Sunday, November 27, 2011

Rikicin Kabilanci da na Addini a Najeriya: Ina Mafita

Najeriya kasace da ta fi kowacce kasa yawan jama'a a nahiyar Afrika kuma kasace mai kabilu daban daban ga kuma yaruka masu yawan gaske kusan kididdiga ta nuna akwai yaruka sama da 250 a Najeriya, kamu Allah ya albarkaci Najeriya da Dumbin arzikin da kusan baitaba baiwa wata kasa aduniya ba kamar yadda masana suke fada, Haka kuma najeriya tana da addinin musulunci da kirista da kuma masu addinin gargajiya.

Duk dan Najeriya ba zabinsa bane ya kasance dan asalin wannan kasar, haka Allah yaso ya hada kura da akuya agarke daya haka Allah ya liccemu kuma ya hadamu a wannan guri da ake kira Najeriya bada zabin mu ba, kuma yayimu kabilu daban daban, wani Bahaushe wani Inyamuri wani kuma bayerabe haka kuma wani dogo wani gajere wani baki wani fari wani mummuna wani kuwa idan ka ganshi kamar shi yayi kansa, Allah mai yadda yaso, hakadai Allah ya yimu bisa zabinsa kusan da za'a tambayi dan Najeriya me ye zabinsa watakila da ba nan zaice ba. mukam muna yiwa Allah godiya da muka kasance 'yan Najeriya kuma masu kishin kasarsu kamar yadda kowanne mahaluki aduniya yake kishin kasarsa, misali duk dan kasar Mesedoniya baiyarda da cewa wata kasa tafi kasar sa ba, domin kuwa tun a makaranta duk yaro ana gaya masa daga Allah sai mesedoniya don haka ne suke alfahari da kasarsu da kuma yarensu.

Yawaitar rikicin Addini dana kabilanci a najeriya, mu duba rikicin kafancan a jihar kaduna wanda akayi ashekarar 1987, mutum nawa ne suka rasa rayukansu da dukiyoyinsu basuji basu gani ba, aka maida wasu marayu wasu mata kuwa suka koma zawarawa.

Sannan mutum nawane wadan da aka hallaka sunaji suna gani saboda kabilanci a Idiyaraba a shekarar 2002, Haka kuma mutum nawa aka kona aka lalata musu dukiyoyinsu aka raba iyaye da 'ya 'yansu a shagamu ashekarar 2001 badon komai ba sai kawai don kabilanci shin su sukayi kansu ne? Mu kalli yadda matasa dauke da makamai suka dirarwa kauyen agbohol a jihar bunuwai ashekarar 2004 wai suna ikirarin su mutanen ba 'yan asalin kauyen bane kawai sabida bambamcin kabila.

An kashe mutane da yawa kana kuma aka jikkata wasu da dama arikicin zangon kataf a shekarar 1992 inda aka yiwa musulmi da kirsta

kisan gilla da kisan wulakanci basuji basu gani ba kawai don biyan bukatar wasu. Sannan mu kalli abin da yafaru a yankin kudu maso

kudu tsakanin kabilun Ijow da itsekiri aka kashe yara da mata da basuji basu gani ba, badon komai ba sai don bambancin kabila

ya kamata mugane kowannenmu bazabinsa bane ya kasance dan kabilar da yake.

Haka kuma mu duba irin yadda rikicin jos wato jihar pilato yaki ci yaki cinyewa tsakanin musulmi da kirista inda yake neman zama

wani dan karamin yakin dumiyar Najeriya, kusan wannan rikici yafaru kashi kashi kusan yafi cikin yatsu amma har yanzu wutar wannan

rikici bata lafa ba, Kusan tundaga shekarar 2001 jihar pilato tayi bankwana da zaman lafiya, har kawo yau wannan rikici bai lafa ba.

A shekarar 2004 rikicin addini ya fara aukuwa a kauyen yalwa dake cikin karamar hukumar Shandam wanda sanadiyar wannan rikici ne

ya watsu zuwa wasu garu ruwa makwabta irinsu karamar hukumar lantan ta arewa da ta kudu da ma wani yanki na Wase wanda

sanadiyar haka ne wannan rikici ya watsu har zuwa sauran jihohi makwabta irinsu kaduna da kano inda aka halaka dukiya mai dumbin yawa

kuma aka kashe rayuka masu yawan gaske kuma aka jikkata wasu, kusan shi rikici masominsa aka sani amma ba'a san karshensa ba,

kusan wannan rikicin da ya samo asali daga kauen yalwan shandam shi ne ya sake barkewa ashekarar 2006 inda a sanadiyar wannan rikicine

dubban jama'a suka rasa rayukansu da dukiyoyinsu.

Kusan rikicin da yafi kowanne kazanta shi ne wanda ya faru a shekarar 2008 wanda ya samo asali daga zaben karamar hukumar Jos ta arewa,

inda daga rikicin zabe ya koma na addini kuma kusan wannan rikici da ya auku shiryayye ne domin ko shakka babu musulmi suke da rinjaye

a wannan karamar hukuma ta jos ta arewa kuma inda zakasan abin da makirci ya mai karatu hukuma sai ta sanya ranar zaben ta kasance ranar

Alhamis inda za'a wayi gari juma'a ranar da musulmi ke fitowa sallar juma'a inda aka hallaka musulmin da basuji ba basu ganiba inda asanadiyar

wannan rikicine 'yan sanda suka binne gawarwaki 426 a rami daya bayaga biliyoyin dukiyar da aka rasa da kuam dubban motocin da aka kona

bayan wannan wani rikicin ya sake barkewa a Dutse-Uku duk a karamar hukumar jos ta arewa, a sakamakon wani mutum da yazo maida

gidan da aka kruguza masa kiristoci suka farmasa a wani kaulin kuma sakamakon wasan kwallo da wasu musulmi sukayi a harabar wata coci,

wallahu a'alam, baya ga wannan rikici na watan nuwamba a wannan shekarar ta 2008 wani rikicin ya sake barkewa wanda kuma ya kazanta inda 'yan sanda sukace sun kirga gawarwaki 362 a yashe akan titi, haka kuma anyi ta ganin wasu gawarwakin musamman a garin Digo na Hauwa inda akaringa ganin gawa acikin rijiya da shadda da gurare marasa kyan gani. Haka kuma babu wanda zai iya kiyasta adadadin mutanen da suka rasa ransu a karamar hukumar Riyom da kuma Dogo na Hauwa.

Baya ga wannan kuma ga kisan mummuke da akeyi da kuma dauki day-day aciki da waje garin jos inda zaka ga wani akwata wani rijiya wani

ma yashe kan titi. Abin tambaya anan shine me yasa a yankin jos ta arewa ne wannan rikici yafi faruwa. Anan ina ga ya kamata gwamnati tayi

duba na tsanaki dan gane da abin da yafi dacewa da jihar pilato idan rabata shi ne mafi alkhairi to babu jira abinda ya kamat ayi kenan.

Kuma me yasa najeriya tayi kaurin suna wajen rikicin addini da na kabilanci shin mukadai ne kabilu da yawa mukadaine muke da bambancin Addini.

Malamai sun sha yin wa'azi a masallatai, haka kuma acoci anshayin irin wannan wa'azi cewaDuk Addinin Musulunci dana kirista babu wanda yake umarni da kisan ran da bataji bata gani ba. Kuma musanifa Dukiyoyin mu ne muke halakawa wanda mukayi wahala wajen tarawa, tayaya muna halaka dukiyoyinmu da kanmu kuma zamu kirawo masu saka jari kasarmu shin su mahaukata ne basa sin dukiya ne.

Mafita shi ne muji tsoron Allah mu koma ga Allah duka musulmi da kirista, kuma yaka mata gwamnati ta hada kai da kungiyoyi irinsu spreme council

for Sharia in Nigeria da Jama'atu nasrul islam da crristian Association of Nigeria da kuma masu rike da sarautu da malaman addini wajen kawo

karshen wannan rikici. Allah ya zaunar da kasarmu lafiya ya bamu karuwar arziki da wadata Amin.

Yasir Ramadan Gwale

Shugaban kungiyar muryar Talakawan

Najeriya reshen jihar kano.

07028690570

Shin ko Gaddafi Ya Tafi Da Mafarkinsa Na Raba Najeriya?

Kanar mu’ammar Ghaddafi kusan shine shugaba mafi da dewa a duniya a wannan zamani. Gaddafi kusan ya shafe shekuru sama da arba’in yana mulki ko kuma shugabancin kasar Libya kusan a wannan karnin babu wani shugaba da ya shafe irin wadan nan shekaru yana shugabanci.

Dukkan mutumin da ya san abu mafi tsawon lokaci zai fahimce shi sosai. Kamar yadda Gaddafi ya shafe lokaci lokaci mai tsawo yana shugabanci za ayi masa zaton cewa yasan shi ciki da bai, wato za ayi masa zaton cewa yasan dukkan wani abu da shugaba ya kamata ya yi wajen kyautatawa al’ummarsa haka kuma yasan dukkan wani abu da zai tsanantawa al’umma.

Hakika idan ana batun shugabanci na adalci Gaddafi ya kamanta. Kanal Gaddafi da ya shafe tsawon lokaci yana shugabancin kasarsa ta Libiya kuma ya kyautatawa al’ummarsa daidai gwargwado. Misali Gaddafi yana daya daga cikin shugabanni kalilan da suka damu da jindadi da walwalar al’ummarsu. Muhimmin aikin da gaddafi ya yiwa Libiyawa shi ne irin yadda ya samar musu da ruwan dadi sakamakon kasar libiya tana kewaye da tekun Mediterranean sea daga Arewacin kasar da kuma Arewa maso yammacin kasar kuma gashi kasace maicike da sahara daga yamma da kuma kudu da gabas wannan ruwa na teku dake arewa da kuma Arewa maso gabas ruwa ne mai gishiri da kuma zartsi, haka gaddafi ya keto daruwan dadi daga gabar tekun Tyrrhenian sea wanda ke daura da tsibirin Malta wanda ke gab da kasashen Turai ta yamma.

Bayaga wannan kokari da gaddafi yayi na samarwa da mutanansa da ruwa mai dadi ko kuma wanda aka rage gishirinsa da kaso mai yawa. Sannan gaddafi ya samarwa da mutanansa da ilimi kyauta tundaga matakin farko na firamare har ya zuwa jami’a. ba wai Libiyawa ba kawai harma da mutanan Afurka da kasashen larabawa matalauta kamar Siriya da Yaman Da palasdinu. Haka kuma Gaddafi ya samarwa da mutanasa harkar lafiya kyauta da kuma kayan masarufi kamar kyauta.

Sannan kuma Gaddafi yana taimakawa da marasa galihu da albashi indai ‘yan libiya ne kuma ko ina suke a duniya, haka kuma yace duk wani abu da dan libiya libiya zai saya kamar mota da kayan kere-kere na zamani zai biya rabin kudin ne gwamnati zata biya masa rabi. Haka kuma maganar gidan zama bakada bukatar ka gina ko kasayi gidan idan kana libiya gwamnatin gaddafi zata baka gida har tsawon rayuwarka kuma ta baiwa ‘ya ‘yanka.

Bayan haka, Gaddafi ya taimakawa kasashen Afurka matalauta da kudade masu dimbin yawa, wani abin burgewa dangane da Gaddafi shi ne cewa ba ataba samunsa ko zarginsa da wawure dukiyar kasarsa ba, ko shakka babu Gaddafi ba barawo bane, kusan shi ne shugaba daga cikin larabawa da ya fara kirkiro wata hukuma mai suna “ min aina laka haza” ma’ana ta in aka samu wannan kamar kace wani dan karamin hisabi kuma wannan anayiwa duk dan libiya idan karshen shekara ta zo kuma ana farawa daga shugaban kasa ne zuwa kasa.

Sai dai kash gaddafi daga karshen rayuwarsa ya ringa wasu abubuwa da suka saba da yadda aka sanshi. Inda ya ringa taimakon kungiyoyin tarzoma da tada hankali a kasashen larabawa da Afurka wannan ta soma janyo lalacewar dangantaka tsakaninsa da kasashen Turai da Amerika. Gaddafi yay i ta kokarin hade kan kasashen Larabawa a matsayin wata kasa guda a karkashin shugabancinsa sai dai hakarsa bata cimma ruwa ba inada mafi yawan kasashen larabawa suka ki amincewa da shi akan wannan batu. Wannan tasa ya watsar da wannan batu nasa ya koma batun kafa kasar Afurka kwaya daya karkashin shugabancinsa wannan ma dai bata samu ba ga Gaddafi,

Mafiya yawan mutane sunyiwa Gaddafi gurguwar fahimta. Da yawan mutane musamman musulmi daga yankin Afurka ta yamma suna kallon Gaddafi a matsayin wani shugaba mai kishin addini wanda zance na gaskiya ba mai kishin addini bane kalamansa da ayyukansa suka nuna haka, sai dai Gaddafi yana da matukar kishin larabawa da kasashen larabawa, domin Gaddafi yay i kaurin suna wajen nuna soyayya ga kasar Palasdinu, kuma kullum batunsa shi ne sai munkwato kasarmu ta al’ummar larabawa daga hannun yahudawa abokan gaba bawai kasarmu ta mu Musulmi yake cewa ba.

Gaddafi mutum ne da ya jingine hukuncin Allah. Kasan cewar libiyawa suna son tafiyar da kasarsu bisa tsarin islama amma Gaddafi yace sam bazai tafiyarda gwamnati bisa tsarin musulunci ba saidai zai tafiyar da gwamnatinsa bisa tsarin wani kundi da ya kira da suna “Green Book” tsarine da akaso anuna addini amma duk wani tsari na Allah babu shi cikin wannan tsari ya zama shiba alqur’ani ba kuma shi ba constitution ba. Wallahul musta’an duk da wannan zuma da gaddafi yake baiwa mutanensa sunfi son tsarin Allah da Manzonsa.

Daga baya mai aukuwa ta auku ga shugaba kanar mu’ammar Gaddafi. Inda mafi yawan mutanan da aka Haifa karkashin mulkinsa suka bijire masa da taimakon kasashen Turai da Amerika da NATO sakamakon wani juyin juya hali da ya bulla a kasashen larabawa a wannan lokaci.

Gaddafi ya yi kira da a raba kasar Najeriya zuwa kasashe guda biyu. Wato kasar Musulmi da ta Kirista Musulmi masu kasa daga yankin Arewacin Najeriya mai hedikwata a Abuja da kuma kasar kirista daga kudunancin Najeriya mai hedikwata a Lagas, kamar yadda ya faru tsakanin kasar sudan mai hedi kwata a khartoum da kuma sudan ta kudu mai hedikwata a Juva. Wannan ta fusata shuwagabannin Najeriya inda shugaban Majalisar dattawa ya kirashi da cewa “Mahaukaci ne”. wanda wannan maganar ta marigayi Gaddafi abar kallo ce da kuma duba na tsanaki.

Ko shakka babu alamu sun nuna cewa da wahala kasar Najeriya ta cigaba da zama tsintsiya madaurinki guda. Domin yadda muke a yanzu ko shakka babu ana kwarar wani bangare wanda wannan shi ne babban abin da ya haifar da kasar sudan ta kudu wato rashin adalci, kuma idan ba ayi hankali ba maganar Gaddafi zata tabbata,domin shugaban kasa da yafi kamata ya nuna adalci ga al’ummarsa shi ne mutum na farko da ke nuna bangaranci da fifiko ga wani bangare da kuma wasu mutane.

Tabbas maganar Gaddafi dan gane da raba Najeriya bawai kawai da ka ya yita ba. Domin ya shafe kusan tsawon sama da shekara arba’in yana kallon Najeriya watakila lokacin da yake shugaban kasa a libiya shugaban Najeriya na yanzu yana makarantar sakandare ko firamare to kaga babu yadda za ayi tunani da hange nasu yazo daya. Allah masani, lokaci ne kawai zai tabbatar mana cewa shin maganar Gaddafi dangane da Najeriya zata rabu ko kuwa zata ci gabada zama kasa daya al’umma biyu.


Sufurin Jirgin kasa a Najeriya: jiya ba Yau ba!

Sufurin Jirgin kasa a Najeriya: jiya ba Yau ba!

Jirgin kasa kusan shi ne abin sufuri da yafi kowace hanya ta sufuri sauki da kuma tabbas. Jirgin kasa shi ne abinda da zaka hau ba tare da fargaba ba ko zullumi, baka tunanin hadari ko ‘yan fashi ko ‘yan kwanta-kwanta. Sannan zaka hau jirgin kasa cikin kudi kalilan. Jirgin kasa ana yi masa kirari da dama, kamar yadda shugaban Amurka ya taba kamanta gwamnatin Amurka da cewa kamar jirgin kasa ta ke ba shida ikon sauya akalar jirgin sai dai kawai ya kara gudunsa ko ya rage gudunsa.

Jirgin kasa ya fara zurga zuraga ne a Najeriya ranar 4 ga watan maris din shekarar 1901, inda yake safara daga Legas zuwa Ibadan cikin sauki da kwan ciyar hankali a wancan lokaci ga kuma arha, jirginsa ka du mutum ka dau kayansa kamar yadda masu Magana suke cewa. Daga nan likkafa taci gaba inda a shekarar 1911 aka sauya jirgin kasa a Najeriya daga mai aiki da gawayi zuwa mai aiki da man dizal sannan kuma aka kara zangon da jirgin zai ci har zuwa Arewacin Najeriya inda yake cin zangon kilomita kusan 45,000 acikin kasar nan.

Duk wannan suna karkashin hukumar sufurin jiragen kasa ta wancan lokacin inda take da jiragen kasa kimanin guda 50 wadanda ke safara gabad da yamma kudu da Arewa. Jirgin kasa kan tashi tundaka ikko ta jihar Legas har zuwa Nguru a jihar Borno ta wancan lokacin inda daga nan yakan ratsa har tsohuwar rusasshiyar jihar Gongola ta wancan lokacin, gashi da manya-manyan tashoshi a kudu da arewacin kasar nan.

Kusan babbar moriyar da akaci ta jirgin kasa a wancan lokacin itace safarar kaya da yake daga kudu zuwa Arewa inda yake Daukar gyada da fatu da kiraga da hatsi da kayan gwari wato tattasai da albasa da attarugu ya kai kudancin kasarnan, sannan ya dauko kayan Marmari kamar ayaba da lemo da kwarar manja da da tufafi ya kawo kasar Arewa, jama’a na amfani dashi cikin kwanciyar hankali. Kusan duk lokacin da jirgi ke zuwa daga kudu zuwa Arewa idan ya yada zango a zariya jama’a kan samu Alheri sosai ta fannoni da daman gaske, haka har ya karaso kano inda nan ma zakatar wata kasuwa ce ta musamman a duk lokacin da akace maka jirgin kasa yazo jama’a na ta hada-hada abin gwanin ban sha’awa. Haka nan jirgin zai tashi har ya isa jogana inda nan ma yakan yada zango duk dai jama’a na ta kaiwa da kawowa ana ta neman arziki.

Kwanci tashi hukumar jiragen kasa dake da ma’aikata kimanin 3505 a duk fadin kasar nan da kuma makarantar koyar da aiki da tukin jirgin kasa dake legas duk suka fara sukurkucewa. Itadai wannan makaranta har yau har kwanan gobe tana nan kuma ana karatu ana yaye dalibai, amma hukumar kula da sufurin jiragen kasa ta Najeriya wadda akafi sani da Railway yanzu ta shiga wani hali na ha’u’lai inda kamfanin ya tarwatse baka ganin komai sai karafa da tarin shara da tsoffin gine-gine tun na turawan mulkin mallaka a duk jihar da layin dogo na jirgin ya bi.

A wancan lokacin da ake amfani da jirgin kasa zaka iske duk titunan kasarnan suna da kyau babu gargada tundaga badagari har zuwa baga duk inda kaga titi da kyansa da lafiyarsa, da wahalar gaske kaga mota tayo laftun kaya tana bin kwalta duk wani kaya mai nauyi da za ayi doguwar tafiya da shi yana tashar jirgin kasa; wata kila wannan shi ne dalilin da yasanya tituna suke da ingancin gaske a wancan lokacin.

Amma abin yanzu ba haka yake ba. Kusan kasar nan tafi kowace kasa bada mamaki a duniya domin bawai komawa baya kawai Najeriya ta ke yi ba kawai aguje a sukwane take komawa baya kuma a murgude. Yanzu maganar da muke dukkan wadan can jirage da suke safara daga kudu zuwa Arewa sun daina wato sun zama tarihi dukkan wata safara yanzu ana yenta ne adogayan motoci masu daukar kaya fife da kima.

Kusan ashekaru 1960 zuwa 1970 dukkan manyan gurare a Najeriya zaka iske da wutar lantarki inda alokacin nan Masallacin juma’a na kofar gidan mai martaba sarkin kano lantarki ake kunnawa a ya yinda masallacin dakin Allah mai alfarma da ke makka acibalbal ake kunnawa ballantana ma kayi tunanin jirgin kasa acan. Amma yanzu bazaka kamanta Najeriya da Saudiyya ba wajen wutar lantarki haka idan ka dauki sufurin jirage kasa sunyi mana fintinaku. Domin yanzu haka akwai irin jirgin nan mai tashi kamar kiftawar ido mai gudun tsiya yana yawo ko ina a kasar.

Alokacin marigayi tsohon shugaban Umaru kasa Musa ‘Yaradua ambayarda kwangilar gyaran hanyar dogo daga legas zuwa kano ga wani kamfaninkasar cana amma har yanzu wannan zance shima shiru ka keji. Ko yaushe sufurin jiragen kasa zai dawo ka’in da na’in a Najeriya? Oho; hana rantsuwa akwai kana nan jirage da suke safara misali a legas da kaduna da kano wanda suna yi ne iyakar jihohinsu. Allah ya kaimu lokacin da harkar jirgin kasa zata koma kamar da a Najeriya.


Waiwaye Adon Tafiya: Rayuwar Bahaushe Ada Da Yanzu

Waiwaye Adon Tafiya: Rayuwar Bahaushe Ada Da Yanzu

Ya dan uwa mai karatu ina mai yimaka godiya da ka samu zarafin karanta wannan mukala tawa, Allah ya sa mu dace amin. Ko kasan rauwar malam Bahaushe a lokutan baya da suka gabata rayuwace mai ban sha’a kwarai da gaske domin tundaga Burgu har zuwa yahuri duk inda kaga malam bahaushe halinsu daya wajen tausayi da amana da biyayya da kamun kai ga kuma taimakon junansu.

A taikaice ya mai karatu Bahaushe kusan dukkan kabilun kasarnan babu wanda ya kaishi gaskiya da amana, wannan tasa kowacce kabila ta ke son hulda da malam bahaushe ba don komai ba sai don tsare gaskiya da girmama abokin zamansa. A lokutan baya wannan tasa ko kasuwanci za’a kulla tsakanin kabilu akan nemi malam Bahaushe ya zama shaida domin ana da yakinin bazaiyi ha’inci da rashin amana ba.

Zaka yarda dani idan ka kalli yadda baki daga kasashen waje idan suka zo nageriya sukan so su zo kasar hausa, misali shuwagabannin kasashe da yawa sun kawo ziyara nageriya amma duk wanda yazo nageriya bai zo kasar hausa ba to ka gayamasa tabbas yana da sauran kallo. Shugaban kasar zambabuwe Robert Mugabe yazo kasar hausa har cikin fadar sarkin kano haka tsohon shugaban kasar Tanzaniya wato julios Nyarere da kuma Shugaba yuwairi musabveni na Uganda, dama kar kayi maganar kasashen Ghana da nijar da sudan da kamaru da benin kusan wadan nan kasar hausa ta zama gida a gurinsu.

Idan kuma muka duba kasashen asiya da kasar turai da amurka dukkan wani shugaba da zai kawo ziyarar aiki nageriya yakanso yazo kasar hausa ba don komai ba sai irin yadda suke samun labarin mutanen cikinta. Idan ka dauki kasar ingila kusan zamuce kasar hausa gidace agaresu.

Wani abain ban sha’awa da rayuwar malam bahaushe har gaiyatarsa akeyi zuwa sauran kasashen duniya, badon komai ba saboda rayuwarsa abin sha’awane saboda me yana da kula da al’adunsa aduk inda ya tsinci kansa domin kuwa zaka ga malam bahaushe da sanye da babbar riga da hula da carbi a hannunsa a tsakiyar birnin landan wannan yakan baiwa turawa da yawa sha’awa ta yadda zakaga suna yawan daukar hota dashi. Ya ishi malam bahaushe alfahari shi ne an gaiyyaci hausawa kusan 42 zuwa ingila a shekarar 1897 domin su taya sarauniyar ingila Victoria muranar cikarta shekara 60 abisa gadon sarauta, ko shakka babu wannan wani abune da tarihi bazai mance da shiba arayuwar malam bahaushe.

Idan ka kalli rayuwa da zamantakewar malam bahaushe ta yadda yake kula da makwabtansa tayadda zaka samu malam bahaushe yana cin abinci musamman na dare da makwabtansa, hakana malam bahaushe yakan hada yaran makwabta ya yi masu kaciya ko asanyasu makaranta tare wannan ko shakka babu zamantakewa ce mai kyau. Tayadda wasu musamman turawa mutum zai shekara baice da makwbcin bihin ba, amma idan ka dauki rayuwarmu idan makwabcin ka ya kwana uku bai ganka ba sai ya tambaya anya wane lafiya kuwa kwana biyu bana ganinka. Wannan tasa ko acikin gaisuwar malam bahaushe zakaji ykan kula da makwabcinsa ta hanyar tambayarsa ya iyalinka kuna lafiya, da sauransu wannan tasa naga wani abin mamaki lokacin da muka gaisa da wani balarabe sai na ce ya iyalinka sai yace kaico ina ruwanka da iyalina, ni kuwa na bashi hakuri nace Allah sarki malam bahaushe rayuwarka abinkoyi.

Haka kuma idan ka dubi abokan zamanmu wato yarabawa da inyamurai zaka ga a idiyaraba bayerabe ya dauki malam bahaushe aiki a matsayin mai kula da sashin kudi wanda ko amafarki bazai taba daukar inyamuri ya bashi amanr kudi ba haka abin yake idan kaje abbah idan zaka iske inyamuri ya dauki bahaushe aiki yana kuma kula masa da dukiyarsa bai dauki inyamuri dan uwansa ba, wannan karara ya nuna irin yadda malam Bahaushe yake da amana a wancan lokacin kuma duk inda akaga malam bahaushe da shigarsa ta hausawa zakaga yadda ake girmamasu.

Na taba jin wani dan jaridar Radiyo nageriya Kaduna wato halilu getso yace ya sauka a filin jirgin sama na Heathrow da ke landan yace yaje sanye da kayan hausawa da hula da carbi a hannunsa kuma tafiyace bashi kadai ba yana cikin wata tawaga ce amma yace shikadaine ba’a bincika kayansa ba, yace awannan lokacin jami’an tsaron wannan filin jirgi sun girmamashi yace badon komai ba sai yadda suka samu labarin Bahaushe mutumne mai gaskya da rikon amana, yace aka tambayeshi mene cikin jakarka yace ‘yar kukace da yajin daddawa na kawo wa ‘yan uwana tsaraba sai kuma ‘yan tsummokarana. Yace haka nan ya wuce amma sauran abokan tafiyarsa dake kabilu daban daban ne sun sha tambayoyi da bincike.

Wannan tasa malam bahaushe ya cirri tuta domin dukkan kabilun kasarnan babu mutumin da ake girmamawa bilhakki kamar malam bahaushe kuma ciki da wajen nigeriya duk inda akaga malam bahaushe ana yimasa kallon wani mutum mai amana da gaskiya da adalci awancan lokacin.

Kamar yadda nace waiwaye adon yafiya sai kawaiwaya baya kaga yadda kake sannan sai kayi tunanin gaba me yakamata kayi. Ko shakka babu yanzu rayuwarmu bah aka take ba yanzu za’a hada baki da mista bahaushe ayi yaudara da ha’inci da makici kala-kala, sannan malam bahaushe ya zama mutum mai buri da yawa ga son taro dukiya mai dimbim yawa ta kece raini da auren mata barkatai ga son gina gidaje ko ina amma kuma ko kadan bamu son shan wahala ko ta sisi. Shin taya zamuyi mu dawo da martabar da akasan malam Bahaushe awancan lokacin mai karatu kalubale gareka.

Zuwa ga Marigayi Mallam Umaru Musa Yar’Adua

Ya mai girma tsohon shugaban kasar Najeriya ina yi maka sallama irinta addinin musulunci Assalamu Alaikum. Amincin Allah ya tabbata a gareka ina mai addu’a a gare ka da kuma fatan samun rahamar Allah da kuma addu’ar Allah ya gafarta maka zunubanka. Amatsayin ka na dan Adam kuma wanda ya rayu da mu a wannan duniyar kafin cikar wa’adinka ko shakka babu kai maikuskure ne kamar kowane bil’adama, kuma a halin da ka ke ciki ya shugaba baka bukatar wani abu daga garemu face addu’a da kuma fatan samun rahama daga madaukakin sarki wanda mulkinsa baya karewa haka kuma rahamarsa bata takaita ga wasu kawai ba shi ne da kansa yace ku rokeni zan amsa muku subuhanahu wata ala! tsarki ya tabbatar masa wanda ya dauke ka a dai dai lokacin da Najeriya da ‘yan Najeriya ke bukatarka.

Ya shugaba Mallam Umaru Yar’adua ko shakka babu a matsayina na dan Najeriya kuma mai kishin ta! kuma kasar da ka taba zama shugabanta lokacin da ka ke raye ko shakka babu ka tafi da burace-burace masu yawa, wanda masu magana suna cewa kana ta ka Allah ma yana tasa sai dai ta Allah ita ce tabbatacciya. Tabbas mun san katafi da burin ganin cewar rayuwar dan Najeriya ta kyautatu al’amura sun koma yadda suke; musamman wadan nan kudurori naka guda bakwai da ka sanya a gaba wadan da mukai ta daukin ganin ka cika wadan nan alkawura da ka dauka, kaico mai aukuwa ta kasance a gareka batare da Allah ya cika maka burinka ba. Ina mai yimaka albishir da cewa insha Allahu wadan nan kudurori naka zasu cika ko ba dade ko bajima kuma Allah yaga zuciyarka kuma ina sa ran zaicika maka ladanka.

Ya shugaba tun lokacin da ka kwanta rashin lafiya al’ummar wannan kasa sun tausaya maka kwarai da gaske birni da kauye kowa addu’a yake ta fatan alheri agareka da kuma nema maka sauki agurin Allah agaskiya ban taba ganin mutumin da ‘yan Najeriya suka tausaya masa ba kamar kai ya shugaba, tun kana kasar saudiyya muna ta yi maka addu’a har aka dawo da kai cikin wani hali mai cike da rudani ya shugaba lokacin da na samu labarin saukar ka afilin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da misalin karfe shida na safe a wata kafar watsa labari ni kadai ina kwance sai da na mike na yiwa Allah godiya! gaskiya nayi farin ciki sosai a wannan safiya, kwatsam daga baya sai labarin ya sauya cewa baka murmure ba. Amma lokacin da muka samu labarin wasu malaman addini da shuaban majalisar koli ta tabbatar da shari’a a najeriya Dacta Ibrahim Datti Ahmed sun kai maka ziyara munji sanyi a ranmu cewa kana nan kana samun sauki wannan ko shakka babu ya sa ran duk wani mai kaunarka yayi dadi.

Ranar 5 ga watan mayu da misalin karfe 6 da minti 3 na kunna radiyan Muryar Amurka abin da na faraji shi ne muryarka abinda ya fara zuwa raina shi ne cewa Shugaba ya samu sauki kawai sai najin an saka wakar mutuwa mai bantsoro daga nan hankalina ya tashi domin nasan ta Allah ta kasance agareka, tun a wannan lokaci hankalin ‘yan Najeriya ya tashi domin kuwa ka tafi alokacin da muke begen ganin irin halin da ka ke ciki ya kyautatu, domin kuwa jita-jita ta yadu sosai game da kai, kan kace kwabo jihar ka ta haihuwa Katsina ta fara daukar harami domin ‘yan uwa da abokan arziki da dangi da sauran ‘yan Najeriya suna ta tururuwa domin halartar jana’izarka Allahu Akbar yadda ka tafi haka dukkaninmu zamu taho kuma kasani wallahi kai da ka rigamu bakayi gaggawa ba kuma mu da muke raye ba mu yi jinkiri ba, kamar yadda Mamman shata ya fada a wata waka da ya yiwa chiroman Gwambe.

Ya shugaba bayan tafiyarka abubuwa da dama sun auku a kasarmu Najeriya abu na farko da aka farayi shi ne nada mataimakinka wanda kafin rantsar dashi cikakken shugaba ya rike mukamin mukaddashi, daga nan kuma abubuwa duk suka sauya domin kuwa ‘yan Arewa da yawa sukai ta rugawa Abuja suna kamun kafar neman kujerar mataimakin shugaban kasa, a karshe dai Allah ya tabbatar da ita akan Gwamnan jihar kaduna Namadi Sambo, bayan nan shugaban da ya gajeka yace zai dora daga inda katsaya, domin yadauki alkawarin cigaba da muhimman kudurorin nan naka guda bakwai. Sai dai yanzu babu su babu dalilinsu Bayan haka abin da kayi ta kokarin ganin yasamu shi ne wutar lantarki wadda sabon shugaba yace dakansa zai gyara.

Bayan haka kayi alkawarin aiwatar da karbabbe kuma sahihin zabe wanda nasan da kana raye ka aiwatar da wannan zabe akace baka ciba tabbas nasan da zaka bada mamaki ta hanyar mika mulki ga wanda ya yi nasara, shugaba yaje Washinton a kasar Amurka da Nice a kasar Faransa kuma duk ya yi alkawarin shirya karbabben zabe, inda ya dauko mutumin da kaso 90 na mutanan Najeriya suka kyautata masa zaton zai yi abin kirki a wannan hukuma ta zabe wato INEC mutumin kuwa shi ne farfesa Attahiru Jega wanda kafin dauko shi shi ne mataimakin shugaban jami’ar Bayero da ke Kano. Kuma sabon shugaban ya yi alkawarin cewa bazai bar duk wani mutum da yake dauke da katin wata jam’iyya ba yakasance a cikin wannan hukuma ta zabe. Sai dai anyi zabe kuma wanda yaci yaci wanda ya fadi ya fadi shin ya cika alkawari ko bai cika ba wannan ‘yan Najeriya su ne sheda

Ya mai girma marigayi tsohon shugaban kasa. Yanzu dai duk abin da aka shirya ya kasance. Don shugaban kasa na yanzu wanda tsohon mataimakin ka ne ya tsaya takara kuma wannan hukuma ta zabe karkashin jagorancin Jega ta tabbatar da cewa shi mutanan Najeriya kusan Miliyan 23 suka zaba. Sai dai babban abokin hamayyarsa tsohon shugaban kasa Gen. Muhammad Buhari da jam’iyyarsa ta CPC sun garzaya kotu da nufin kalubalantar wannan zabe; kamar yadda shi Gen. Buhari ya yi a baya na kalubalantar zabenka a karkashin tsohuwar jam’iyyarsa ta ANPP wadda tsohon Gwmanan Jihar Kano Mallam Ibarhim Shekarau ya yiwa takara.

Ya mai girma marigayi, kamar yadda ta faru a lokacin ka kotun sauraran kararrakin Zabe ta tabbatar da shugaba mai ci wato Goodluck Jonathan a matsayin wanda ya lashe wannan zabe. Kamar yadda ta faru a agareka. Ya maigirma tsohon Shugaban kasa na so nayi babbar mantuwa ta rashin shida maka abin da ya biyo bayan sakamakon zaben shugaban kasa.

Kusan bada sakamakon zabe ke da wuya sai rikici ya barke a kusan daukacin jihohin Arewa inda matasa suka fusata suka yita kone-kone musamman Gidajen sarakuna wadan da ake zarginsu da karbar toshiyar baki da kuma gidajen fitattun ‘yan siyasa kamar Alh. Bashir Tofa da Rt. Hon. Ghali Na’abba a kano haka abin yake a kaduna kai hattana tsohuwar ministarka ta ilimi Haj. Aishatu Dukku wadda ake kallo a matsayin wadan da suka raba gari da shugaba mai ci itama bata tsira ba daga wannan kone-kone, antafka asarar dukiya mai dimbin yawa. Bayan da Dantakarar jam’iyyar CPC Gen. Buhari ya barranta daga masu wannan kone-kone inda yace hattana shima an kona masa motoci abin ya lafa.

Daga nan kuma aka shiga batun hada-hadar rantsar da sabon shugaban kasa. Wanda wani abu mara dadin ji ya faru a yayin wannan hidima, ya maigirma tsohon shugaban kasa juma’ar da ta ta zo kafin ranar lahadin da a itane za a rantsar da shugaban kasa an tsaurara matakan tsaro a kusan ko wane gefe na babban birni tarayya Abuja, inda Musulmi da zasu tafi Babban masallacin kasa sallar juma’a aka tsananta musu ta hanyar sa su daga hannu sama da yin doguwar tafiya a kasa kafin sukai ga masallacin, ya mai girma shugaba lokacin da aka rantsar da kai bamu fuskanci wannan matsin lamba ba. Wannan ta sa limamin da ke fassara huduba da turanci Uztaz Abubakar Siddeeq ya nuna rashin jin dadin abin da akayiwa musulmi inda yace harda jakadun kasashen duniya sun fuskanci wannan wulakanci, wannan ta kai ga dakatar dashi akan wannan aiki da ba biyansa albashi ake yi ba.

Ya mai girma marigayi Umaru YarAdua, bayan rantsar da shugaban kasa ya sauya dukkan al’amura ba yadda aka tsammata ba. Sannan ya kafa kwamiti karkashin dattijo wato Sheikh Ahmad Lemu kan ya binciki musabbabin wannan rikici da ya biyo bayan zaben shugaban kasa, kwamitinsa ya yi bincike na gaskiya da adalci kamar yadda muka zata kuma ya mika rahotonsa! Rahoton ya kunshi muhimman abubuwa wadan da idan har ambisu za a samu kyautatuwar al’amura, wanda kuma suka tsoratar akan cewa matukar aka bi son zuciya aka kaucewa wannan rahoto kasar nan na iya fadawa wani mawuyacin hali da kasashen larabawa suke ciki a yanzu.

Bayan nan kuma, wasu muhimman al’amura da suka shafi tsaro sunyi ta aukuwa, kamar rikicin Jos wanda musulmi suka ji haushinka a lokacin da kake raye inda kaje ta’aziyar rasuwar Gbom Gom Jos da Victor Pam, amma ko ka tsaya ka jajan ta musu. Wannan rikici dai har yanzu da nake rubata maka wannan kasida yana nan kuma yana cigaba, shugaban kasa da gwamnan jihar plateau sun kasa shawo kan wannan al’amari, kisan rai kusan yanzu har ya zama ba labari ba a birinin Jos da sauran sassan jihar plateau.

Haka kuma ya shugaba, Rikicin nan na Boko Haram da ka bada umarnin gamawa da su kafin tafiyarka ta karshe zuwa neman magani saudiyya wanda shi ne ya kai ga halaka shugaban kungiyar mai suna Mallam Muhammad Yusuf, wannan rikici shima ya dauki sabon salo inda akayi ta tayar da bama bamai a garin Maiduguri abin ya wuce dukkan lissafinmu, har sai da ta kai ga rasa ran Dantakarar gwamna na jam’iyyar ANPP Alh. Madu fannami Gubio da wasu fitattun mutane da masu unguwanni abirnin na Maiduguri, babban wanda ya faru kuma ya girgiza mu shi ne wanda bom ya tarwatse a damaturu ta Jihar Yobe wanda rahoton ‘yan sanda ya nuna kusan mutane 100 ne suka halaka tare da daruruwa da suka ji raunuka.

Sannan kafin wannan na damaturu ya faru. Bom ya tarwatse a hedikwatar ‘yan sanda ta kasa da ke Abuja, ‘yan awanni bayan shugaban ‘yan sanda na yanzu wato Hafizu Ringim ya yi ikirarin cewar kwanakin ‘yan Boko Haram kididdigaggu ne. Sannan an sake samun wani Bom da ya fashe a ginin majalisar dinkin duniya da ke Birnin tarayya Abuja, duka wadan nan hare-hare kungiyar Boko haram ta dauki alhakin kaisu.

Sannan, gwamati ta nada kwamiti karkashin Giltimari na ya duba yadda za’a shawo kan al’amarin ‘ya ‘yan kungiyar ta Boko Haram sai dai wannan ma bai biya bukata ba domin kuwa ‘yan kungiyar sun zargi shi Giltimari da marawa tsohon gwamna Ali Shariff baya, yanzu dai shima giltimari ya mika rahoton sa zuwa fadar shugaban kasa.

Da yawan mutane suna ganin gwamnatin tarayya ta bayar da a huwa ga wadan nan matasa; kamar yadda ka cika kudurinka na farko wato samar da cikakken tsaro a yankin neja dalta ta hanyar yiwa wadan nan tsageru ahuwa da mayarda su makaranta da koya masu sana’o’i da basu jari, wanda wannan shugaban ya cigaba da wannan tsari ta hanyar kashe masu kudi makudai tare kuma da turasu kasashen Turai da Amurka da Malaysia da Afurka ta kudu wai duk da sunan yi musu ahuwa, wanda wannan shi ne abin da ke neman motsa ko kuma iza wutar kabilanci a zukatan ‘yan Najeriya inda da yawanmu ‘yan Arewa muke ganin bai kamata a fifita wadan nan tsageru da wannan ta gomashi ba abar miliyoyin matasa a yankin Arewa suna watan gaririya akan tituna, da yawa suna ganin irin wannan shi yake haifar da kungiyoyi irinsu Boko Haram da darul Islam da makamantansu a yankin Arewa.

Ya mai girma marigayi tsohon shugaban kasa, hukumar nan da ka tursasawa shugabanta na da sauka tare da mayar da shi makaranta a Kuru tare da kokarin kamashi da laifin da bai jiba bai gani ba wato Mallam Nuhu Ribadu wanda shi ma ya yi takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar ACN a zaben da ya gabata, ka nada Uwargida Farida Waziri a matsayin wadda zata jagoranci wannan hukuma wanda ya gajeka shima ya barta don taci gaba da aiki a wannan hukuma ta EFCC, amma sai dai mafi yawan ‘yan Najeriya sun zarge ta da gazawa wajen aikinta bata iya kai banten ta ba kamar yadda magabacin ta Mallam Ribadu ya kai ta hanyar kame tare da kwato dukiyar da azzaluman shugabanni suka diba alokacin da suke rike da madafan iko. Yanzu dai itama madam Waziri ta kama gabanta a wanna hukuma kamar yadda shugaban kasa ya umarci kakakinsa Dr. Rueben Abbati ya bada sanarwar sauke ta daga shugabancin wannan hukuma da umarta Mallam Ibrahim Lamorde a matsayin wanda zai rike hukumar nan da wani lokaci .

Abubuwa da yawa sun faru, ya mai girma marigayi tsohon shugaban kasa tun bayan barinka wannan duniyar Musamman ma a inda kafi sani wato Najeriya, bazai yiwu gareni na baiyana maka dalla dallar abin da ya faru ba duk da nasan wannan sakona ba zai sameka ba, amma ina fata ya zama izna. Kamar yadda hausawa suke cewa “kukan kurciya jawabine amma......”

Daga karshe ya mai girma marigayi tsohon shugaban kasa, ina yi maka addu’a ta fatan alheri da samun rahama agurin mahaliccinka da kuma fatan can inda ka ke tafi nan. Allah ya tabbatar mana da alheri a kasarmu Najeriya ya azurtamu da shugabanni masu tsoron Allah.