Sunday, December 21, 2014

Siyasar 2015 An Kai Arewa An Baro


SIYASAR 2015 AN KAI AREWA AN BARO

Shi fa yaki irin na siyasa dan zamba ne, dole ayi shirin tunkararsa indai da gaske yakin za'a yi. Dole kayi nazarin kanka a karon farko, kasan waye kai me zaka iya, meye karfinka, meye rauninka, meye manufarka, me kake san cimmawa; sannan kuma, sai ka nazarci abokin fito na fito, meye karfinsa, meye yake nema da zai iya cin lagonka da shi, wanda daman kai tuni ka gama sanin wadan can hanyoyi ka gama nazartarsu, dan haka ko da abokin fito na fito ya taso maka kana da dukkan dabaru da kai tanadi na kare kanka daga duk wani yunkuri irin nasa. Dole kuwa kai haka, domin kaine ka taro yakin ba shi ne yazo ya sameka ba, dan haka ne aka Ruwaito Manzo SAW idan zai fita Yaki yakan nufi Gabas alhali kuma inda zai tunkara a yamma yake, wannan dabara ce ta yakin da ake neman cin nasara da gaske.

Manyan 'yan Siyasa daga Arewa tun lokacin da aka fara fuskantar 2015 sukai ta batun dole sai mulkin Najeriya ya koma Arewa. Alhali babu wani shiri da akayi dan hakan, wace Manufa Arewa take da ita gamammiya idan Mulkin ya dawo Arewa? duk da dai kawai yaudara ce kawai ake yi da sunan Arewa, kuma galibi Talakawa sune ke bata lokacinsu da sunan Arewa, dan nasan babu wani dan siyasa da zai ce yana yin siyasar Neman Mulki kuma yace da sunan Arewa yake yi. Shi yasa galibin masu kiran Arewa, kodai 'yan Siyasar da ba neman Mulki suke ba, kawai basa san a manta da su ne shi yasa suke kiran Arewa, ko kuma wasu mutane ne da ba zasu iya sanyawa ako hana komai ba. Daman kuma Talaka maganarsa bata cika tasiri ba a wajen masu mulki.

Shin masu fatan mulki ya dawo Arewa wane tanadi suka yiwa hakan? Idan Mulki ko Shugabancin Najeriya ya dawo Arewa me suke san cimmawa, ko kuwa kawai muna san Mulki a suna ace wane dan Arewa shi ne Shugaban kasa alhali kuma babu wani abu da zai iya kullawa! Na farko dai tun ran gini tun ran zane, wadan da suka ginamu akan kabilanci sunyi kuskure. Shi yasa aka wayi gari babu wani da yake batun Najeriya a siyasance, dan kudu fatansa dan kudu ko da kuwa babu wani abu da za'a tsinanawa mazabarsa, haka shima dan Arewa, ai bincike ya nuna cewa da dama daga cikin mutanan kudu maso kudu suna cikin mawuyacin halin rashin aikin yi da rashin karatu, duk kuwa da cewa sitiyarin da ke jan Najeriya dan garinsu ke tukashi.

A ganina da wahala Mulkin Najeriya ya iya dawowa Arewa a hannun jam'iyyar hamayya, idan maganata gaskiya ce, to Gwamnonin nan guda biyar ko bakwai da suka tada kayar baya a PDP kuma daga karshe suka fice suka koma APC sune suka kai Arewa suka baro! Wannan dai ra'ayi da tunani na ne, kuma gwargwadan abinda na gani na fahimta. Sai nake ganin kamar muna da saurin mantuwa, mun rudu da yawanmu alhali kuwa a Najeriya ba'a zaben gaskiya a matakin Shugaban kasa! Batun Arewa da Yarabawa kuwa aganina wani abu ne adukunkune mai rikitarwa, dan kuwa mai yasa ba'a dauko Kayode Fayemi da ya fadi zaben Gwamnan Ekiti an bashi mataimakin Buhari ba? Duba da cewa sananne ne kuma anga kamun ludayinsa, amma aka dauko tsohon kwamashina alhali ga Gwamna da yake da dukkan kwarewa ta Mulki! Wannan fa wata katuwar ayar tambaya ce, amma duk aka ja baki akai gum... Zan cigaba In sha Allah.

Yasir Ramadan Gwale
21-12-2014

Sunday, December 14, 2014

Kwangwaratuleshans Janar Muhammadu Buhari


KWANGWARATULESHANS JANAR BUHARI

Assalamu Alaikum Warahmatullah. Sunana YASIR RAMADAN GWALE, ina mai yin amfani da wannan dama wajen taya Janar Muhammadu Buhari murnar lashe zaben fidda gwani a karon farko da aka kasa a faifai Janar yayi takara kuma ya lashe zabe. Ba shakka na san Zainab na cike da murnar samun wannan Nasara, ina kara tayata murnar samun wannan Nasara da GMB yayi.

Ina fatan Janar Buhari a matsayinsa na jagora zai rungumi kowa da kowa dan tafiya tare. Nasarar Buhari nasara ce ga Dimokaradiyya, a koda yaushe dimokaradiyya na alfahari da irin wannan damar da ake baiwa al'ummah dan bayyana ra'ayinsu na tsayawa zabe. Haka nan kuma ina taya Gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso murnar zamowa na biyu a wannan zabe, ba shakka Kwankwaso yayi kokari ya nuna iya siyasarsa, da yawa na ganin Atiku Abubakar ne zai zo matsayi na biyu, amma kwankwaso ya shammaci mutane. Ina kuma taya Atiku Abubakar din alhinin samun wannan matsayi na uku, na tabbatar ba haka ya so ba amma hukuncin Allah shi ne abin karba, kuma ya burgeni matuka da ya nuna jarumtaka ya karbi faduwa! Wannan ita ce kaiwa makura a dimokaradiyya duk da ba laifi bane neman hakki idan har wani yana ganin anyi masa ba daidai ba.

A daya gefen kuma ina taya tsohon mawallafin jaridar Leadership Newspapers Pharm. Sam Nda-Isiah murnar samun kuri'u guda goma ba shakka, na aminta da irin kishin kasa da kaunar Najeriya da Sam yake da shi, ina masa fatan Allah ya bashi wata dama da zai hidimtawa al'ummar Najeriya.

Haka kuma, Janar Buhari zai kuma fuskantar Shugaban Kasa Dr. Goodluck Jonathan dan yi wannan karon battar a karo na biyu. Tun a zaben da ya gabata na 2011 da yawan 'yan Najeriya masu bibiyar harkokin siyasa sun san lagwan kowa tsakanin Buhari da Jonathan. Fatana shi ne Allah ya saukaka mana al'amuranmu ya zabar mana shugabanni na gari adalai a dukkan matakai na shugabanci. Kuma in sha Allah zan taimaka da Naira 10,000 ga kwamatin yakin neman zaben Janar Buhari na BSO.

Ina taya murna ga 'yan uwanmu abokanmu 'yan Buhariyya musamman wadan da suka tayamu murnar samun Nasarar Malam Nuhu Ribadu da Malam Salihu Salihu Sagir Takai dama wadan da basu tayamu murna ba, da kuma masu yi mana mummunan fata, har da masu yi mana tadiya da mugun baki irinsu Mansur Manu Soro duk muna musu murnakuma muna yi musu adduar fatan alheri. Allah ya taimaki kasarmu Najeriya ya bamu nasara, ya amintar da mu ya bamu lafiya da zaman lafiya.

Cc: Ibrahim Sanyi-Sanyi, Muhammad Aliyu Dutsin-Ma, Kwamared Baban Shareek Gumel, Affan Buba Abuya, Sagir Musbahu Daura Dole, Hussein Abdussalam, Attahiru Muhammad Marnona, Abubakar Aminu Ibrahim, Bashir Ahmad, Sunusi ShehuSunusi Musa, Auwalu Lawan Aranposu, Hamza Ibrahim Baba, Abdulrashid Ahmad, Baba Bala Katsina, Ibrahim D Itsenyabi, Khaleel Nasir Kiru, Lawal Muazu Bauchi, Yamai Muhammad, Hk Yaradua, Husain Husain Kyar'adua, Uba Danzainab.

Bcc:....

Yasir Ramadan Gwale
14-12-2014

KHRTAOUM: Ban Kwana Da Ismail Lamido


KHARTOUM: BAN KWANA DA ISMAIL LAMIDO

Da fatan an sauka gida lafiya Malam Ismail Lamido. Allah ya saka da alheri da wannan takakkiya kuma ya bar zumunci. Muna godiya mara adadi ga Jagoranmu Sardaunan Kano Malam Kano Shekarau CON. Allah kuma ya bamu Nasara a wannan zabe. Allah ya baiwa Malam Saluhu Sagit Takai Gwamnan kano kuma ya yi masa jagoranci zuwa ga adalci da daidaito. Allah ya taimaki jihar Kano da Najeriya.

Yasir Ramadan Gwale
13-12-2014

Thursday, December 11, 2014

Taya Murna Ga Malam Shamsu Abbaty

L-R Shamsu Abbaty da abokinsa

TAYA MURNA GA MALAM SHAMSU ABBATY

Congratulations Malam Shamsu Abbaty. Allah ya sanya alheri ya yiwa rayuwarka albarka. Ba shakka yau muna cike da farinciki da farincikinka ka, zamu kasance cikin sahum masu murna da fatan alheri a wannan rana. Allah ya yi maka jagora ya ya sanya maka albarka.

A madadin Ni Yasir Gwale da Auntynka Zainab Gwale muna tayaka murnar wannan saukar karatu da ake yi a yau a Kamfala Uganda.

Yasir Ramadan Gwale
10-12-2014

Tuesday, December 9, 2014

Alhamdulillah Takai Yaci Zabe


ALHAMDULILLAH TAKAI YACI ZABE

Godiya ta tabbata ga Allah madaukakin Sarki da ya nuna mana wannan Nasara ta Malam Salihu Sagir Takai da ya zama dan takararmu na Gwamna a Kano. Muna kara mika godiya ga Daliget da suka zabi cancanta. Allah ya bamu nasara a babban zabe mu kada madu bacci. Allah mun gode maka.

JIGAWA: Muna taya murna ga Malam Aminu Ringim bisa nasarar da ya samu. Allah ya nuna mana babban zabe lafiya.

KADUNA: Muna taya Dallatun Zazzau Malam Ramalan Yero murnar samun nasara da yayi. Allah ya baka Nasara a babban zabe Dallatu.

Yasir Ramadan Gwale
09-12-2014

Alhamdulillah Malam Nuhu Ribadu Yaci Zabe


ALHAMDULILLAH MALAM NUHU RIBADU YACI ZABE

Alhamdulillah muna godiya ga Allah madaukakin sarki da ya nuna mana wannan Nasara. Haka kuma muna kara mika godiya ga Daliget na Adamawa hakika kun zabi wanda ya dace. Muna murna da wannan zabe da kuja yiwa Malam Nuhu Ribadu. Alhamdulillah Allah mun gode maka. Allah ka nuna mana babban zabe lafiya kuma muna kara rokonka Ya Allah ka baiwa Malam Nuhu Ribadu nasarar lashe babban zabe mai tafe. Masha Allah.

Muna kuma fatan kara samun Nasara ga Malam Salihu Sagir Takai a nan gaba kadan.

Yasir Ramadan Gwale
09-12-2014

Sunday, December 7, 2014

Jinjina Ga Jami'an Tsaron Najeriya


JINJINA GA JAMI'AN TSARON NAJERIYA

Ba shakka wannan Nasara da jami'an tsaron Najeriya suka samu na kame wannan jirgi cike da kayan yaki da ake kyautata zaton makiya zaman lafiyar Najeriya ne suke taimakawa 'yan ta'adda da miyagun makamai wajen jefa rayuwar al'umma cikin mawuyacin hali, wannan Nasara da jami'an tsaron suka samu na kame wannan jirgi abin a yaba ne tare da karfafa musu guiwa wajen jajircewa akan aikinsu. Muna yabawa da wannan aiki na kokarin tabbatar da zaman lafiya, da kuma kwa-kwulo wadannan miyagu azzalumai 'yan ta'adda wadan da suka dauki zubar da jinin al'umma a matsayin wani aiki na yau da gobe.

Addu'armu bata tsaya kadai akan Allah ya tona asirin irin wadannan miyagu ba, Muna kara yin adduah akan Allah ya yi mana maganin duk wani abu da yafi karfinmu, Allah ka yi mana maganin duk wasu miyagu azzalumai 'yan ta'adda da suka addabemu. Allah ka rusa shirinsu ka wargaza sha'aninsu. Allah ka darkakesu, ka dawo mana da dawwamammen zaman lafiya.

Allah ka taimaki jami'an tsaronmu da suke aiki babu dare babu rana wajen ganin an samu zaman lafiya a garuruwanmu. Haka nan kuma, muna kira ga Gwamnati da ta basu dukkan kulawa wajen ganin sunci lagon 'yan ta'adda. Allah ka taimaki kasarmu Najeriya ka bamu lafiya da zama lafiya.

YASIR RAMADAN GWALE
07-12-2014