Saturday, September 28, 2013

KANO TA DABO TUMBIN GIWA: Ko Da Me Ka Zo Ka Fimu!!!

KANO TA DABO TUMBIN GIWA: Ko Da Me Ka Zo Ka Fimu!!!

Kirarin da ake yiwa jihar Kano a baya shi ne "KANO TA DABO TUMBIN GIWA, KO DA ME KA ZO AMFIKA" wannan shi ne kirarin da duk mutumin kano yake alfahari da shi a baya, wanda kwanci tashi wannan kirari yana neman zama ba gaskiya ba. Domin idan ka kalli jihar Kano da Kanawa sai kaga da dama anzo Kano amfi Kanawa komai, abin da yake nuna wannan kirari ba gaskiya bane. Akwai misalai da yawa akan haka.

Abu na farko, ka dauki batun OTAL, kafatanin  Jihar Kano Otal guda daya ne wanda zaka iya kiransa Otal na fitar kunya. Wannan otal shi ne TAHIR GUEST PALACE, kusan idan ka dauke otal din Tahir duk sauran otal da suke Kano kodai sun dade a sume, ko sun mutu, ko kuma su ba masu raiba kuma su ba matattatu ba. Mu dawo batun Tahir, wannan Otal na Tahir, bako ne dan kasar Labanan yake mallakarsa, ko shakka babu abin farinciki ne da alfahari ace wani ya zo garinmu ya bude harkoki na kasuwanci dan tattalin arzikinmu ya bunkasa. Haka kuma, bayanai sun nuna cewa a kullum Tahir na samun kudi a kalla Naira Miliyan guda daga hannun jami'an gwamnati ciki da wajen Kano da suke yada zango a otal din, kaga a wata yana samun Miliyan Talatin kenan, wannan lissafin yana fin haka ninkim ba ninkim a wasu lokutan wani zubin kuma akan samu ragi.

Ka shiga Tahir ka gani abin da ke faruwa a cikinsa. Su waye ma'aikatan Otal din tun daga Junior Staff har zuwa Senior Staff. Wallahi galibin ma'aikatansu daga Arnan Jos sai Katafawa da sauran 'yan Kudancin Kaduna, idan kaga Bahaushe mutumin cikin birnin Kano bai wuce Direba (Mai tuka Mota) ko kuma mai wankin takalmi ko mai gadi da wankin mota ba, wadannan su ne galibin aikin da 'yan Kano suke yi a cikin Otal din! Shin babu 'yan Kano din da zasu iya sauran ayyukan ne? Ina wadan da hakkinsu ne su kula da harkar daukar ma'aikata a kamfanoni? Mun sani dokar kasa ta ce duk wani kamfani da zai bude a wata jiha to ya zama wajibi ya dauki "Personnel Manager" dan asalin jihar, amma ka je ka bincika ba wai Tahir kadai duk wani Kamfani da yake a Kano indai na baki ne to tabbas Personnel Manager ba dan Kano bane. Shin bamu da wannan masaniyar dokar ne?

Wani abin ban sha'awa kuma da takaici, shi ne gwamnatin da ta gabata ta Malam Ibrahim Shekarau ta yi yunkurin samar da katafaren Otal "Five Star" a Lamba wan (No 1) Ibrahim Taiwo Road inda yanzu ake kira Governors College. Abin takaicin shi ne wasu 'yan gaza gani suka je suka samu Mai martaba sarkin Kano suka fada masa cewar a dakatar da Gwamnati daga gina wannan Otal mai hawa 12 ko 15, wai a cewarsu baki wadan da ba 'yan Kano ba, zasu dinga zuwa suna kalle asirin cikin Birnin! Wallahi wannan shi ne abinda aka je aka gayawa mai martaba sarki, aka fada masa karya da gaskiya akan lallai a dakatar da gwamnati daga samar da wannan otal din. Yanzu zance ya zama sai labari.

Duk lokacin da za'a yi wani gagarumin bikin da baki za su zo Kano to a wannan ranar dakunan Otal na alfarma karanci suke yi. Domin idan ka zare Tahir da Royal Tropicana wanda shima yana daga cikin Otal din da ya suma. Sai wanne kuma? Duk sauran 'yan rakiya ne. Ita kanta gwamnatin Malam Shekarau da ta gabata anyi ta matsa mata lamba akan ta gyara Otal din Magwan yadda zai yi daidai da zamani ya samarwa da gwamnati da kudin shiga, gwamnatin ta yi jan kafa sosai akan batun, sai daga bisani aka so yin aikin kuma lokaci ya yi halinsa, wannan gwamnatin kuma yanzu haka ta mayar da Otal din makaranta kamar yadda ta mayar da Lambawan Ibrahim taiwo Road. Haka shima, Otal din Daula dake kan titin Murtala Muhammad shima ance ya zama Makaranta. Allah ya sakawa maigirma Gwamna da alheri lallai muna da bukatar karin makarantu bila adadun a cikin birni da kauyukan Kano. Amma lallai Kano na da bukatar dakunan kwanan baki da ake kira Otal, sannan kuma na bukatar kudin shiga. Wannan fa Otal kenan kadai.

Abu na biyu, shine kamfanonin Kwarori da sinawa 'yan chana da Indiyawa, ka je kabi kididdigar wadan da suke aiki ka tuntubi ma'aikatan kaji me ke faruwa a cikinsu. Dan chana arne a garin Kano zai hana Bahaushe Musulmi dan Kano zuwa Masallacin juma'a saboda keta da karya doka dan yasan babu abinda za ai masa. Da yawan wasu ma'aikatan kamfanuka sallah AZAHAR suke yi ranar juma'a saboda ba'a basu damar zuwa masallaci. Ina 'yan Kano da masu kishin Kano? Ina kungiyoyin kare hakkin Bil-Adama? Shin wannan ba cin mutuncinmu bane a addinance da 'yan kasance? Amma saboda su ma'aikata ana yi musu barazana da cewa ga mutane can a bakin get suna neman a daukesu aiki, duk wanda yaga ba zai iyaba ya kama gabansa, dole suke hakura saboda tsoron talauci da subucewar dama. Bayaga wannan ka tambayi yadda ake cin zarafin ma'aikata, dan chana ko Indiya ko kwara zai takarkare ya gallawa ma'aikaci mari akan abinda bai kai ya kawo ba, sai dai yayi Allah ya isa a zuci, ko abokan aikinsa ba zai iya sanarwa ba, saboda tsoron zai iya rasa aikinsa da yake ciyar da iyalansa da shi.

Akwai wani kamfani da na sani yanzu haka yana cin karensa babu babbaka a Kano. Asalinsa a jihar Edo ko Imo ya fara yada Zango, amma saboda jihohin sun san me suke suka ce lallai su zasu bashi Personnel Manger kamfanin yaki yarda. Akan haka ya yarda yayi asarar kudin da ya kashe wajen yin gine-ginen matsuguni, ya wanke kafa ya zo Kano, yanzu haka yana cin akuya ce ko karensa babu babbaka, saboda ya samu jahilai gidadawa wadan da basu san inda yake musu ciwo ba. Su dai bukatarsu cikinsu da farjinsu. Wadannan fa, baki ne 'yan kasashen waje suke gallaza mana da cuta mana a cikin garuruwanmu, da muke ihu da kirari mun fi kowa. Sannan kuma akwai  'yan kasa kudawa abokan zamanmu, Inyamurai da sauran kabilu wadan da suka mayar da kafatanin kasuwanninmu nasu, idan kaga Bahaushe to ko dai dillali ko dan kamasho ko dan kayi nayi. Allah ya sawwake! Zan cigaba In Sha Allah.

Yasir Ramadan Gwale
28-09-2013

Friday, September 20, 2013

Anya Gwamnonin Arewa Suna Da Gaskiya Kuwa?


ANYA GWAMNONIN AREWA SUNA DA GASKIYA KUWA?

Halin da Arewa ta samu kanta a ciki a wannan mawuyacin lokaci, hali ne da babu wanda yake bukatar a yi masa bayanisa. Irin wannan mummunan yanayi da Arewa ta samu kanta a ciki bamu ta'ba shiga wani irin yanayi mai kama da haka ba a baya. Zaman lafiya ya kauracewa jihohi da dama, harbe-harben bindigogi da karar tashin bomabomai sun zama abu na yau da kullum, kusan yanzu zamu iya cewar da dama a Arewa an saba da jin karar harbin bindiga da karar fashewar Bom. Abubuwa na ta'addanci sun gama kankama a kusan kafatanin jihohin Arewa, ko ina batu ake na sukurkucewar al'amuran tsaro. Wannan rashin tsaro gwamnonin Arewa suka saya da kudinsu, aka kuma sayarmusu. Domin tun da aka samu gwamnonin da suka dinga Amfani da 'yan Banga suka saya musu Makamai dan farwa duk wanda suke jin zai iya shiga gabansu, al'amuran tsaro suka lalace. Misali na gwari-gwari shi ne yadda tsohon Gwamnan Borno Ali Shariff yayi amfani da ECOMOG ya saya musu makamai su ba jami'an tsaro ba, wanda wannan tsohon gwamna yana da hannu dumu-dumu akan halin da jihar Borno ta samu kanta a ciki na lalacewar al'amuran tsaro.

Haka zalika, idan muka kalli gwamnonin nan bakwai masu tayar da kayar baya a jam'iyyar PDP ya isa ya nuna mana rashin gaskiyar Gwamnonin Arewa. Su wadannan gwamnoni sun hada kai tun suna su hudu har suka zama Biyar daga baya suka zama bakwai dan abinda suka kira kwatowa kansu 'yancin da suke ganin Jam'iyyarsu tana neman danne musu. Labarin sabatta juyattan da ake yi tsakanin wadannan gwamnoni da suka bijirewa jam'iyyarsu da kuma shugabancin jam'iyyar karkashin Bamanga Tukur kusan ya zama ruwan dare gama duniya, duk wanda yake bibiyar al'amuran da suke faruwa yana da masaniyar abubuwan da suke faruwa da wadannan gwamnoni. Wadannan bijirarrun gwamnoni sun hada kai suka nemi tsayar da kasarnan cik domin nemawa kansu mafita. Kusan kullum Mitin ake a Abuja fadar gwamnati domin tattauna yadda za'a shawo kan wadannan bijirarrun gwamnoni. Wannan abu ne da yake a fili cewa suna yi ne dan biyan bukatar kashin kansu, kuma dole aka tsaya ake sauraren yadda za'a biya musu bukatunsu.

Daga cikin bukatun da wadannan gwamnoni suke son a biya musu bayan sallamar shugaban jam'iyyarsu Bamanga Tukur, har da kiran da suka yiwa shugaban kasa na kada ya kuskura ya tsaya takarar sake neman shugabancin kasarnan a zaben 2015 mai zuwa. Anan ne zaka fahimci rashin gaskiyar wadannan gwamnoni, domin idan muka koma baya sun fito suna ihun cewa Jam'iyyar tana da tsarin karba-karba, wanda suka ce dole a mutunta shi domin yarjejeniya ce da aka yi a Jos a shekarar 2005, kuma shi wannan shugaban Goodluck Jonathan ya halarci wannan yarjejeniya, amma ya kekasa kasa yace shi sam bai san zancen ba, a zaben 2011 da ya gabata, kuma gwamnonin suka mara masa baya. A takaice suka yi yarjejeniya shugaban ya karya musu yarjejeniya. Ban sani ba ko batan basira ne ya sa suka ce wai bayan da shugaban ya karya waccan yarjejeniya, suka sake kulla wata yarjejeniyar da shi akan cewa karo daya kawai zai yi, inda shima da bakin shugaban ya amsa cewa Karo daya zai yi! Wanda daga bisani Kakakinsa yace Shugabanfa da wasa yake yi. Tayaya mutumin da kuka yi yarjejeniya ya karya zaku sake kulla wata yarjejeniyar tare da shi? Watakila ko nine ban fahimci al'amarin ba.

A zaben fitar da gwanin da aka yi na PDP tsakanin Atiku dan Arewa da Goodluck Jonathan, wadannan gwamnoni suka tsaya kai da fata cewa sai keyar Atiku ta taba kasa a zaben fitar da gwanin. Domin kuwa Gwamnan jihar Adamawa Murtala Nyako da kansa ya tsaya a bakin akwatin jiharsa akan dole daliget na jihar su zabi Jonathan su bar dansu Atiku. Haka zalika sauran gwamnonin babu wanda bai yiwa Jonathan Kamfe a sarari ko a boye ba, akan ganin shugaban ya kai labari. Haka suka dage sai da shugaban ya samu kaso 25 da hukumar zabe ta yi tanadi a kowacce jiha. Babu gwamnan da bai yi kokarin Jonathan ya kawo wadannan kuri'u ba. Yanzu kuma abin mamaki wai sune suka fito suke kalubalantar abinda suka ce sunji sun gani gara tsintacciyar mage akan magen gida.

Sannan kuma wannan tayar da kayar baya da gwamnonin suke yi da ta kusa tsayar da kasarnan cik saboda sun hade kansu, zai tabbatar maka da cewa da sun hada kai su sha tara ko sha bakwai akan cewa tilar al'amuran tsaro su kyautata a Arewa gabaki daya, kana jin zamu kawo yar yanzu ana fama da tashe-tashen hankula? Kanajin da sun hada kai suka ce Tilar a tayar da kafadun masana'antun da suka durkushe hakan ba zai yuwu ba? Kanajin da sun hada kai suka ce tilar a aiwatar da aikin yashe kogin kwara da marigayi YarAdua ya faro za'a tsaya? Wannan ya kara tabbatar mana da gangan duk abinda suke faruwa na sukurkucewar tsaro, da karyewar tattalin arziki suke faruwa, wallahi idan wadannan gwamnoni sun so sai al'amura sun daidaita, amma da yake su gaba ta kaisu suna samun fa'ida da tashin hankali babu abinda ya shafesu. A kalla ace gwamnoni Goma suka hade kai suka ce sai shugaban kasa ya gyara al'amuran tsaro da suka sukurkuce lashakka sai lamura sun kyautata, amma saboda ba bukata bace ta kashin kansu shi yasa muke cigaba da kasancewa cikin zullumi a kullum ranar Allah.

Jami'o'i suna cigaba da kasancewa a garkame 'ya 'yan talakawa na gararamba da watangaririya babu karatu babu aikin yi a cikin unguwanni. Kasuwancin yana kara komawa baya a kullum, Fashi da makami kullum yana karuwa, fashi na rainin hankali domin sai a shafe awanni sama da biyu ana fashi, kuma a gudu bayan ankwashi makudan kudi ba tare da anga ko kurrar 'yan fashin ba. Lallai da ace da gaske wadannan gwamnoni suna kishin Arewa da suke tinkaho dole a tsaya a sauraresu a kuma biya musu bukatunsu, dan fitar da Arewa daga cikin halin da ta ke na bacin tafarki.

Lallai Muna kira ga gwamnoninmu da suji tsoron Allah su hade kansu wajen dawo mana da martabarmu da kimarmu da ta zube warwas a idan duniya. An rainamu saboda bama iya warware matsalolinmu da kanmu, mun kasa fahimtar ina muka dosa, an jahiltar da mu, an shiga gabanmu ta ko ina. Lallai suji tsoron Allah su hada kai wajen kawo karshen wannan tashe tashen hankula da suke faruwa.

Yasir Ramadan Gwale
20-09-2013

Thursday, September 19, 2013

MALAM SALUHU SAGIR TAKAI: Mai Kamar Zuwa Kan Aika!!!

MALAM SALUHU SAGIR TAKAI: Mai Kamar Zuwa Kan Aika!!!

Malam Saluhu Sagir Takai mutum ne da ba shi da bukatar wani dogon ta'arifi wajen al'ummar jihar kano. Malam Saluhu tun yana shugaban karamar hukumar Takai al'umma suka shaida nagartarsa da kwazonsa da kuma jajircewarsa wajen ganin anyi gaskiya da sanya abubuwa a muhallansu, wannan ce ta sanya ko a shekarar 2001 lokacin da tsohon shugaban kasa cif Olishegun Obasanjo ya kawo ziyarar aiki a Kano lokacin Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso karamar Hukumar Takai aka kai Obasanjo domin ya ga ayyukan raya kasa da shugaban karamar hukumar yayi duk kuwa da kasancewarsa dan jam'iyyar Hamayya. Wannan kadai ya isa ya nuna maka nagartar wannan dan tahaliki, haka kuma abokan aikinsa sun shaida tare da yabawa da irin gaskiyarsa da rikon amanarsa.

Jama'a da dama sun shaida lokacin da ya rike kwamishinan Kananan Hukumomi da kwamashinan Ruwa, karkashinsa aka samar da madatsar ruwa mafi girma a fadin Najeriya, har ya gama ba'a zargeshi da wata al'mundahana ko batar da sawun gaskiya ba. Malam Saluhu Sagir Allah ya sa mutum ne mai tsantseni da takawa ga kuma tsoron Allah, wannan shakka babu zato ne na zahiri wadan da dukkan jama'ar da suka yi Mu'amala da shi sun kyautata masa wannan zatan, ya alkinta amanar dukiyar da aka bashi, har yanzu ba'a sameshi da almubazzaranci ko barnata dukiyar al'umma ba.

Haka zalika ko a lokacin da ya yi takarar Gwamna a shekara ta 2011, anga irin shaidar da al'umma suka yi masa domin, ya gudanar da yakin neman zabe mafi tsafta a tarirhin siyasar Kano. Babu kalamai na tashin hankali, babu zage-zage ballantana zubar da jinin wadan da basu ji basu gani ba da sunan Bangar Siyasa. Allah shi ne mai bayar da Mulki a Lokacin da ya so kuma ga wanda ya so, Allah cikin hukuntawarsa bai kaddara Malama Saluhu ya samu Nasarar zama gwamna ba a zaben da ya gabata. Bisa irin waccan Nagarta tasa da kuma tsantseni da kokarin kamanta gaskiya tasa ta sanya muke ganin ya kamata jama'ar kano su bashi dama domin tabbatar da zaton alkhairi da aka yi masa.

Alhamdulillah, Batun ayyukan raya kasa wannan ba bakon abu bane a wajen Malam Saluhu Sagir Takai, domin da irin shawarwarinsu ne Gwamnatin Malam Ibrahim Shekarau ta aiwatar da kyawawan ayyukan raya kasa a fadin jihar kano. Tun daga asibitoci da tituna, da makarantu da ayyukan yi. Ta bangaren Inganta harkokin Addinin Musulunci a Gwamnatance wannan abu ne da tun farko aka yi masa shaida akai, akan haka ne ma wasu ke zarginsa da cewa ya cika riko da addini, wanda wannan kyakykyawan zato ne ba zargi ba a wajen duk wani mai hankali da sanin ya kamata.

Lallai Jihar Kano tana bukatar Jan Namiji gwarzo jarumi mai kokari da tsantseni da takawa da sanin ya kamata. Malam Saluhu Sagir Takai Allah ya amince ya zama Gwamnan Kano a 2015.

Yasir Ramadan Gwale
Shugaban Kungiyar, Takai Youth Mobilisation.
yasirramadangwale@gmail.com
19-09-2013

RIKICIN BOKO HARAM: Ana Rufe Kura Da Fatar Akuya!!!

RIKICIN BOKO HARAM: Ana Rufe Kura Da Fatar Akuya!!!

Tun lokacin da aka bayar da sanarwar ayyana dokar ta baci a jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa adadin rayukan da suke salwanata yake karuwa musamman a jihar Borno. A zatanmu ayyana dokar ta bacin nan da shugaban kasa ya yi zai kawo saukin lamura, adadin rayukan da suke salwanta zasu ragu, amma sai akasin haka ne yake faruwa. Tun da sojoji suka yiwa Jihar Borno tsinke kusan kullum labarin asarar rayukan da ake bayarwa sun shallake hankali da tunani, wani abin mamaki da daure kai shi ne yadda ake bayar da rahotannin cewar su 'yan Boko Haram suna yin bazata ta hanyar amfani da kayan sojoji su je su farwa farar hulu su salakasu. Ko shakka babu wannan babban abin tashin hankali ne da kuma daure kai. Ta yaya rundunar tsaron jihar Borno zasu iya gamsar da mu cewar wadan da ake bada rahotannin sun sanya kayan sojoji sun kaiwa fararan hula farmaki 'yan ta'adda ne ba sojojin gaskiya bane?

A baya duniya ta shaida yadda sojoji suka shiga garin BAGA inda suka kashe darururwan mutane sannan suka sanyawa dubban gidajen jama'a wuta babu gaira babu dalili, sannan daga bisani bayan karairayin kare hakkin bil adama da kungiyoyi da daidaikun mutane suka dinga yi gwamnati ta bayar da sanarwa kafa kwamatin da zai binciko gaskiyar abin da ya auku. Inda babu jimawa rundunar tsaron suka ce 'yan Boko Haram ne suka batar da kama wajen sanya kayan sojoji suka aikata wannan mummunan aikin ta'addancin! Kuma shi kenan har yanzu zancen ya sha ruwa babu wanda ya kuma daga shi, zancen rahoton kwamitin da shugaban kasa ya kafa yabi iska, har yau babu wanda aka kama ko aka tuhuma da wannan mummunan aikin ta'addanci, an kashe banza an gudu.

Sannan kuma, Tun bayan harin garin BAGA kusan duk sanda za'a bayar da rahotan kisan fararen hula, sai ace wasu masu sanye da kayan sojoji sun kashe mutane 10 ko 20, ko 30. Wanda yanzu abin ya fara neman shallake hakali da tunani inda a cikin wannan makon aka ce wai wasu  'yan Boko Haram sanye da kayan sojoji sun tare hanyoyi suna yayyanka mutane tare harbesu har lahira, a yayin da a gefe guda kuma aka bayar da rahotannin an kashe 'yan Boko Haram kusan 150 wanda wannan adadi ne mai girman gaske. Al'amarin akwai daure kai da rikitarwa! Shin da gaske ne wadan da sojojin suke kashewa 'yan Boko Haram ne? Shin da gaske ne su 'yan Boko Haram ne suke yin bazata da kayan sojoji suke kashe jama'ar da basu san hawa ba basu san sauka ba? Wadannan sune tambayoyin da ya kamata mu yi.

Bisa ga dukkan alamu, duk irin wannan batarnaka da ke faruwa a jihar Borno ana rufe kura da fatar akuya ana sauya akalar gaskiya. Amma hakika munyi Imani da dukkan Kaddara mai kyau da marar kyau, duk abubuwan da suka wakana masu kiyayewa sun kiyaye a cikin takardun da ruwa baya shafe zanens. Lokaci zai zo komai tsowon zamani da gaskiyar abubuwan da suka faru zata bayyana. Fatanmu Allah ya cigaba da karemu da kariyarsa, ya yi mana garkuwa da garkuwarsa. Su kuma wadannan 'yan ta'adda Allah ya tona musu Asiri ya wargaza shirinsu da makircinsu. Allah ka bamu lafiya da zama lafiya.

Yasir Ramadan Gwale
19-09-2013

Thursday, September 5, 2013

RIKICIN PDP: Bamu Ci Nanin Ba, Nanin Ba Zata Ci Mu Ba!!!


RIKICIN PDP: Bamu Ci Nanin Ba, Nanin Ba Zata Ci Mu Ba!!!

Tun bayan da rikicin cikin gida ya balle a cikin jam'iyyar PDP da yawan 'yan Najeriya da kafafan yada labarai suka mayar da hankali kacokan akan al'amarin. Wannan rikici na PDP kamar yadda su 'yan jam'iyyar suka sha nanatawa cewa ba sabon abu bane a wajensu, daman sun saba da irin wannan yakin cacar bakin lokaci bayan lokaci, amma sanin kowa ne wannan rikicin ya sha bamban da duk wanda jam'iyyar ta taba fuskanta a baya, kasancewar ya hada manya-manyan duwatsun cikin jam'iyyar. Kuma a bayyane take cewar wannan rikita-rikita da dambarwa da ta dauki hankalin kusan dukkan 'yan siyasa dama wadan da ba 'yan siyasa ba, su masu kafsawa suna yi ne gaba dayansu domin neman mafitar kashin kansu, ba wai mafitar halin da Najeriya take ciki ba. 'Yan PDP kwararru ne wajen juyar da hankulan da dama daga cikin 'yan Najeriya musamman talakawa, domin wannan rikici ba wai zuwa ya yi bagatatan ba, daman can ana sane da wannan kwantacciyar a kasa, ana sane da dukkan wani zaman doya da manja da akeyi, sai da suka bari al'amarin zaben 2015 yana kara tunkarowa sannan suka kwanto wannan ruwan domin samun farin jinin talakawan da basu san yadda abubuwa ke wakana ba.

Su wadannan masu cewa sune sabuwar PDP karkashin Jagorancin tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da wasu gwamnoni; da kuma su wadan da ake ganin su ne 'yan tsohuwar PDP, duk cikinsu babu wanda ya sanya halin da al'umma take ciki a gabansa, kamar yadda suka sha fada kowa na yunkurin rike madafun iko ne. Su masu kiran kansu 'yan sabuwar PDP suna yaudarar talakawa akan suna rigima da fadar shugaban kasa da kuma shugaban jam'iyyar Bamanga Tukur. Kusan idan ka cire Gwamnan Ribas Rotimi Amaechi (Wanda shima sun Arewantar da shi) kusan dukkansu 'yan Arewa ne, suna kallo aka dinga bankawa Arewa wuta; ana yayyanka mutane babu ji babu gani; ana tayar da bomabomai; ana karya tattalin arzikin Arewa, ana kashe manyan mutane amma babu wanda ya fito ya kalubalanci gwamnatin tarayyar da alhakinta ne ta karewa dukkan 'yan Najeriya rayukansu da dukiyoyinsu. Suna ji suna gani aka dinga bin unguwannin talakawa a Borno da Yobe da Kano da Bauchi ana daddasa musu Bamabamai mutane suna mutuwa babu kakkautawa, amma babu ko daya da ya nuna yatsa ga gwamnatin tarayya, balle ya yi fito na fito da ita.

Wannan ta nuna mana cewar wadannan mutane ko mun tausaya musu ko mun kusancesu, to kada ka ji da wai su ba Arewa ko al'ummar Arewa ce a gabansu ba. Tunaninsu shi ne ya za'a ayi kada shugabanci ya kubuce musu, kada damar da suke da ita ta tursasawa talakawa 'yan takara bata sunce daga hannunsu ba. Batun fitar da talaka daga cikin kangin talauci da rashin makarantu da rashin asibitoci duk ba shi ne a gabansu ba, ya isheka abin misali ga kungiyar malaman jami'o'i ta ASUU tana fama da yajin aiki akan abinda suka kira hakkinsu, galibi kuma dalibanmu na Arewa ke cutuwa da wannan yajin aiki amma babu wani daga cikinsu da ya nemi kawo karshen abun, ko ya je Abuja yana zagin gwamnatin tarayya akan yajin aikin. Su duk wani mawuyacin hali da talaka zai shiga wannan ba damuwarsu ba ce. Su kuma talakawa da dama sun ara sun yafa, wasu tuni garkuwar jikinsu ta fara yin rauni wajen tausayawa wadannan gungun mutane, wasu sun fara yabo da yin kirarari ga wadannan mutane, alhali su ba su ma san talaka yana yi ba, da ka yi da kada ka yi duk ba agabansu kake ba, kana da amfani ne kadai lokacin da bukatunsu suka taso irin wannan lokacin.

A ranar 11 ga watan 5 na wannan shekarar Sashen Hausa na BBC a cikin shirinsu na Gane Min Hanya, sunyi hira da Atiku Abubakar inda ya tabbatar da cewar dukkan kudaden da ake warewa wajen tafiyar da tsaro sacewa ake yi, ya fada balo-balo, kuma wannan batu na tsaro Arewar da Atiku ke ciki ita ce wannan al'amari ya shafa amma babu wani mataki da suka dauka na ganin an kare rayukan al'umma. Suna ji suna gani tattalin arzikinmu yana durkushewa, kasuwanninmu suna komawa bayawa, harkar noma na sukurkucewa, babu wani wanda ya damu da hakan tunda suna da kamfanoninsu a kudancin Najeriya da kasashen waje. Amma saboda rashin sanin inda kai ke ciwo talakawa har murna suke tare da yabawa wadannan mutane wanda ba su damu da duk yawan mutanan da za'a kashe a jihohinsu ba. Haka suma masu gwamnati ba al'umma bace a gabansu. Muna ji aka ce wasu magoya bayan PDP da suka je taronsu na musamman a Abuja daga Adamawa su 9 suka yi hatsari kuma duk suka mutu amma ko zancen baka ji an daga ba, domin su ba ta talakawa suke ba, amma kuma a haka talakawa ke bata lokaci akansu. Lallai dole mu tashi mu san inda yake mana ciwo!

Atiku Abubakar ya bar PDP babu irin sunayan da bai kirata ba ya kafa AC, amma daga baya ya yi mata kome, kuma mutanan da ya dinga zagi sudin dai ya sake tararwa da ya komo ba wasu ne sababbi ba. Duk wannan bai isa ya nuna mana cewar wadannan mutane ba damuwarsu bace duk irin mawuyacin halin da muke ciki na matsin rayuwa. Dan haka da Bangaren su Atiku da su Bamanga Tukur duk uwarsu daya ubansu daya, babu wani nagari a kashi, da busasshen kashi da danye duk kashi ne, ita daman kura tun tana jaririya sunanta ya baci, babu yadda za'a zo daga baya bayan ta girma tayi dukkan irin barnar da ta yi, ta samu wanda ya fi karfinta sannan a ce mana ai daman ita ta gari ce. Dan ahaka mu namu ido, sai dai muce musu Allah ya karawa Barno dawaki, Allah kuma ya kara dalili.

Yasir Ramadan Gwale
05-09-2913