai masu wa’azi da kira zuwaga adalci da daidaito da kuma abaiwa kowane mai hakki hakkinsa. Don haka nema unguwanni a cikin birnin kano suka shahara da karatun ilimi, misali duk wanda yazo kano yake neman ilimin fiqihu za’a ce dashi ya tafi Madabo wajen babbaan malami na Madabo, haka kuma idan ilimin al’qurani yake nema za’a ce ya nufi tudun nufawa, inda zaka sami karatun al’qurani da tajiwidi da kuma tafsirinsa, Allah ya jikan babban Mallami marigayi shiekh Abubakar Ramadan da mahaifinsa bisa irin hidimar da sukayiwa al’qurani. Kusan haka duk bangaren da ka dauka na jihar kano yake!
Bayan haka kuma Jihar kano tayi gwamnoni da yawa kusan tundaga kan marigayi Mallam Audu Bako wanda ya yi dukkan mai yiwuwa wajen ci-gaban jihar duk da kasancewar Audu Bako ba musulmi ba ya taimakawa jihar ta bangarori da daman gaske da suka shafi cigaba da rayuwa da kuma addini. Kusan ana cewa a tarihin jihar kano ba’a taba samun wani gwamnaba kamar shi marigayi Audu Bako ba, haka kuma har aka zo kan Marigari Alh. Muhammadu Abubakar Rimi Allah ya jikansa shi ma a lokacin da ya yi gwamna a jihar kano ya taimakawa al’umma sosai jama’a da dama a wancan lokaci sunyi al’fahari da gwamnatinsa, wannan ce ma ta sanya da Allah ya yi masa rasuwa jama’a da dama a ciki da wajen jihar kanon suka girgiza ainun kasancewar sa jigo a siyasar Arewa da Najeriya.
Bayan haka Allah ya albarkaci jihar kano da salihin gwamna, wato Mallam Ibrahim Shekarau. Kusan babban hadafin da ya kawo Mallam Shekareu gwamnatin Jihar kano shi ne kokarin kulawar da yake da ita ga addini a lokacin da yake ma’aikacin gwamnati a lokacin da gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso ke gwamna a kano a shekarar 1999 zuwa 2003, kusan rahotannin sun nuna cewa gwamntin kano ta wancan lokacin ta muzgunawa mallam Ibrahim Shekarau kasan cewar yana sanya kansa a harkokin da suka shafi addini da kuma gwagwarmayar tabbatar da shari’ar Musulunci wadda ta samo asali daga jihar zamfara, wannan ce ma tasanya ya rasa kujerarsa ta sakataren dun-dun a gwamnatin jihar kano inda aka maidashi makarantar share fagen shiga jami’a ta kano domin ya dauki alli ya cigaba da koyarwa wanda shi ne abin da ya kware akansa tun tasowarsa.
Cikin iko da yassarewa ta ubangiji Allah ya karfafi Mallam Shekarau da fitowa ta karar gwamna a lokaci mai cike da kalubale. Mallam ya yi nasarar zama dantakarar jam’iyyarsa a wancan lokaci bayan andade ana sabatta juyatta. Hakika lokacin da mallam ya zama gwamna abin ya zowa da kowa kusan da bazata domin babu wanda ya taba zaton haka zata kasance, mutumin da aka yiwa kora da hali daga aikin gwamnati, kuma ya tsaya takara da wanda yake da dukkan iko na yaga ya samu nasara akan wannan zabe kasancewar shi ne gwamna kuma yana son zarcewa a karo na biyu yana da cikakken goyon bayan gwamnatin tarayya da kudi da karfin jami’an tsaro, Amma da yake Allah shi ne mai jujjuya al’amura yadda yaso alokacin da ya ga dama, ya bashi Nasara akan abokin hamayyarsa Rabiu Musa kwankwaso.
Kusan, tarihi ya nuna cewa tun da akayi Jihar kano ba’a taba samun gwamna mai hakuri da juriya da yakana da yafiya irin mallam ibrahim shekarau ba, kasan cewar yana da alamu na nuna kishin addini da kuma son addini ya gamu da kalubale mai yawan gaske daga masu hamayya da shi ciki da wajen jihar kano, da yawa daga cikin mutanan da sukayi aiki da Mallam Ibarhim shekarau sunga baikensa don da dama suna zarginsa cewa yawan hakurinsa ya yi yawa, domin yana gwamna da dukkan irin karfi da yake da shi na mulki aka sami wani mara tarbiyya inda ya buga takarda da hoton malamin gwamnan da iyalinsa da kalamai na batanci wanda wannan ya wuce hamayyar siyasa ya shafi taba mutuntaka amma malamin yace ya yafe, wanda ba karamin mai imani ne zai iya hakan ba a lokacin da yake da dukkan ikon daukar duk matakin da yaga dama. Daman Allah yace kuyi bushara ga masu hakuri!
Mallam Ibarhim Shekarau ya yi abubuwa da daman gaske na tabbatar da wanzuwar shari’ar musulunci a jihar kano wanda itace jigon hawansa kujerar gwamnan kano, musamman sanyawa da yayi majalisa tayi dokar kafa hukumar shari’ah ta jihar kano da kuma hukumomin da suka hada da zakka da hubusi da hukumar Hizba da kuma hukumar Adaidaita Sahu da zauren sulhu, da hukumar karbar koke-koke da korafi, wanda ya dauko hazikan Mutum ya sanya a wadan nan hukumomi irinsu mallam Bala Muhammad a matsayin babban darakta na Adaidaita Sahu tare da mai Martaba Sarkin Kano a matsayin jagora da kuma shi mai girma gwamna a matsayin babban limami, da mutane irinsu Mallam Ibrahim Mu’azzam mai Bushura da Proffessor Sani Zaharaddeen da Proffessor Ibrahim, da kuma mutane irinsu Shiekh Dr. Bashir Aliyu Umar da Mallam Umar Sani Fagge a hukumar shari’a. Kasan cewar jama’a da gaggawa suke da son kasan cewar abu nan da nan wasu da dama sun ga baiken malam akan al’amuran shari’a, domin da yawa sun zargeshi da cewa yana jan kafa ko kuma tafiyar hawainiya dangane da al’amuran shari’a domin an dauki lokaci kafin duk wadan can hukumomi suka sami cikakken ‘yanci, amma cikin yassarewar Allah mallam ya yi iyakar yinsa akan tabbatuwar al’amura da kuma inganta harkar tafida shari’ar Musulinci a jihar kano, wannan kam jama’a sun shaida kuma Allah ma ya shaida.
Mallam Ibarhim shekarau: babban mai wa’azi kusan kamar yadda kowa ya karanta shi ne taken wannan rubutu. A hakikanin gaskiya na yi wannan rubutune domin yin martani ga Editan jaridar nan mara farin jini wato Desert Herald wanda Mr. Tukur Mamu yakewa babban edita. Wannan jarida dai ana bugata ne kamar sauran jaridun Nijeriya, wato bisa dogaro da sashi na 39 karamin kashi na 1 cikin baka wanda ya baiwa ‘yan kasa dama. Ita dai wannan jarida kusan ana buga tane dukkan mako a jihar kaduna, amma bisa ga dukkan alamu basu da wani aiki da suka sanya a gaba illa kazafi da kage da yarfe ga mutanan kirki irinsu Mallam Ibrahim Shekarau.
Domin a lokacin da mallam Ibrahim Shekarau ya fuskanci kalubale mafi girma a lokacin da yake neman sake komawa kujerar gwamnatin jihar kano aka yiwa fitaccen Malamin Sunnah wanda sautinsa ya daga ya yi sama yana kururuwa da bin sunnar Manzon Allah sallalahu Alaihi wasallam wato Marigayi Sheikh Ja’afar Bin Mahmood Bin Adam kisan gilla a masallacinsa na juma’a da ke Daurayi a cikin karamar hukumar Gwale a yayin da yake yiwa mutane jagorancin sallar Asubashi sallar da Allah yace munafukai basa yinta, kisan marigayi sheikh Jafar yazo kwana daya kafin babban zaben gwamna na 2007 a jihar kano, kuma kwana daya kafin cikar alkawarin da sheikh jafar ya dauka na haskawa al’umma mutumin da ya kamata su zaba, Allah ya jikan mallam ya kai rahama kabarinsa, kusan da yawan masu hasashe sun dauka cewa daga wannan lokaci jihar kano zata yamutse, amma cikin taimakon Allah da yassarewarsa hakan baici nasaraba, Malaman sunnah irinsu shiekh Dr. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo sunyi iyakar yinsu wajen kwantar da hankalin dalibai da kuma almajirai da abokan marigayi sheikh Jafar din.
Bisa ga adalci da sanin ya kamata, a wannan lokaci idan akwai abinda Mallam Ibrahim Shekarau ya ke so to kuwa bai wuce zaman lafiya ba, domin irin yadda ya sha da kyar da jibin goshi a hannun hukumar EFCC bisa zargin da ake yi masa na al’mundahana da kudin taki wanda daga karshe dai akace bashida laifi, abinda Bahaushe yake cewa ciki da gaskiya wuka bata hudashi, haka nan batare da magauta sun so ba Allah ya sake baiwa Mallam Ibarhim shekarau gwamnan kano a karo na biyu, Allah mai yadda ya so.
Kwatsam bayan wasu ‘yan lokuta, sai ga wani shafi a internet da ake kira da sunan SAHARA REPORTERS sun buga wani labari cewa gwamnan kano Mallam Ibrahim Shekarau yana da hannu dumu-dumu wajen kisan marigayi sheikh Jafar Adam kano, wanda ita wannan jarida ta Desert Herald tayi ta yamadidi da labarin cewar ai lallai Mallam Ibrahim Shekarau gwamnan Kano yana da hannu wajen kisan Sheikh, babu irin kalaman da basu yi ba na batanci akan malamin gwamnan, babu jimawa da bullar wannan labari Gwamnan kano a wancan lokaci Mallam Ibarahim Shekarau ya fito kafar watsa labarai ta jihar kano ya yiwa al’umma bayanin cewa wannan abinda aka fada akansa ba gaskiya bane anyi kawai domin bata masa suna, kuma da yake dalibai da malaman sunnah ba Gidadawa bane basu karbi wannan labari da ya fito daga sahara reporters ba domin babu wani abu da zai iya nuna maka gaskiyar labarin abu a duniyar gizo kowa na iya shiga ya rubuta baragadar da yake so.
Kusan tun daga wannan lokaci shi wannan mutum Mr.Tukur Mamu bashi da wani aiki a cikin jaridarsa illa bata sunan mallam Ibrahim shekarau, ta hanyar buga labarai na kanzon kurege a kansa acikin jaraidar tasa da haryanzu mafi yawa daga cikin al’ummar kasarnan basuma san da zaman jaridar ba zance da ake, yana yawan yin maganganu akan cewa Mallam Ibrahim Shekarau mutumin da ake zargi da kisan Sheikh Jafar Adan Kano, daga cikin irin karyar da wannan jarida ta ke bugawa harda buga hoton wani katafaren gida a kano wanda shaidu suka nuna cewa mallakin fitaccen attajirin nan ne wato Alhaji Bashir Tofa cewa wannan gidan Mallam Ibrahim Shekarau ne ya mallakeshi amma ya zuwa yanzu gaskiyar ko gidan wane ta tabbata, domin mallam yana cikin gidansa na Mundubawa Avenue yana watayawa da iyalansa kamar kowane mai iyali.
A matsayina na daya daga cikin daliban marigayi Shiekh jafar Adam kuma na kusa da shi, haryanzu ban san wani daga cikin Iyalai ko abokai ko kuma almajirai na hakika da suke zargin Mallam Ibarahim Shekarau da kisan Sheikh Jafar ba, tambaya anan itace don me Mr. Tukur Mamu yake irin wadan can kalamai akan cewa ana zargin mallam shekarau da kisan sheikh Jafar Adam? Idan har Mr. Mamu yana jin cewar shi dalibin Sheikh jafar ne kuma yana zargin Mallam Shekarau da hannu wajen kisan Sa me yasa bai kaishi kotu ba tunda doka ta bashi dama idan har nuna kishi yake ga jinin Sheikh Jafar, ai yanzu Mallam Ibarahim Shekarau mutumne kamar kowa bashi da kariyar sashi na 308 da ya hana gwamna gurfana a gaban kowane irin kwamitin bincike ko kotu. Ko kuwa yana son ya yi amfani da wannan ne kawai domin cimma wata boyayyar manufa tasa?
Kasan cewar yanzu haka gwamnatin kano ta hamayya ce ga Mallam Ibrahim Shekarau me ya sanya shi Mr. Mamu ba zai matsa musu lamba ba wajen fito da gaskiyar binciken wadan da suka kashe shiekh jafar? Idan har yana son Sheikh Jafar din da gaske, na tabbata idan da mallam shekarau yana da hannu ko masaniya wajen kisan Sheikh jafar Adam da wallahi bazai sha ba a hannun wannan gwamnati Engnr. Rabiu Kwankwaso. Don haka yanzu ta bayyana cewa da Mr. Tukur Mamu da jardarsa marar farinjin ta Desret Herald cikakkun makaryata ne sannan kuma har ila yau ina da tambaya a garesu, Mecece alakar ita wannan jarida da shafin Sahara Reporters? Kuma su waye suke gudanar da shi wannan shafi na Sahara Reporters? Ya kamata shi mista Mamu ya zo ya bamu amsar wadan nan tambayoyi, idan ba haka ba zamu cigaba da kirga wannan jarida a matsayin jaridar ‘yan yaudara masu bata sunan mutanaan kirki.
Idan zan iya tunawa a lokacin da shi mallam Ibrahim Shekarau yake gwamnan kano, akwai daya daga cikin mashawartansa Mallam Suleman Uba Gaya ya yi cikakkun bayanai ta shafukan Jaridun Aminiya da kuma Leadership Hausa cewa babban dalilin da ya sanya shi Mista Mamu yake wannan batanci ko Blackmailing da turanci shi ne saboda gwamnatin mallam taki baiwa jaridar kwangilar buge-buge tallanta ko kuma yin amfani da jaridar a matsayin hanyar da gwamnatin zata rinka bada sanarwa. Haka kuma shima mai magana da yawun gwamnan Yobe Abdullahi Bego ya yi makamancin wancan ikirari da suleman Uba gaya ya yi na cewa yana amfani da jaridarsa wajen bata sunan gwamnatin Gwamna Ibrahim Geidam, kuma tabbas biri ya yi kama da mutum.
Don akwanakin baya munji jaridar taje kasar Chadi inda ta karrama shugaba Idriss Deby Itanou. Wannan ya nuna cewa kawai neman kudi sukeyi domin me Shugaban chadi ya yi har da zasu karramashi, ko kuwa kawai abin nan da ake cewa reza yanki bakauye kasancewar Shugaba Idriss Daby ba turanci yake jiba don haka bazai iya fahimtar cewa ita jaridar Desert Herald ba wata tsiya ba ce a Najeriya domin idan da zaka tambayi masu karanta jarida cikin mutum 50 da kyar ka sami mutum 3 da sukan da ita.
Don haka Mr. Mamu ya sani mu agurinmu Mallam Ibrahim Shekarau babban mai wa’azi ne domin a atarihi ba’a taba samun gwaman nan da yake wa’azi duk karshen Ramadan a kano ba kamar Mallam Ibrahim Shekarau Sardaunan kano kuma wazirin raya kasar Nupe. Ina kuma kira ga shi shi Tukur mamu da yaje Masallacin Juma’a na Al’furqan dake Alu Avenue yaga waye Mallam Ibrahim Shekarau yaga yadda Allah yake kara daukakashi a kullum, daman haka gaskiya ta ke idan ka tsaya akanta Allah sai ya sanya soyuwarka a zukatan al’ummar da ke tare da kai.
Daga karshe, ina addu’a Allah ya taimakin Mai Girma Sardaunan kano mallam Ibrahim Shekarau ya kara masa daukaka kuma ya bashi nasara akan makiya da mahassada, Shi kuma Mr. Tukur mamu Allah ya shiryeshi ya dena hassada da kyashi akan ni’imar da Allah ya yiwa mutanan kirki. Allah ya shiryemu baki daya.
Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@hotmail.com
http://yasirramadangwale.blogsport.com
No comments:
Post a Comment