Bara, Roko, Tumasanci, Al-majiranci da kuma karatun al-qur’ani a Arewa!!!
A kasar hausa idan akace almajiri ana nufin wani dalibi da yafito domin neman ilimin alqurani; wannan shi ne almajiri. Kuma galibi almajirai ana tura su gurin wani malamin alqurani ko kuma malamin da akafi sani da alaramma. Shi wannan alaramma shi ne wanda wadan nan iyaye da suka aiko dansu wajen sa domin ya nemi ilimin alqurani rayuwarsa ta ke a hannunsa. Alhaliknsa ne koyawa wannan almajiri karatun alqurani da kuma lura da yadda wannan almajiri yake gudanar da rayuwarsa tare da sauran abokan zamansa almajirai. Wanda wadan nan almajirai suna karatu a hannun malaminsu a wasu lokuta sanannu. Misali yawancin makaran tun Allo suna fara karatu daga bayan sallar Asuba zuwa lokacin da rana ta hudo daga nan za’a salami kowane yaro don ya fita domin neman abin da zaici har zuwa kimanin karfe takwas na safe daga nan za’a koma karatu baza a tashi daga karatu ba sai karfe goma na safe zuwa sha daya a wannan lokacin akansamu wasu almajiran da suke fita neman tuwan da aka ci jiya da daddare aka rage wanda akafi sani da dumame. Sannan wadan nan almajiran suna da lokacin shakatawa kusan tundaga wannan lokacin da suka tashi harzuwa lokacin sallar Azahar sannan wasu su koma makaranta suyi rubutu ko wankin Allo kodai wani dan aiki da zasuyi amakaranta wanda wannan lokacin shi zai daukesu zuwa la’asar daga nan ne fa karatu yake kankama harzuwa dab da magaruba daga nan za’a tashi zuwa sallar magriba baza a dawo karatu ba sai bayan sallar isha to daga nan ne za’ayi karatu harzuwa lokacin day a sawwaka. Wannan shi ne karatun makarantar Allo wanda ake turo yara daga garuruwa zuwa gurin alarammomi domin neman karatun Alqurani.
Sannan su wadan nan malamai da akafi sani da alarammomi ba dukansu ne malaman da za’a kira malaman Addini ba domin Addinin musulunci bai takaitu zuwa ga karatun alkurani ba kawai; akwai sauran karatu na litattafan hadisi da fiquhu wanda wadan nan malaman da suke wannan karatu su akafi sani da malaman zaure; to a musulunce wadan nan sune ake kira malaman Addini domin sunhada ilimin duka na Alqurani da na hadisai. Sannan su kuma alarammomi galibin su sunfi shahara da karatun alkurani wato ba tare da sanin fassararsa ba a wani lokacin ana kiransu dasunan Gardawa. To a gaskiya baduk wadan nan gardawa ko alarammomi bane malaman Addini. Ba ina muzanta karatun kur’ani bane ko alarammomi.
Sannan idan muka duba Bara ko roko wanda galibin wadan nan Almajirai suke yi da sunan karatun alqurani. Agaskiya bara bata da alaka da karatun alkurani yanzu misalin idan kadauki kano da Maiduguri zaka iske yara suna bara da sunan sunzo karatun Alkurani tundaga karfe bakwai nasafe harzuwa karfe takwas na dare. Sai kayi mamaki ina karatun da suke yi ko kuma ina malaman da aka damka amanar wadannan yara a hannunsu suke. Zaka gansu babu tsafta babu takalma akafafunsu gashi kuma kayan su duk sun yage kai kace tonosu akayi daga bola kuma da sunan su makaranta alkurani ne shin anan me suke nunawa? Ga wanda baisan karatun alkurani ba idan ya gansu mai zaidauka? Wanda kuma a zahirin gaskiya wannan hali da suke ciki na kazanta Alqurani yayi turda ita. Kuma zaka samu su wadan nan yara da ake kira Almajirai wanda galibi shekarunsu daga biyarne zuwa shekara goma sha biyar suna bin kwararo lungu da kuma manyan tituna musamman na cikin birni kai zaka samu Almajiari sunazuwa har ma’aikatun gwamnati misali Audu bako sakateriya a kano zaka iske almajiarai maza da mata yara da manya da ‘yan jagaliya duk suna roko da tumasanci. Wanda a halinyanzu a kano alkalumma suna nuna cewa akwai almajirai sama da miliyan biyu duk da gwamnatin da ta gabata taya iyakar kokarinta wajen taga ta tallafawa abin wanda maimakon wannan ya zama ansamu raguwar abin a a kullum sai kara samun karuwar almajirai akeyi. Kaduba kasuwanni ko ina kaje kaga almajiri kuma waishi dalibin alqurani ne.
Baya ga wadan nan yara da suke bara da sunan neman abin da zasu ci akwai kuma wani kashin na mabarata wanda sukuma ba makaranta alqurani bane wasu tsofaffi ne mata da maza da yawan wadan nan tsoffi suna bin manyan tituna da unguwannin masu hannu da shuni da kofar gidajen attajirai dan sunan bara wani lokacin zaka gansu tare da kana nan yara kodai sunayi musu jagora ko kuma suna binsu rabe-rabe, sannan idan ka dubi wadan nan tsofaffin da kyau zaka ga ba ‘yancikin birni bane domin akan tituna suke kwana, misali kaje titin miyangu road dake kano da Abbas Road da Tukur Road da Audu Bako Way duk zaka rika ganinsu da tsummokaransu jibge mata da maza, watakila idan ka bibiya a kauye da suke zaune suna da mahalli da ‘yan kaji da agwagi da suke kiwo duk da munsan cewa akwai matsananciyar rayuwa acikin kauyuka amma zaka samu mutuwar zuciya ce ta fito da wadan nan tsaffi daga kauyukansu, a gefe guda kuma gwamnati babu wani yunkuri da take yi na taimaka musu, munsan da cewa akwai gidan tsofaffi kusan a kowace jiha a Arewacin Najeriya misali a kano akwai wanda Audu Bako ya gina a Mariri yana nan haryanzu inbanda kadangaru da gafiyoyi da kunami sune kawai ke budurinsu a wannan gida.
Sannan wani kason kuma na almajirai su ne kutare da makafi da guragu wadanda akafi sani da nakasassu ko masu bukata ta musamman, suma suna nan suna bin tituna da ma’aikatu da guraran zaman jama’a da masallatai da majami’u, kai yanzu abin harma yakai kawai da mutum yaji ciwo a hannu ko a kafa kawai saya nannade hannu ko kafa da bandeji da sunan shi almajiri ne ataimaka masa kai abin ma ya wuce nan zaka ga kato lafiyarsa kalau yan cewa wa jama’a sutai makamasa. Wanda anan jama’a da dama sun taimaka wajen karfafawa wadan nan masu mutuwar zuciya gwiwa domin da mutum yace a taimaka masa sai kaga jama’a kowa na yunkurin zura hannu a aljihu yana lalubo ragowar canji, bayan ga makwabtansa sune a hakku da ya taimakawa akan wani mutum da hanyace ta hadasu, da dama wasu suna sane da cewa makwabtansu suna cikin mawuyacin hali na bukata mai makon su taimaka sun gwammace su je bakin titi su cigaba da kashewa wadannan mutane zuciya.
Bayaga wadan nan akwai masu bara yar tafida gidanka wato mobile begging sukuma suna bin masallatai ne da an idar da sallah sai kaga kato lafiyayye ya tashi tsaye kodai yace jama’a ni matafiyi ne ina neman ataimakamin guzurina ya yanke ko kuma yace jama’a nabaro iyalina babu abin da zasuci a taimakamin. Wasu kuma zaka ga nasu salon daban ne domin su kuwa rataya gatari suke a kafada suna bin guraren zaman jama’a suna cewa wallahi munnemi aiki bamu samu ba ku taimaka mana dana abinci hakadai bara salo-salo idan kaga wani salon barar ma abin sai ya baka kunya da mamaki. Wata rana wani magidanci yana zaune a kofar gidansa sai ga irin wadan nan mutane da gatura biyu a kafadunsu suka rokeshi, da ya kallesu sai yace tunda baku sami aikiba ga aiki yace ku sare wannan bishiyar ku daddatsata nawa zan biyaku sukayi ciniki kafin ya shiga gida ya fito sun tsere, kaga wannan karara ya nuna karya sukeyi daman mabarata ne.
Shin wai mu muka fi kowa talauci ne akasar nan ko kuwa mu muka fi kowa mutuwar zuciya? Shin ina alakar bara da alkurani? Wai yanzu abin haryakai ga almajirai zasu hada kudi sutafi lagas ko Ibadan ko Abuja ko wasu garuruwan ba wadan nan ba dasunan bara.Ga misali za a kwaso almajirai daga legas azo kano a zubar dasu kuma kaji babu wani mataki da gwamnati ke dauka na magance aukuwar hakan anan gaba. Ga kuma manyan Almajirai wadan da suke barar kasa da kasa wato international bagging wato irin masu zuwa saudiyya da Sudan kusan nayi maka jam’i duk almajirin da ka gani a Sudan insha Allahu Bahaushe ne wai yana tara kudin tafiya maka ta barauniyar hanya wanda da yawa suna mutuwa a teku a cikin wannan tafiya mai hadari a cikin kwale-kwale.
Anan yaka mata gwamnati tatsaya tayiwa abin duban tsanaki bawai ataimakawa almajirai ba kawai a’a yaya za’a yi a rage kwararsu zuwa cikin birane, wannan shi ne babban abin da gwamnati yaka mata tayi domin idan katai makawa goma to insha Allahu zaka samu sabbabin almajirai wanda sun nunka wadan nan da aka taimakawa. Sannan sukansu malamai yaka mata sufadakar da mutane dan gane da cewa bara bata da alaka da karatun alkurani.
Abin Tambaya me ya sa kawai Hausawa ake gani suna bara da a Najeriya? Me gwamnatocinmu suke na yakar talauci da fatara? Me ya sanya ‘yan kudu basa yin bara kamar yadda akeyi a Arewa? Misali idan ka kalli kasafin kudi na bana na jihohin Arewa ya ninka na jihohin kudu amma kuma tsananin rayuwa yana Arewa jihar Ekiti tanada kasafin kudi na Naira Biliyan 88, Kuros Riba Naira Biliyan 144, Ananbara Naira Biliyan 82, Enugu Naira Biliyan 74. Amma idan ka kalli na jihohin Arewa sai kaga ya fi nasu nesa ba kusa ba misali a bana Jihar Kano tanada kasafin kudin da yakai Naira Biliyan 210, Borno Naira Biliyan 150, Gombe Naira Biliyan 92 duk da irin wadan nan makudan kudi da ake warewa amma baka ganin wani canji duk shekara, ga rubutun kasafin kudi akan takarda abin gwanin sha’awa amma kuma yana tsayawa iyakar takardar ne kawai domin babu wani abu da yake nuna cewa ana aiwatar da wannan kasafin kudi dake kan takarda tundaga gwamnatin tarayya har ta jihohi.
Lallai akwai babban aiki na kokarin yakar bara da almajiranci a jihohin Arewa. Misali idanda da gaske shugabannin Arewa suke me zai hana su kai koke zuwaga majalisar kasa da gwamnatin tarayya akan a kirkiro da sabuwar wata ministiri ta al-majirai kamar yadda aka kirkiraro ma’aikatar Neja dalta inda ake taimakawa da zauna gari banza tsageru da dimbin kudade kuma ana kaisu kasashe dabam-dabam suna zuwa suna karatu. Idan har tsagerun Neja Dalta zasu zama barazana a kudu don haka aka samar masu da Ministry to shakka babu muma a yankin Arewa al’majirai babbar barazana ne domin da irin wadan nan Al-majirai Mai Tatsine yaci karensa, haka kuma irinsu suke saurin shiga kungiyoyi irin na Boko Haram wanda tuni bayanai suka nuna tun asali sune ‘yan gani kashenin Muhammad Yusuf ire-irensu ya rika ribata da kalamansa, shakka babu muna bukatar a kirkiro da sabuwar ma’aikatar al-majirai ta gwamnatin tarayya domin idan har za’a sami al-majirai sama da miliyan 2 wanda sunkai ko sun ninka yawan mutanan jihar Bayelsa da delta da Ekiti da Ebonyi.
Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@hotmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com