Sunday, November 27, 2011

Shin ko Gaddafi Ya Tafi Da Mafarkinsa Na Raba Najeriya?

Kanar mu’ammar Ghaddafi kusan shine shugaba mafi da dewa a duniya a wannan zamani. Gaddafi kusan ya shafe shekuru sama da arba’in yana mulki ko kuma shugabancin kasar Libya kusan a wannan karnin babu wani shugaba da ya shafe irin wadan nan shekaru yana shugabanci.

Dukkan mutumin da ya san abu mafi tsawon lokaci zai fahimce shi sosai. Kamar yadda Gaddafi ya shafe lokaci lokaci mai tsawo yana shugabanci za ayi masa zaton cewa yasan shi ciki da bai, wato za ayi masa zaton cewa yasan dukkan wani abu da shugaba ya kamata ya yi wajen kyautatawa al’ummarsa haka kuma yasan dukkan wani abu da zai tsanantawa al’umma.

Hakika idan ana batun shugabanci na adalci Gaddafi ya kamanta. Kanal Gaddafi da ya shafe tsawon lokaci yana shugabancin kasarsa ta Libiya kuma ya kyautatawa al’ummarsa daidai gwargwado. Misali Gaddafi yana daya daga cikin shugabanni kalilan da suka damu da jindadi da walwalar al’ummarsu. Muhimmin aikin da gaddafi ya yiwa Libiyawa shi ne irin yadda ya samar musu da ruwan dadi sakamakon kasar libiya tana kewaye da tekun Mediterranean sea daga Arewacin kasar da kuma Arewa maso yammacin kasar kuma gashi kasace maicike da sahara daga yamma da kuma kudu da gabas wannan ruwa na teku dake arewa da kuma Arewa maso gabas ruwa ne mai gishiri da kuma zartsi, haka gaddafi ya keto daruwan dadi daga gabar tekun Tyrrhenian sea wanda ke daura da tsibirin Malta wanda ke gab da kasashen Turai ta yamma.

Bayaga wannan kokari da gaddafi yayi na samarwa da mutanansa da ruwa mai dadi ko kuma wanda aka rage gishirinsa da kaso mai yawa. Sannan gaddafi ya samarwa da mutanansa da ilimi kyauta tundaga matakin farko na firamare har ya zuwa jami’a. ba wai Libiyawa ba kawai harma da mutanan Afurka da kasashen larabawa matalauta kamar Siriya da Yaman Da palasdinu. Haka kuma Gaddafi ya samarwa da mutanasa harkar lafiya kyauta da kuma kayan masarufi kamar kyauta.

Sannan kuma Gaddafi yana taimakawa da marasa galihu da albashi indai ‘yan libiya ne kuma ko ina suke a duniya, haka kuma yace duk wani abu da dan libiya libiya zai saya kamar mota da kayan kere-kere na zamani zai biya rabin kudin ne gwamnati zata biya masa rabi. Haka kuma maganar gidan zama bakada bukatar ka gina ko kasayi gidan idan kana libiya gwamnatin gaddafi zata baka gida har tsawon rayuwarka kuma ta baiwa ‘ya ‘yanka.

Bayan haka, Gaddafi ya taimakawa kasashen Afurka matalauta da kudade masu dimbin yawa, wani abin burgewa dangane da Gaddafi shi ne cewa ba ataba samunsa ko zarginsa da wawure dukiyar kasarsa ba, ko shakka babu Gaddafi ba barawo bane, kusan shi ne shugaba daga cikin larabawa da ya fara kirkiro wata hukuma mai suna “ min aina laka haza” ma’ana ta in aka samu wannan kamar kace wani dan karamin hisabi kuma wannan anayiwa duk dan libiya idan karshen shekara ta zo kuma ana farawa daga shugaban kasa ne zuwa kasa.

Sai dai kash gaddafi daga karshen rayuwarsa ya ringa wasu abubuwa da suka saba da yadda aka sanshi. Inda ya ringa taimakon kungiyoyin tarzoma da tada hankali a kasashen larabawa da Afurka wannan ta soma janyo lalacewar dangantaka tsakaninsa da kasashen Turai da Amerika. Gaddafi yay i ta kokarin hade kan kasashen Larabawa a matsayin wata kasa guda a karkashin shugabancinsa sai dai hakarsa bata cimma ruwa ba inada mafi yawan kasashen larabawa suka ki amincewa da shi akan wannan batu. Wannan tasa ya watsar da wannan batu nasa ya koma batun kafa kasar Afurka kwaya daya karkashin shugabancinsa wannan ma dai bata samu ba ga Gaddafi,

Mafiya yawan mutane sunyiwa Gaddafi gurguwar fahimta. Da yawan mutane musamman musulmi daga yankin Afurka ta yamma suna kallon Gaddafi a matsayin wani shugaba mai kishin addini wanda zance na gaskiya ba mai kishin addini bane kalamansa da ayyukansa suka nuna haka, sai dai Gaddafi yana da matukar kishin larabawa da kasashen larabawa, domin Gaddafi yay i kaurin suna wajen nuna soyayya ga kasar Palasdinu, kuma kullum batunsa shi ne sai munkwato kasarmu ta al’ummar larabawa daga hannun yahudawa abokan gaba bawai kasarmu ta mu Musulmi yake cewa ba.

Gaddafi mutum ne da ya jingine hukuncin Allah. Kasan cewar libiyawa suna son tafiyar da kasarsu bisa tsarin islama amma Gaddafi yace sam bazai tafiyarda gwamnati bisa tsarin musulunci ba saidai zai tafiyar da gwamnatinsa bisa tsarin wani kundi da ya kira da suna “Green Book” tsarine da akaso anuna addini amma duk wani tsari na Allah babu shi cikin wannan tsari ya zama shiba alqur’ani ba kuma shi ba constitution ba. Wallahul musta’an duk da wannan zuma da gaddafi yake baiwa mutanensa sunfi son tsarin Allah da Manzonsa.

Daga baya mai aukuwa ta auku ga shugaba kanar mu’ammar Gaddafi. Inda mafi yawan mutanan da aka Haifa karkashin mulkinsa suka bijire masa da taimakon kasashen Turai da Amerika da NATO sakamakon wani juyin juya hali da ya bulla a kasashen larabawa a wannan lokaci.

Gaddafi ya yi kira da a raba kasar Najeriya zuwa kasashe guda biyu. Wato kasar Musulmi da ta Kirista Musulmi masu kasa daga yankin Arewacin Najeriya mai hedikwata a Abuja da kuma kasar kirista daga kudunancin Najeriya mai hedikwata a Lagas, kamar yadda ya faru tsakanin kasar sudan mai hedi kwata a khartoum da kuma sudan ta kudu mai hedikwata a Juva. Wannan ta fusata shuwagabannin Najeriya inda shugaban Majalisar dattawa ya kirashi da cewa “Mahaukaci ne”. wanda wannan maganar ta marigayi Gaddafi abar kallo ce da kuma duba na tsanaki.

Ko shakka babu alamu sun nuna cewa da wahala kasar Najeriya ta cigaba da zama tsintsiya madaurinki guda. Domin yadda muke a yanzu ko shakka babu ana kwarar wani bangare wanda wannan shi ne babban abin da ya haifar da kasar sudan ta kudu wato rashin adalci, kuma idan ba ayi hankali ba maganar Gaddafi zata tabbata,domin shugaban kasa da yafi kamata ya nuna adalci ga al’ummarsa shi ne mutum na farko da ke nuna bangaranci da fifiko ga wani bangare da kuma wasu mutane.

Tabbas maganar Gaddafi dan gane da raba Najeriya bawai kawai da ka ya yita ba. Domin ya shafe kusan tsawon sama da shekara arba’in yana kallon Najeriya watakila lokacin da yake shugaban kasa a libiya shugaban Najeriya na yanzu yana makarantar sakandare ko firamare to kaga babu yadda za ayi tunani da hange nasu yazo daya. Allah masani, lokaci ne kawai zai tabbatar mana cewa shin maganar Gaddafi dangane da Najeriya zata rabu ko kuwa zata ci gabada zama kasa daya al’umma biyu.


No comments:

Post a Comment