Friday, April 12, 2013

WAKAR BULALIYA TARE DA MALAM SANI YUSUF AYAGI


WAKAR BULALIYA TARE DA MALAM SANI YUSUF AYAGI


Randa duk kwana ya kare
ko a daki ko a zaure
ka rufe kofa da kyaure
zata zo RAN za a zare ba da kai mata ja inja ba

Ba a jinkirtama kowa
ba a gaggautama kowa
ajami ko larabawa
in ta zo ko sai macewa ko sakan ba a dadawa


kunji dai ku 'yan uwana
manya manya da kankana
zata zo musu ko a gona
ko a daki ne na kwana In ta zo baza su kwan ba

Malamai ko jahilawa
masu kudi talakawa
masu mulki dogarawa
zata zo musu ba rabewa ba ganin matsayi take ba

Dubi ayar kur'ani
kullu nafsin tai bayani
za'iqatul mautu aini
ko a kauye ko a birni babu wanda ba zai mace ba

duk mutum da sanadinshi
wani yai cuta ta jashi
wani ba ciwo ta kaishi
wani ko hadari silarshi babu yadda bazata zo ba

wani na yawo a titi
wani na ciniki a kanti
wani ko na shafa fenti
wani ko ya kama kati bai sani yau zai mace ba

wani na fama da aiki
wani na sukuwa da doki
wani na wanka a tafki
wani ko ya kama wanki zata zo bai karasa ba

wani ko na cin abinci
wani ko sai yayi barci
wani na fama da kunci
wani ko a cikin takaici zai mace bai ma sani ba

wata na tukin tuwanta
wata tazo haihuwarta
wata ko na kan gadonta
zata zo dan zare ranta bada ta farka anan ba

mutuwa ita ba ruwanta
inta zo ba mai hanata
babu mai ikon tareta 

masu mulki ko wadata dai cikinsu bazai hana ba


ba ruwan mutuwa da mulki

Ba ruwan mutuwa da mulki
ko na mai rawaninga sarki
in ta zo tilas ta dauki ransu mulkin bai hana ba

dubi jariri kamar shi
sai yana hannun uwarshi
ta riga ta rungumeshi
sai ta rabo tsaf ta jashi ga uwar bata ko hana ba

ko ta dauki uwar ta barshi
ba ruwanta da tausayinshi
bata duban wai uwarshi
zata dau nono ta bashi inta zo ba za ya sha ba

Mutuwa bata kulawa
saurayi ko 'ya budurwa
yanzu ta maishe su gawa
babu sauran shakatawa bako zata jira biki ba

Mutuwa ba raya shaho
ta buge yaro da tsoho
ta kade kuturu makaho
wani ma tun kan a haihu zai mace ko ba da wai ba

Mutuwa inhar ta sauka
a gida wani zata dauka
ba ruwanta da masu sanka
yanzu kaji ana ta kuka wanda bai hana dauke ran ba

yanzu aya zan karanta
'yan uwa kowa ya jita
ko wani zaiga ma'anarta
yadda kowa zai kowa fahimta ba tare da na barta a dunkule ba

Aina ma kuntum ku gane
yata rukumul mautu kune
ai walau kuntum mutane  i burujun can gaban ne 'yan uwa ban karasa ba

Ma'ana Allahu yace
ko ina ne kun kasance
zata zo muku karku mance
Mutuwa Ala-sa mu dace kan ta zo mana duk mu tuba

kunji dai zance na aya
gaskiya ce babu karya
ko ina ne kunka buya
zata zo muku sai ku shirya ba shirin shan magani ba

Ga misali mai kulawa
Mursalai haka annabawa
ga sahabu da auliyawa
sun wafati da dadewa in kana ji ne da kanka 

 
da isa ko dukiyarka
ko yawan mulki gareka
can a baya akwai gabanka ya wuce bai dakata ba

In yawan bauta gareka
rabbi yai wani kan ayika
wanda in bautar yafika
daukakar ya sha gabanka ya wuce bai ko tsaya ba

Kunji tarihi da kissa
Annabin Allah da kansa
wanda babu mutum kamarsa
Musdafa an zare ransa ya waninsa ba zai mace ba

wanda zabi anka bashi
shin a dau ran ko a barshi
Daha dan jarumtakarshi
sai ya zabi a zare ranshi bai bukaci ya dakata ba

Dan uwa bar shirya fati
kyale cin naman faranti
tunda annabi yai wafati
babu mai ikon sabati duniyar nan bai mace ba

Da uwa da uba gareni
sai uban ya mace ya barni
tun ina karami ku ganni
sai uwata ta rikeni har na girma ba zan rufe ba

Sai na girma gaban uwata
sai ta kyautata rayuwata
har ta min aure da kanta
gashi yau ni na rasata ban ko samu kamarta dai ba


Duniyarnan ba kamarta
shi yasa in na tuno ta
yadda tai mini tarbiyyarta
sai nace Allah jikanta . . .

Gashi yau na samu kaina
ba uwata ba ubana
sun bacewa ganin idona
to ashe wataran kwa raina zai bace ko ba da wai ba

'Yan uwa in kun fahimta
duniyar da muke cikinta
dole kowa zaya barta
babu mai ikon suturta wai yace ba za ya kau ba

'dan uwa bari yin dagawa
dan ganin ka samu baiwa
bar ganin ka zarce kowa
mutuwa na kewa yawa babu inda bazata je ba

Ran da duk aka zare ranka
yan uwanka suna ta kuka
wanda bai dawo da ranka
ai su ce Allah jikanka zaji ba sui ta kururwa ba

Burinsu kawai a kaika
a saka ka a kabarinka
sai su zo kan dukiyarka
sui rabo ba mai tuno ka sai kace basu sanka da ba

da kana mulkin gidanka
yanzu bamai girmamaka
babu sauran bada doka
babu mata 'ya'ya da jika sai kace basu sanka dai ba

Alhajin Allah kamarka
mai isa da isa ya sanka
gashi yau likkafaninka
ba a sa shadda a dinka sai farin alawayyo duba

kaga tarin dukiyarka
bata amfani gareka
duk yawan motar gidanka
ba a kaika a marsidinka sai kace ba taka ce ba

'dan uwa kardai ka mance
duk kudin nan naka nace
anyima gata fitaacce
sai a dau motar itace a saka ba marsidinba

matukar sun girmamaka
sug gine kabaringa naka
daga nan sun sallameka
ko ziyara in gayama sai su shekara ba su jeba

Dubi duk girman gidanka
sai ya zam kango rashinka
wanda ba ya shiga da ranka
sai ya aure sahibarka yash shige ba a mar hani ba


Dan uwa in an saka ka
a cikin kabaringa naka
ko ina an toshe iska
babu mai sha'awar taya ka shi zaman nan ba da wai ba

Sai a tashi kawai a barka
daga kai sai dai halinka
sai mankir nankir su sauka
sush shigo dan tambayarka duk da ko baka san guda ba

Sai a dawo ma da ranka
sai su hau bisa tambayarka
in ka amsa sai su barka
sai a yalawata kabarinka ba a barshi a takure ba

Inko har suka tambayeka
babu amsa zaka koka
sai su hauka kawai da duka
sai a matsatse kabarinka har gabobi duk su bamban

Sai a nuna ma makoma
hawuya koko jahima
inda nan zakai ta fama
har zuwa tashin kiyama babu sassaucin azaba

'Dan uwa zan sake janka
kar ka ce na tsorata ka
zanyi ma zancen gidanka
inda farko za a kaika sanda ka mutu ba da wai ba

Kwanciyar kabari tuno ta
ba katifa zaka yi ta
ba filo haka zaka kwanta
babu juyi dan ka huta kaji ba karya nake ba

Babu haske babu iska
babu ac babu fanka
kai ka dai ba sahibarka
sai abinda kawai ka aika zai fito maka ba da wai ba

Kwanciyar nan ko a barka
babu zagi babu duka
kaita bacci dai abinka
wata ran ka so ka fark bada an maka izini ba

To bare kuma babu tashi
ga gumi zafi ka sanshi
ba rigingine sam cikinshi
ya ka shirya zaka yi shi baka sa Allah gaba ba 


Kaji dai yana yin cikin shi
gashi ya zama babu fashi
dole kowa zai shi ge shi
ya kamata ka tanajeshi da yawan zikiri da tuba

In gaya muku 'yan uwana
kun sakankance ganina
sai yawan sabo da barna
sun sani da wuta da jannah ya ba mu yi musu tana di ba

Shugaba kake ko ko gwamna
ofishin nan naka auna
wanda kai ka shige ka zauna
sai ka dau biro ka zana kai zaton fa ba'a sani ba

In tuna maka karka manta
karka yarda ka shirya cuta
ko kadan ce karka yita
in ko kayi an rubuta bako gogewa ake ba

Karka ce ba'a ganinka
tunda ba'a shiga wajenka
sai da yin izini a ganka
to kaji Allah na ganinka ga rakib da atib ka lura

duk abinda kake ka gane
shin na kirki ko tsiya ne
su suna hangenka zaune
sun rubuta ko kadan ne basu kyale ko guda ba

'Dan uwa komai ka shuka
zai fito kaji babu shakka
zaka girba kai da kanka
Randa ka mutu kai da kanka zaka zana ba da wai ba

Sun ka ce can nayi sata
can ko na bai wane kyauta
can ko naci hakkin makota
kayi alheri da cuta baka biye ko guda ba

shin ku dubi mu'amalarmu
mun sake sam ba ruwanmu
bamu tanyon 'yan uwanmu
dukiya daga mu diyanmu bamu ba kowa kwabo ba


kasuwarmu Idan ka duba
bamu ware haram halal ba
bamu san zi da ribaa ba
bamu bar yin algushu ba sai kace ba zamu kau ba

'Yan uwa tuni ni na lura
mun sakankance da naira
burikanmu kawai mu tara
ba tunanin zamu saura bamu dau mutuwa akwam ba

Ga shigarta kwarai ganina
gashi mun cika cin amana
ga yawan sabo da barna
sabuka manya kanana yi muke karya da giba

Ni abinda ka bani haushi
'dan adam sam ba ruwanshi
bai kula da abin gaban shi
ko hisabin dukiyarshi dan uwana bai kula ba

Wanga wake 'yan uwana
nayi dan wa'azi akaina
dan na lura na gyara kaina
in rage sab'o da kaina in tuno mutuwa na tuba

Dan ganin ni na shagalta
mutuwa bana tuno ta
ban tunanin ya kamarta
nafi kyautata duniya ta lahira ban ko kula ba

Shi ya sani na wallafa ta
dan tunawa zuciyata
da akwai mutuwa gabanta
ko da yaushe zata zo ta bakwa sa rana take ba


Nafi so naga na wadata
na sayo babur da mota
marsidis honda tiyota
ga gidana har da kwalta can a gefe ba gari ba

In yi dinkin kece raini
riguna ko wanne launi
shadda boyal na aini
nayi dan nima a sanni mai kudi ne ba kadan ba

Nan da nan kaga nai abokai
masu kuddi har sarakai
masu mulki malamai sai
sui ta dan kamin mukami duk da ban iya godiya ba

Sai a ce an ban sarauta
shugaban duka masu kyauta
aita famar gayyata ta
gun afil fand nai ta kyauta ba 'yar kadan ba

Malamai ko su zo gidana
sui ta nemana mu gana
sai a ce musu nayi kwana
sai su sami guri su zauna basu san ko zan fito ba

Sai su kirkiri yin karatu
ko su kawo min rubutu
wai na sha dan kar na zautu
dukiya haka sai da hutu kai magauta suc ci riba

gun biki sai an jira ni
duk ana burin a ganni
in nazo fa a kewayeni
ga maroka na zugani inyi kyauta ba kadan ba

To a sannan na gama ni
dole kowa zaya bini
yaita famar girmamani
sai ace komai sai an jirani ko abin ni ban sani ba

dukiya ta ja sarauta
na zamo malam akanta
ba a karyata magana ta
sai a so ni maza da mata duk da ko ban san alif ba

ba a karyata magana ta
ko a yaya ni nayi ta
ko nace na shuka fata
ta fito kuma naga dan ta wani zai ce ba da wai ba

Ana haka sai na gane
duniya wani gun zama ne
burinka da nake haram ne
mai nutsar da mutum a zaune wanda bai dace da ni ba


Mutuwa ni bani san ta
bani san naji ambatonta
dan tana kada zuciya ta
take sai kaga na dimauta kwarjinin fa ba zai gushe ba

Na sani ita gaskiya ce
naji lallai na amince
zata zo ba kauce-kauce
to fa Allah na dimauce dan kwa ban mata tanadi ba

Mai ya sani nake gudunta
yadda malam ya fade ta
gashi yadda ya suffata ta
naga babu gwani a gunta yaya ba zan fargaba ba

Ba macewar nag guda ba
mutuwa ni ba da wai ba
ba ina kyamarta ne ba
karta dau raina ku duba kwanciyar kabari na duba

Nayi sab'o ba kadan ba
gashi ba sadaka nake ba
ni ko ban wata nafila ba
ban yi aiki masu kyauba ya ba zan mata farga ba ai

Ni mutum ne mai kasala
mai bukatar tara daula
gani bana san wahala
banda sallolin farilla gashi ban wani tanadi ba

Inka duba ayyukana
wanda dai ni nai da kaina
manya manyan laifukana
nai nadama ni da kaina rabbi ba zan sake yi ba

In na dubi abinda nay yi
laifuka ne masu nauyi
sai jikina yay yi sanyi
sai kawai rokon buwayi gafara ba sake yi ba

Tunda yanzu idan ka ganni
duk gabobi sunyi rauni
ya gwani ar-Rahamani
Nayi rokona da nuni kaj ji kan ummi da abba

Rabbi wanke mahaifiyata
dagga dukan laifukanta
dole nai roko ka sata
can gidan rahama ta huta ba da an mata bincike ba


Rabbi kaine Arrahimu
Shafe dukkan laifukanmu
duk abinda mukai ka barmu
a gidan nai'mu ba da ka kula laifukanmu

Rabbi baban ka barshi
kar a bincika ayyukanshi
naay yi roko jalla sashi
cancikin firdausi sashi rahama bai sha wuya ba

Duk hakkina ya biyani
ya gwada mini kur'ani
makaranta shi ya kaini
yayi min horo da nuni bai gwadan san zuciya ba

Ya gwani Allah karimi
zul-jalal wal'ikirami
nayi roko ya rahimi
kaj jikan dukkan musulmi hada kanmu mu daina gaba

Naga nan ne ya kamata
'yan uwana in takaita
in batun mutuwa na huta
Allah sa dai mun fahimta ba mu barta mu shantake ba

Wanda duk ya tsaya ya jita
ko ya dauka ya karanta
inda yagga kure cikinta
Yai yi himma dan ya gyatta sani bai wuce yin kure ba
 
 
 
 
 
 
 

Thursday, April 11, 2013

BA MA KIN SHUGABAN KASA DAN SHI BA MUSULMI BANE, SAI DAI . . .

BA MA KIN SHUGABAN KASA DAN SHI BA MUSULMI BANE, SAI DAI . . .

Ko kadan bama kin shugaba Goodluck Jonathan dan kasancewarsa shi ba Musulmi bane. Muna kinsa ne dan shi ba Adali bane, muna kin mummunan halinsa na zalunci da rashin gaskiya da nuna wariyar yanki da kabila. Ya fifita mutanan yankin da ya fito akan sauran 'yan Najeriya, an daga musu kafa suyi dukkan tsiyataku da mugayan kalamai masu barazana ga tsaro, saboda suna da uwa a gindin murhu. Shugaban kasa ya daurewa cin-hanci da rashawa gindi a gwamnatinsa, idan kai gawurtaccen barawo ne ka iya bayar da cin hanci, sai ka zama abokin tafiyarsu, yana yaudarar 'yan Najeriya, gwamnatinsa cike take da tarin masu zunubi marasa tsoron Allah da kishin kasa.

Ya kasa samarwa da al'ummar Najeriya musamman ta Arewa da cikakken tsaro na lafiya da dukiyoyinsu. Amma kuma abin mamaki duk irin wannan barazana ta tsaro da muke fuskanta ta 'yan ta'adda babu irinta a yankin kudu. Shugaban kasa mugun makaryacine wanda ya daurewa karya da yaudara gindi. Yau tattare 'yan abi yarima a gindinsa suna bashi gurguwar shawara, ya kasa samarwa da al'ummar kasararnan abubuwan da ya alkawarta a lokacin yakin neman zabe, duk inda ka shga Iska ta gurbace!

Wannan mutumin, Shugaban kasa ya kai kasarnan ya baro. Yana ta yawan zuwa kasashen Turawa da Amerika yana yi musu karyar cewa gwamnatinsa tana yin iyakacin kokarinta wajen ganin al'amura sun kyautata, alhali kuma a zahiri kowa yasan babu wasu al'amura da suka dauko hanyar kyautatuwa. A zamaninsa ne mutum zai sace dukiya wajen Biliyan 30 amma a yi masa tarar kudin da bai kai Naira Miliyan ba, wannan shine tsabar zalunci da kaiwa makura wajen iya nuna tsageranci da rashin tsoron Allah.

Shugaban kasa bai dauki mutanan Arewa da wata kima ba. Yana kallonsu da wani irin mugun ido ta cikin wani karkataccen Tabarau. Yana ji yana gani ana ta kashe mutane a jihar Pilato babu ji babu gani. Sannan kuma, ga 'yan ta'adda suna yin yadda suka ga dama an barsu suna cin karan da babbaka. Haka kuma, ambar jami'an tsaro da sunan aikin samar da tsaro da zaman lafiya suna cin mutuncin duk wanda suka ga dama, su shiga gidanka su yi maka wulakanci babu inda zaka iya zuwa ka kai kukanka a share maka wahaye.

Wannan wacce irin shedaniyar gwamnati ce da bata da kishin al'ummarta kokadan. Mutum ya sace dukiyar al'umma amma wannan mutumin yace an gafarta masa wai saboda ya gyra halinsa. Wannan shu'umanci ne da kekashewar zuciya.

Wadannan da wasu tarin dalilai sune suka sanya muke nuna matukar kiyayya ga wannan shugaban kasa. Amma ba wai dan kasancewarsa Kirista ba, Yau idan ya gyara halinsa ya nutsu ya zama mutumin kirki ya tsaida Adalci da daidaito zamu yaba masa tare da bashi cikakken goyon baya. Dan haka munyi shirin fatattakarsa ko da tsiya ko da arziki. Shekara ta 2015 kare jini biri jini zamu ga dan iskan da zai kawo mana tallar wannan mutumin mu zabeshi!

Tuesday, April 9, 2013

MU KEWAYA DUNIYA

MU KEWAYA DUNIYA

Assalamu Alaikum, Ina fatan 'yan uwana Gizagawa suna nan cikin koshin lafiya, haka kuma ina fatan za a yi min afuear kutsen da shirin yayi ba akan lokacin da ya kama ta zo ba, wannan kuwa ya faru ne sakamakon wasu dalilai, da fatan za'a gafarceni.

Yau insha Allah zamau yi bayani ne akan wata kasa da Nasan da yawan mutane basu san da ita ba, wasu ma ina zatan basu taba jin sunanta ba. Amma ko kun san da cewa akwai Kasar Turai da babu Jami'a (University) ko daya a cikinta? To ku karkade kunnanku ku sha labari. Domin yau zamu danna can cikin tsakiyar kasashen Turai ne, kuma zamu isa zuwa wata 'yar karamar kasa amma kuma babbar kasa ta fuskoki da yawa.

Wannan kasa sunanta LIECHTENSTEIN ko kuma Likstantain da Hausa. Ita dai wannan kasa tana a tsakiyar kasashen turai ne, sannan tayi iyaka ne da kasashe guda biyu kacal, wato tayi iyaka da kasar Switzerland daga yankin kudu da yamma, sannan kuma tayi iyaka da kasar Austria daga yankin Arewa da kuma Gabas. ita dai wannan kasa 'yar kara mace kwarai da gaske ta fuskar yawan jama'a, domin gabaki dayan mutanan kasar su 36,000 ne kwata-kwata, wato idan zan kwatanta ta da mazabar Gwale dake karamar hukumar Gwale sai nace mazabar Gwale ta ninka wannan kasa yawa sau biyu. Tabdi jan!

Haka kuma, kasar tana a fadin kafa 160 murabba'i. Babban birnin kasar sunansa VANDUZ, sannan kasar tana da larduna ne guda shida. Sannan, ta fannin tsarin shugabanci kasar tana da Sarki ne irin na gargajiya wanda ake gada, amma kuma suna da majalisar dokoki waan a sune suke tsarawa kasar dokoki kuma zabarsu ake yi duk bayan shekaru hudu.

Wannan kasa itace kasar da tafi kowacce kasa karancin Bashi a duniya. Haka kuma tana daga cikin kasashen da tattalin arzikinsu yake da karfi sosai, domin ta fuskar masana'antu yawan kamfanonin dake kasar sun haura yawan al'ummar kasar, gwarigwari zamu iya fahimtar cewa duk dan kasar ba zai rasa aikin yi ba kenan.

Ta fuskar addini kuma Musulmi suna da kashi 4.8 na adadin al'ummar kasar, kiristoci mabiya darikar Katolika sune suke da kashi 78.4, sannan kiristocin Reformed Church suke da kashi 7.9. Musulmi sune suke da matsayi na uku.

Idan kuma muka koma ta fuskar al'adun mutanan kasar. Kasancewarsu basu da yawa, wannan ya sanya al'adun kasashen da ke kewaye da su ya mamaye kasar. Da kuma al'adun kasar Jamus, domin yaren kasar shine Jamusanci. Dan haka mutanan kasar suna da sha'awar kide-kide irin na gargajiyar turawa da kuma wasan kwaikwayo. Haka kuma kasar tana da gidan tarihi kasaitacce da ake kira Kunstmuseum Liechtenstein, dan yana daga cikin abinda yake samarwa da kasar kudin shiga. Mutanan kasar dai sun dogara ne da irin yanayinsu mai dadi na lambuna da shuke-shuke da duwatsu masu tuntsuro da ruwa daga sama wajen samun kudin shiga, manazarta sunce wannan kasa tana daga cikin kasashen da sukafi yanayi mai dadi a duniya, wannan ce ta sanya mutane da yawa musamman Turawa suke zuwa kasar yawan bude Ido da kuma shakatawa.

Ta fannin tsaro kuma, wannan kasar itace kasa mafi karancin aikata laifuffuka domin akwai gidajan yari da ko tsuntsu babu a daure da sunan ya aikata laifi. Sannan a cikin shekara guda ne kacal ake samun mutum guda ya aikata laifin da za'a iya daureshi. Abinda ya sawwaka kenan a shirinmu na wannan makon sai kuma mako mai zuwa inda zamu sake Nausawa zuwa wata kasar.

Amadadin wanda ya sadani da ku Abubakar Idris FCT, Ni Yasir Ramadan Gwale da na shirya na gabatar nake cewa Wassalamu Alaikum.

Sunday, April 7, 2013


LABARIN WANI YARO DA YA KWAIKWAYI MALAMINSU

Wasu yara ne su uku suke zuwa makarantar Firamare, daga cikin yaran nan uku akwai wani mai suna Halifa ya lura sosai da yadda malamin PEnsu malam Salisu yake sanya hula. Dan haka ya hadda ce, duk ranar Juma'a Halifa da sauran 'yan uwansa sukan tafi masallaci tare da mahaifinsu, duk lokacin da aka yi musu wanka aka saka musu kaya aka saka musu hula sai Halifa ya karkata hularsa yadda yaga Malam Salisu yana sakawa. Duk sati haka yake yi, Mahaifiyar Halifa ta lura da yadda yake saka hula yana karkata ta, rannan sai tace masa kada ka sake karkata hula irin ta 'yan iska, budar bakin Halifa sai yace "Ai Malam Salisu ma haka yake sa Hula" akayi juyin duniya Halifa ya gyara hularsa yaki, sai yace ai malam salisu ma haka yake sakawa. Da labari yaje kunnen Mahaifinsu Halifa, sai yace masa kada ya kara karkata Hula, yaro ya dage cewa Ai haka malam Salisu yake saka hula. Rannan dai Mahaifinsu Halifa yace shi kuwa sai yaje yaga Malam Salisu, yana zuwa Ofishin Head Master, ya tambaya cewa yazo ne yaga malam Salisu Malamin Ajinsu Halifa, aka ce ya jira za'a nemo Malam Salisu, cikin Kankanin Lokaci sai ga Malam Salisu yana tahowa daga Nesa, Mahaifin Halifa yace Lallai wannan mai tahowar shine Malam Salisu, domin irin yadda ya karkata Hularsa babu bambanci da yadda Halifa yake karkatawa. Da Malam Salisu ya shigo suka gaisa da mahaifinsu Halifa, sai yake gaya masa ai Halifa ne duk lokacin da aka saka masa Hula sai ya karkataa yace Ai haka Malam Salisu yake saka, Munyi munyi ya daina amma sai yace Haka kake sakawa, Shine na ce ni kuwa sai na zo naga Malam Salisu, kuma abin mamaki shine yadda ka karkata haka Halifa yake karkatawa kamar kaine kake saka masa. Jin haka sai malam salisu ya gyara hularsa ta koma dai-dai, yace Insha Allah daga Yau na daina Karkata Hula. Wannan labari a gaske haka ya faru. Wannan kuma yake kara tabbatar mana da cewar Iyaye ba su kadai ne zasu baiwa 'ya 'yansu tarbiyya ba, Malamai ma suna da gudunmawa me yawan gaske da zasu iya bayarwa wajen kyautata tarbiyyar yaran da aka basu Amana. Domin anan zamu ga yadda Halifa yaki yarda da maganar mahaifinsa amma ya gwammace ya kwaikwayi Malaminsa wannan ya nuna tasirin Malamin sosai, ko shakka babu irinsu Halifa suna da yawa.

Hakika a yadda al'amarin ya nuna cewa Yara da yawa musamman 'yan Firamare suna koyar dabi'um Malamansu, na kirki ko akasin haka. Wannan kuma kalubale ne ga Malamai Lallai suyi shiga mai kyau, kuma su nuna kyawawan halaye a yayin da suke koyar da dalibansu, domin da yawan yara suna koyar malamansu ta dabi'a ko magana ko yanayin sanya sutura. Abubuwa marasa kyau ko da malamai suna yi to lallai su kaurace musu a duk lokacin da suke cikin makaranta wajen Dalibansu, musamman SHAN TABA, ko dura ASHAR ko GWALNAGWASO ko RANGWADA dama dukkan wasu abubuwa da basu kamata ba. Lallai YARA MANYAN GOBE, Allah ya taimaki Yara.